BABU RUWAN SO

PAGE* 19-20

by @xayyeesherthulhumaerath

------------------------------------------------------------------

*WASHE GARI*

su fayal suntashi da huri domin tafiya scul Domin daman yau ne zasu gama practical dinsu.

Bayan sun kammala komai sunyi wanka sannan suka shirya cikin shiga iri daya bak'a doguwar riga tare da farin gyale farin takalmi da farar jaka.

Amnah ce kadai ta tsaya yin kwalliya duk da dai bame yawa tayi ba itako fayal daman ba yi take ba iyaka karshen kwalliyarta shine tashafa farar hoda da farin manbaki.

Amman duk da haka kyanta kara fitowa yake sai kaga kamanma intayi kwalliyar muni zatayi.

Bayan sungama shirine sukayi breakfast karfe takwas daidai sannan suka nufi mota domin fayal jiki yayi sauki sose kaman ba ita bata jiya ba lafiya. Amnah ce ke driving dinsu itako fayal sai tunanin abinda zatawa Amsard yau take.

Da isarsu makaranta akace musu ae yau lecturern bazai samu damar zuwa ba yayi tafiya so dole sai yadawo sucigaba.

Dan haka ynzu zasu cigabada lectures ne.

Ita dai fayal bataso haka ba domin kuwa yau taxomasa da tsarabar rashin mutunci ita practical dinma bai dame taba akan shirinta daya baci.

Fayal tacewa Amnah"kinga fa mutuminnnan baida mutunci fa".

Amnah tace"haba fayal yanada uxurine fa".

Fayal taja tsaki sannan ta huce ajinsu.

Sannan Amnah tabi bayanta.

๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’– *malesia*

Amsard ne zaune adakinsa yafito DAga wanka yashirya cikin kananun kaya bak'in wando bluen riga sannan yasaka glass dinsa na likitoci.

Ankawo masa abincinsa sannnan yaci .

Bayan yagamane yadauko wayarsa yakira usman.

Bayan sun gesane usman yace"yauwa yallabe bani labarinku kai da madam".

Sai da Amsard yaja numfashi domin shi harma yamanta dawata wai fayal. Sannan yace"kai dai baka mantuwa wallah".

Usman yasheke da dariya sannan yace"eh din naji nidai abani labari".

Amsard yakwashe duk abinda yafaru tsakaninsa da fayal yafawa usman.