PAGE 6
---------------------------------
GODIYA AGAREKU LODI LODI DOMIN KUKE DAURANI AKAN HANYA hassan atk.Real shaxee.princes dija inayinku irin totallyn nan
Amnah tuki take cikin sauri dan ita aganinta sunyi letti mah.
Amsard kuwa shima yana shiga mota yafara sauri domin yanaso ya isa kafin 10pm Tuki yake cikin sauri.
Dadai karfe 8.00pm su fayal suka isa domin suna da nisha da makarantar .
Amnah tace."kingama fa wai dan nayi sauri kenan nasan dakece da sai munkai 10 kafin mu iso.
Fayal ta yatsine fuska tare da jan dogon numfashi irin damwarkin nan.
Atare suka fito domin nufar inda sukaga students na zaune.
Da isarsu wajen amnah ce ta nufi wajen wata class mate dinsu tare da fadin"wai daman ba afara bane? Tace"hmm eh wlh wai bai iso ba ashe yanada nisa.
Amnah tace"kai gaskiya amman su azabtar damu sunce mu fito da huri Amman gashi shi bai zo ba.
Takoma wajen da fayal ta tsaya domin kuwa fayal bata kula kowa askul din inkaga tayi magana da amnah take toh .
Shiyasa tun wasu nashishshige mata har sun gaji sun rage shiga harkarta domin kuwa yan kwana su take.
Da ta iso guri zakaji Anfara cewa ga yar girman kai nan tazo kowa yana fadan albarkacin bakinsa.
Wasu suce tana birgesu .
Wasu kuwa haushi take basu .
Amnah nazuwa tace."hm wai ashema bai iso ba.
Fayal tace"what!
Duk sammakon nan dakikasa mukayi?
Alallai ma wannan mutum min ya isa. Ai naga ba dole bane practical dinko?
To wallahi baranyi ba nafasa komawa gida zanyi.
Nina tsani wulakanci arayuwata yawani sa an ajiye mutane kaman kaji..
gashi har rana tafara fitowa mtsw.
Amnah tace."haba fayal kinama mutane uxuri mana .
Kinsan mai yatsayar dashi kuwa?
Fayal tace"mtsw nikinga tafiyata wallahi har kai na yafara ciwo.Innaje zan turo driver yakawo miki motar.
Amnah tace."hmmm shikenan ai .
Fayal ta."figa mota aiko duk tabade mutanan gurin da kurah.
Mutane suka fara cewa."tir dai da hali irin naki
Ita kuwa batama san mai suke ba tayi tafiyarta.
ita kuwa Amnah ta koma wajen wata yar ajinsu Khadija suka zauna.
Fitar fayal keda wuya Amsard yashigo makarantar.
Da shigowarsa usman yazo yashiga dashi ciki.
Khadija kawar amnah tace"kai Amnah gaskiya yayarnan taki batada hakuri gashi daga fitar ta har ya iso.
Amnah tace."hmm wlh haka take ni bansan wani irin hali fayal kedAShi ba.
Suna cikin hira akazo kiran mutane domin shiga bayan kowA yashiga.
Amsard yaga wajen mutum daya babu yace"wa usman gurin waye wannan?
Sannan usman yayi bincike akaga ashe wajen fayal ne.
usman yazo Yafadawa Amsard fayal ce. dakuma dalilin tafiyarta.
Ran amsard yayi mutukar baci domin yatsini mace mai girman kai.
Acewarsa matan mesukedashi da hardasuyi girman kai.
Yayi murmushi yacewa usman kabarni da ita i will teach her a lesson
DAMUGANI KOWANI MATAKI AMSARD ZAI DAUKA AKAN FAYAL??