PAGE* 26,27
---------------------------------------------------------------- Bayan usman sunyi sallama da Amsard .
Sai Amsard yacigaba da shirinsa nakoma wa nigeria.
Abangaren fayal kuwa tun karfe 9take barci sai 1 tafarka daidai da fitowar su Amnah kenan.
Amnah nafitowa ta hango motarsa abin yabata mamaki dan batayi tunanin ganin fayal ayanzu ba.
Batama ga abin mamaki ba sai da taga fayal da alamun tashi daga barci.
Azuciyarta tace"ikon God".
Niko nace sai kallo.
tana zuwa tace"fayal lafiya kuwa".
fayal ta yamutsa fuska har kungama kenan?
Amnah tace "eh wlh lecture usman ma yasanar damu insha Allah jibi zamu cigaba da practical dinmu".
Fayal tace"kwaji dashi dai".
Amnah tace"hhhh ai shiyasa kikaga mun fito da huri yau yasin da sai 6 inaga har sai kingama kumburah ma'.
Fayal taja tsaki sannan tace"ni kishigo mutafi ko malama".
Ita dai Amnah dariya take da dariyarta tashiga mota suka nufi hanyar gida.
Sun isa gida bakowa dahike momy ta tafi aiki shikuma dady yayi tafiyama.
Dan haka suna isa fayal tayi sallah tukun tadawo kichin domin daura abinci.
Duk irin halin fayal na kyaliya hakan baisa iyayenta sun sakalta ta ba .
Aduk sanda momy zatayi girki sai ta tabbatar da su fayal da Amnah na wajen.
Dan haka fayal tashiga kichin domin musu girki .
shinkafa da wake dafa domin itama shine abincin datafi so arayuwarta.
Tana kammala momy tadawo dan haka suka hadu a dainin domin cin abinCi.
Ananne momy tace"yadai maganar practical dinnaku gashima naga yau kun dawoma da huri".
Amnah tace"umm momy wai jibi zamu cigaba kinsan gobe sunday shiyasa kawai akabari sai monday inAga yau me practical din zai dawo shiyasama yau bamu jima a lectures ba".
Momy tace"owk su fayal ansha aiki ko maganar ma baza amin ba".
Fayal ta yamutse fuska sannan tace"hmmm momy". Daganan bata kara cewa komai ba . Sukuwa momy da Amnah suna hira sunacin abincinsu.
Itakuwa Fayal yadda batason yin magana haka bataso nakusa da itama su cika yi dan Haka da anfara cin abinci taga su momy sunfara bude dandalin hira sai tayi sauri tabar wajeN.
Toh yau mah haka tayi tayi tatashi tabar wajen.
Dashike sunsaba da halinta hakanma baya damunsu.
Fayal tana shiga daki Tadauko wayarta tafara game.
Domin datayi magana gwarah tata karatu ko game.
Suko su momy sai dasukaji sunyi nak tukun Amnah ta kwashe kayan da tA bata tatafi wanke'wanke .
Sai momy afalo dake danna wayarta.
Megadi yashigo da sallamarsa. Momy ta Amsa.
Sannan me gaji yace"wai wani ne yace nakira masa fayal".
Shikansa asanyaye yake maganar domin yasan halin ta sarai. Bayau akasaba zuwa wajenta ba tana hulakanta mutane . Amman duk da haka kaman karuwa masoyanta suke.
Sai da momy taja dogon nufashi. Domin ita kanta tsoron yartata take.
Sannan tace"waye ke kirinta?. Megadi yace"wani ne yazo amota yana waje ".
MOmy tace"owk kace tana zuwa".
Megadi yace"toh sannan yatashi yatafi jikinsa asanyaye.
Momy takasa motsi sai tunanin yadda zata bullowa yartata take.
Daga karshe dai kawai ta yanke shawarar zuwa tasanar mata.
Momy nashiga ta tarar da fayal kwance tana game awaya.
TAyi sallama sannan fayal ta dago tukun ta Amsa.
MOmy tace"fayal ".
Fayal ta dago. Tukun momy takara da cewa dadynki ya aiko wani dan abokinsa kije ku gesa".
fayal ta yatsina fuska sannan tace momy ni wallahi agajiye nake kawai Amnah taje su gesa".
DAkyar momy tajawo hankalin fayal dataje su gesa tukun tayarda.
Momy tabar dakin gaban ta sai faduwa yake. Azuciya kuma tana addu'ar Allah yasa adace yau".
FAyal tadauko hijjabinta harda daukowa Amnah likaf tasa.
Tana fita!.