BABU RUWAN SO

PAGE* 36,37

by @xayyeesherthulhumaerath

------------------------------------------------------------------------- Dan haka tace"owk ba matsala sai anjimah".

Sukayi sallama acikin nutsuwa.

Bayan sun kammala wayar Amsard yaji gaba daya yanayinsa ya chanja . Sai wani farin ciki yake wanda shikansa bai san meya jawo hakan ba . Shidai kudurinsa akan fayal da bannne yanzu kuma yaji yanayinsa daban ba irin wanda yatsara ba.

Kome yasa hakan,ohoo Yake tambayar kansa.

Abangaran fayal ma jitayi farincikita na karuwa amman ita ayanzu tafara tantamar kardai so ne yakamata . Azuciyarta tace"aa fa kawai yana burgeni neh".

Niko nace zama kiyi bayani.

Tundaga ranar kusan kullum misalin karfe 8 nadare amsard yake kiran fayal awaya su gesa bayan sun gesa haka dukansu zasuyi shiru na yan mintuna sannan suyi sallama kowa kuma yana begen juna.

Duk da basu da wata hirar dasuke tabukawa awayar amman haka bai sa Amsard yadaina kiran fayal awaya ba Haka kuma itama fayal duk sanda bataga kiransa ba takan shiga damuwa.

Yanzu gaba daya fayal ta chanja tafara sakewa da mutane amman duk da hka dai bata dai na wannan yatsinar fuskarba kuma rashinson maganar nan ma na nan sai dai tadan ragu.

Momy da dady tare da Amnah bakaramin farinciki sukeba sanadiyar ganin fayal cikin walwalah.

Shiko Amsard har yanzu dai miskilancinsa na nan amman kuma bai baryiwa mutane murmushin nan dayasaba ba.

Yauma dai kamar kullum fayal da amnah sun gama shirinsu tsaf domin tafiya skul.

Yau kam amnah batajin dadi sose dan hka fayal ce tayi driving dinsu.

misalin karfe 8suka isa Suna zuwa kuwa ana shiga lectures Dashike yau lectures din safe suke dashi kadai hakan yasa suka fito karfe 2.

Suna fitowa Fayal tace ma amnah"inaso muje zan siyo wani story book kinga yau mun fito da huri".

Amnah tace"owk toh muje nima naduba".

Sukaje wani shagon littafai.

Fayal tana zuwa tafara dube-dube bataga littafin da takeso ba.

Chan kuma taga Amnah tazo tace"nikam kinga nina sami nawa fadamin sunan wanda kikeso natayiki nemah". Fayal tace"muga nakin". Amnah ta bata

Aiko fayal nakarba taga an rubuta true love story Fayal tace"woow toh ai wannan nake nima". Amnah takasa magana dan mamaki wadda ta tsani jin kalmar love ma wai itace me cewa tana neman love story!

Ita dai kawai kallon fayal take

Fayal takara da cewa"muje nima kidauko min ko".

Sai alokacin amnah tace"owk to rike wannan ni bara nadauko wani". Amnah taje tadauko sannan ta biya .

Suka koma mota sannan suka kama hanyar gida.

Wajen karfe 3 suka isa gida suna zuwa sukayi sallah sannan fayal tashiga kichin domin daura abinci.

Ita kadai take aikin domin amnah tana dan zazzabi.

Dan haka ta yanke hukuncin daura musu indomie suci kawai daga baya sai ta daura girkin dare.

Aiko tana kammala indomien tadaura girkin dare sannan tadawo sukaci ita da Amnah.

Sai wajen karfe 6 sannan ta kamala girkin dai dai da dawowar momy da dady.

tana gama taje tayi wanka tukun dukansu sukayi sallah magriba .

Sannan suka ci abinci SAi bayan sallar isha kowa yatafi daki.

FAyal nashiga daki tafara karanta littafinta Tana karantawa tana kallon agogo .

TAga har karfe 9 amsard bai kirata ba. Tun tana boye damuwarta harta fara bayyanata.

Tayi kwokarin mayar da damuwar amman takasa . Dan haka ta yanke hukunci kiransa kawai.

Tadauko wayar zata kira takasa. Taga abindai ba yi dan haka ta dan nah kirah.

Takira wayarsa akashe taki shiga kwatakwata.

Duk da haka bata daina kira ba har wajen 10 amman yaki shiga.

tacigaba da kira har wajen 12 sannan taga tashiga.

Tashigan tana ringin amman ba adauka ba. Sai da takira wajen sau 9 ba adaga ba ata goman ne taci sa a aka daga .

fayal tace"assalamu alaikum".

Adaya bangaren akace"wa alai salam". sai da fayal taji numfashinta yafara daukewa domin muryar mace taji awayar .

meyasami amsard? Shin wacece tadaga wayar?

Sai kubiyoni domin jin yazata kasance.