BABU RUWAN SO

PAGE* 31,32

by @xayyeesherthulhumaerath

-----------------------------------------------------------------------

Fayal ce tarafara tashi tabar Amnah tanacin abinci Haka kawai taji tana farincikin da ita kanta batasan dalilinsa ba Ahaka ta wuni cikin farinciki wadda ko su momy sai da abin yabasu mamaki.

Kawai binta suke da ido Sai kallo.

Amsard ya iso jigawa karfe 4.00 ina isowa yakira usman awaya domin yazo yadaukesa.

Batare da bata lokaciba kuwa Usman ya iso Yana isowa Amsard yahangosa dan haka yasa yakarasa wajen sa.

Amsard nazuwa yace"a lallai usy kanaji dani naga saurinka fah".

Usman yayi murmushi sannan yace"ba dole naji dakai ba tunda kakusa angwancewa".

Amsard yadan daki bayan usman sannan yace"kai ko baka da dama gwara kai nikam muje kasaukeni amasaukina insamu inyi wanka dan wallahi nagaji".

Usman yayi dariya sannan yace"owk oga muje".

Usman ne ke driving dinsu cikin kwanciyar hankali yanata jan amsard da surutu . Shiko Amsard sai dai yayi murmushi Amman duk da haka usman bai bar magana ba sabida yasaba da halin abokin nasa.

Ahaka har suka isa hotel din da amsard ke sauka tukun sukayi sallama tare da fadin cewa gobe sa hadu a skul cewar Amsard. Usman yace"owk".

Amsard nashiga dakinsa yayi wanka sannan yayi sallah tukun aka kawo masa abinci yaci.

****WASHE GARI*****

Fayal tunda tatashi sallar asuba bata koma barci ba tana ta shirin skul tare da girka breakfast .

Ita tayi musu komai nakaryawa sai da ta kammala ma tukun Momy tafito domin daurawa aiko da mamakinta taga har fayal ta gama komai.

Taji dadi sose domin tana ganin yarta takusa dawowar rayuwa kamar takowa.

Momy tace"sannu fayal".

Fayal tayi murmushi tukun tace"morning momy".

MOmy tace"morning daughter.

Sannan fayal tace"momy bara naje natashi Amnah tayi wanka nimA nayi sai muyi breakfast din".

Momy tace"owk".

Fayal taje tatashi Amnah tukun tashiga wanka bayan ta fito neh Amnah ma tashiga tayi.

Bayan sun kammala shirinsu tsab tukun suka nufi falo domin yin breakfast.

Sai dasuji duk sunyi da dam tukun suka tashi domin tafiya skul Suka mawa momy sallama tamusu addu"a sannan suka tafi mota.

Dasuka shiga mota Amnah ce ke driving ita kuwa fayal sai murmushi take tana tunani.

Amnah tadago ta kalleta abin yabata mamaki azuciyarta tace"oh kome yasami fayal ne ? ohoo tabawa kanta Amsa sannan takara dacewa Allah yasa dai lafiyarta kalau".

Abangaren Amsard ma tuntuni yagama shirinsa nazuwa skul .

Yana fitoWa yahau motarsa domin jiya daddare usman yabadaa motar aka kawo masa .

A dai dai Amsard dasu Fayal suka iso school.

Amsard ne yafara fitowa ya shiga ciki.

Sannan su fayal suka bishi abaya amsard yana shiga yaga usman har angama shirya kome kawai shi ake jirah.

Su fayal ma sun shigo.

Batare dA bata lokaci ba kuwa akafara practical .

Sunfara tun wajen 8 amman gashi har 3 basu gama ba duk kowa yagalabaita.

Dan haka Amsard yace suje suyi sallah sai adawo .

Amsard da usman suka tafi masallaci sukayi sallah aiko suna idarwa usman yace"kai oga yamaganar dramar nan tamune ?. Amsard yayi murmushi sannan yace"dadina dakai zumudi Amman karka damu yau za afarah".

Usman yagyara zama da darisa sannan yace"dakyau". Amsard yace to ai sai katashi mutafi ko?. Usman yatashi domin komawa.

Suna tafiya tare kamar bazasuyi ba sai dariya usman yakewa Amsard. Ahaka har suka isa. Suna shiga akacigaba da aiko ba tsayawa domin Amsard yarike wuta akan dole sai sun kammala yau.

Ai ko sai karfe 6.00 suka gama.

Amsard yahango fayal zaune Amota tana jiran Amnah taje karbo wani book dinta.

Amsard yataka asannu har motarsu yama fayal sallamah ta Amsa. Tadago takallesa tukun ta sunkuya.

Amsard yace"yajikin naki fatan kinsamu sauki dai ko?.

Fayal tace"dasauki jiki Alhmdlh". Amsard yace"ko zan iya samun numberki?. Fayal ta tsinci kanta dason bada numberta Batare da bata lokaciba tafada masa .

Sannan yayi saving Amsard yace"toh nagode malamah fayal".

Fayal sai dataji wani tsigar jikinta natashi sabida yarda yafada sunan.

Murmushi kawai tamai shima yamata sannan yatafi. Yana tafiya Amnah ta isa taga hucewarsa dan haka take ta tunanin kardai fayal ta wulakantasa neh ahaka har ta isa motar.

Tana shiga kuwa ta ga fayal sai wannan murmushinfa take nayanzuma har yafi nada ita dai abin yaKara kule mata kai kenan.

Shikuwa Amsard yana karba ya nufi inda usman yake domin yalabe ne yaga me zai wakanah.

Yana zuwa usman yace"yana kanata murmushi ne kodai andace ne?.

Amsard yace"da alamu yar nan har tafara fadawa tarkona".

Anan amsard yama usman bayanin komai . Aiko usman yayi farinciki da jin haka domin burinsa kenan.

Abangaren fayal kuwa har ynzu dai murmushinan take amnah sai da tagaji da kallon ikon Allah tukun tafara tuki.

Ita kuwa fayal har ynzuma batasan wai amnah kallonta take ba domin tunaninta yayi zurfi.

Ahaka har suka isa gida.

Amsard yabi usman gidansa sai da sukayi sallahr magriba da isha sannan suka shiga ciki wajen Ameenah.

Ameenah tayi farinciki da ganin amsard abokin tsokanarta.