PAGE* 38,39
-------------------------------------------------------------------------
Fayal takasa maganar da hajiya momy taji shiru sai tace"me wayar bai da lafiya neh yana barci kuma yanzuma nina kunna wayar".
Sai alokacin fayal tace"ayyah ina hini?.
hjy momy tace"lafiya lau".
Fayal tace"toh ya mejikin?
Hjy momy tace"dasauki inya tashi ma zan fada masa kin kirah".
Fayal tace"owk sai da safe ".
Ahaka sukayi sallama.
gaba daya daren ranar fayal takasa barci sai tunini take tarasa me yake mata dadi daga tace wannan sai tace wanchan.
Gaga karshe kuma tace"toh kodai sonsa nake?
Ta tambayi kanta sannan takara dacewa"aa shakuwace kawai".
Ahaka sai wajen karfe 3 nadare tukun fayal tasamu damar yin barci.
Shiko Amsard dama tun safe yatashi da matsanecin zazzabi hakan yasa momy takira family doctorn su yadubasa yamasa allurai shiyasa tunda yasamu barci bai farka ba har cikin daren.
Momy nagama waya da fayal ta tsinci kanta cikin farinciki mara misaltuwa domin ita aganinta yanzu danta har yasamu lokacin kula wata budurwa da har zata kirasa.
Dama alokacin tazo dubasa ne sai ta kunnah wayar domin tasan za ane mesa aiko tana kunnawa taga kiran fayal yashigo.
Dan haka tana gama waya da fayal ta nufi dakinta domin kwantawa.
*WASHE GARI*
Fayal takasa tashi sallar asuba sana diyar rashin barcin datayi jiya dan haka sai da Amnah ta tasheta tukun tayi sallar .
Amman gaba daya jitake bata da lafiya ga tunanin amsard fal azuciya.
Dan haka tana idarwa tashiga wanka tayi kozataji dadin jikinta sannan takoma barci. Dayike yau weekend ne.
Amnah tazo kiranta suyi breakfast kawai taga sai rawar sanyi take abin yarazana Amnah dan hKa tayi gaggawar kiran momy aka kira doctor .
Batare da bata lokaci ba doctor ya iso yadubata tabata magani da allurai sannan tasha tea sai ta koma barci.
Abangaren amsard kuwa yau yatshi da kwarin jiki .
yau duk su sahala da sameer na gida . Dan haka suna tashi suka nufi dakinsa .
Sai rigima suke masa shiko da hike ba me magana bane inyayi daya biyu sai yamusu murmushi.
Anacikin haka hjy momy tashigo dauke da breakfast din Amsard.
hjy Momy tace"toh ba za dai abar min da ya huta ba ko?.
Sahala tace"uhumm hjy momy nikadaice fa yarki".
Sameer yace"tab ni ne kuma ma nitafiso".
Sai alokacin Amsard yace"bawani nan dukanku ba ya"yan hjy momy bane ku ya'yan Alhaji neh".
Tuni sahala tafara shagwaba ita adole itace yar hjy momy.
Ita kuwa hjy momy sai dariya take musu tana farincikin ganin iyalenta cikin walwalah Daga karshe tace"haba auta aike ta da bance Kai kuma sameer aikasan kai yayanta neh dan haka kaci girma".
Samer sai murna shi adole yayan sahala ne.
Suko amsard da hjy momy sai dariya suke musu.
hjy momy tace"in kutashi muje ga breakfast dinku chan kai kuma son ganaka nan kaci".
SAmeer yace"ai nima ance yayan sahala ne toh sai akaimin daki irin na bros".
Amsard yace"a lallai ma sameer wato kanmu daya ko?
Dukansu suka sa dariya sannan suka fita.
Abangaren fayal kuwa sai wajen karfe 2 ta farka tasamu tayi wanka sannan tasha kosta.
Amsard sai alokacin dayagama kome tukun yadauko wayarsa yana duba wa aikowa sai gashi yaga kiran fayal DAtayi jiya yaga andauka dan haka Yace"kar dai momy ce tadauko".
YANata sakye sakye azuciyarsa.
DAi dai da lokacin da fayal tadauko waya
TAfara kiran amsard Tana kira kuwa taci sa,a yashiga bajimawa ya dauko.
tare da yin sallamah
FAyal sai da taji wani farinciki tare da annaushuwa najin muryarsa datayi.