BABU RUWAN SO

PAGE* 24,25

by @xayyeesherthulhumaerath

-----------------------------------------------------------------------

Amsard yagama abincinsa yaci kuma sannan yayi lafila tukun ya kwanta barci.

Suma su fayal sunci abinci tukun sukaje kwanciya.

Anan ne fayal take ta tunin Amsard dayaki zuwa azyciyarta tace kodai ma tsoro yajine yace zai tafi wajen aiki ana nemansa tana ta tunani dai iri iri daga karshe kuma tace"toh ma ina ruwana dashi mtsw".

Batasan maganarma tafito fili ba sai ji tayi Amnah ta shek'e da dariya . Sannan tace "aiko da ruwanki tunda kina tunaninsa".

Rain fayal yabaci dan haka taje dogon tsaki sannan ta kwanta.

Sai tajima ita kanta haushin kanta take.

****WASHE GARI****** ๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–

Da Asusuba Amsard yatashi yayi sallah sannan yayi wa kansa breakfast . Yayi wanka sannan yashirya tukun yayi break kafin 7 har ya kammala komai nasa sai tafiya asibity.

Da isar sa asibity akasanar masa Da ai feshen din sa ta farka .

Aiko yayi farinciki da jin hakan . Batare da bata lokaciba yaje yaduba sannan yamata tambayoyi tukun yakoma office dinsa.

yau gaba daya fayal ta tashi jiki ba kwari ita kanta batasan meke damunta ba ita dai kawai taji jikinta ba kWAri .

Dan haka tanayin wanka ta zumbula doguwar riga sannan ta dauko hijab da glass dinta tasa .

Ko breakfast dinma takasa yi su momy sun tambayeta menene Amman sai dai tace musu bakomai.

Tun suna tambayarta har suka gaji sukayi shiru.

Ahaka suka tafi skul itada Amnah .

Fayal sai faman tsaki take wanda ita kanta batasan dalilin hakan ba.

Ita kuwa Amnah me zatayi banda kallo . Azuciyarta kuwa cewa take"da alamu kinkusa chaza hali mu huta dan inAga kinkusa fadawa tarko".

Afili kuma tayi murmushi abinta.

Fayal ko sai sake yamutsa fuskarnan take ga tsaki.

Ahaka suka isa skul ba mai wa wani magana .

duk da dai daman hakan dabi'ar fayal dince . Amman nayau din yafi nakullum.

Sun isa skul wajen 8 dan haka har anfara lectures ma Amnah tashiga sannan tace"excuse sir".

Sai da yabata izinin shiga tukunna tashiga .

Ita kuwa Fayal batama fito amotar ba sai ynzu duk da tasan sunyi letti Amman ko ajikinta .

Tafiya take kamar bazata taka kasa ba .

TaNa zuwa tashige lecture room din ko sallama babu.

Shiko lecture yace"tafita mai a aji tabari sai takoyo sallama tukun tadawo.

Aiko hakan ko ajikinta Dan hakama yasa tacigaba da tafiya kamar wadda kwai yafashe mata aciki.

kowa yakoma da kallonsa gareta ahaka har tabar ajin.

shiko lecturern sai da yazabga tsaki sannan yace"wallahi duk mace me irin wannan halin tausayima ni take bani gwara ku gyara halayenku ku huta.

Sannan yacigaba da lectures dinsa.

Amnah azuciyarta kwatakwata bataji dadin abin da fayal tayi ba domin koda yaushe infayal tayi wani Abu kanta yake dawowa sai yan ajin sutamata habaici.

Itakuma batason hakan Shiyasa kawarta guda dayace akaf makarantar.

Fayal tana fita tayi mota tabude baya ta kwanta abinta ita har taji makarantar tafitan mata akaima.

KOMai yasa? Ohooo Amsar da taba kan ta kenan.

Ahaka har tafara barci abinta.

๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–

Amsard yaga yau ba aiki sose a office dan haka yafara shirin komawa nigeria gobe.

MIsalin karfe 2 Yakira usman yafada mai insha Allah gobe zai dawo .

SAnnan usman yace"toh Allah yasa nidaman na zaqu kadawo aciga ba da drama domin naga mutuniyar ma amota ita kadai DA alama dai yau ma ankuma da wani kenan".

Amsard yace"hmmm ai wannan yar sai dai Allah yakyauta Amman fa karka damu nakusa saita ta".

USman yasa dariya sannan yace"toh nidai kullum inama fatan sa'a ".

Amsard yayi dariya shima sannan yace"kadai ji dashi ageshemin da uwargida".

USman yace"aiko zataji domin nafara bata labarin dramar ku".

Amsard yace"kace kasani a faifai kenan". Usman yasa dariya.

SAnnan AMsard yace"nidai sai anjima inashiri ne". Sukayi sallamah.