PAGE* 28
----------------------------------------------------------------------
fayal ta fito tana fitowa ta hango wani saurayi Tsaye tare da abokinsa sai washe baki suke.
Taja dogon tsaki tukun azuciyarta tace"hmm shirme".
Tafiya take kaman bazata karasa garesu ba.
Hakanne ma yasa basusan da fitowarta ba.
Sai da ta isa dai dai wajensu tukun suka ankarah.
Saurayin nan ne yafara magana dace"hajiya bako sallama ne?.
Abokinsa yace"kokuma tayi bamuji ba dai ko?.
Saurayin yace"oh hakane fa ashe kanata jana da hira ne".
Suka sheke da dariya dukansu .
Ita kuwa fayal abin ya kona mata rai taja dogon tsaki.
Tukun saurayin yafara dacewa"toh hajiya nidai sunana ibrahim Anakira da khaleel ni dan kasuwa ne kuma ina karatune har yanzu Kuma ni dan garinnan neh".
Yakara jan numfashi sannan yace"naganki ne wallahi Askul dinku nikuma naga bai kamata namiki magana acen ba shiyasa naxo nan".
Agaskiya inasonki sokuma na aure.
Khaleel sai washe baki yake waishi adole Amsa yake jirah.
Duk maganar nan yake itA fayal ko ajikinta ita haushinsa nema yakamata.
Gawata dariya dayake kamar anmasa kyauta.
Duk azuciyarta take ta fadin hakan.
Abokin khaleel yace"kodai kunya hajiyar tamu take neh".
Shiko khaleel har yanzu dai washe baki yake.
Sai Alokacin fayal tadago ta kare musu kallo sannan taja dogon ciki tafara tafiya.
Shikuwa khaleel da Abokin sa tsayawa kawai sukayi suna ganin ikon Allah.
Tafiyarta take hankalinta kwance kamar ba abinda yafaru .
Sai da tashiga cikin gida tukun abokin khaleel yace"kaga dai abinda nke gujemaka kenan ko?
Sai da akace kar muzo kowa yafadamana halinta Amman kai kaki yarda wai adole sai ka gwada sa'arka toh ai kuwa yau ga sa'arnan kazo gun wadda ko kalloma bamu isheta ba".
Shidai khaleel yakasa magana domin har ynzu abin mamaki yake basa.