PAGE* 40
-------------------------------------------------------------------------
Fayal ta amsa masa sallamarsa tare da fadin"ina hini? Ya jiki?.
Sai da amsard yayi murmushi sannan yace"lafiya jiki kuma dasauki".
Fayal tace"toh sannu Amsard yace"yauwa ashe hjy momynace tafadamiki bnda lafiya ni sai ynzu ma dauko wayar shine naga kiranki".
Fayal tace"hmm eh".
Amsard yace" yanaji kema kaman baki da lafiya?.
Fayal tace"eh wallahi dan zazzabi nake".
Amsard yace"ayya ashe dukanmu daya ne to Allah dai yabamu lafiya".
Fayal tace"Ameeen".
Sannan sukayi sallamah cikin nutsuwa tare da farinciki.
suna gama wayar nan fayal taji kamar ba ita ke rashin lafiya ba gaba daya ta ware walwalarta ta dawo .
Ba shiri ta dauko book dinta tacigaba da karantawa.
Sukansu su momy sai da sukayi mamakin warware wartah.
Amsard suna gama waya da fayal ya kira usman awaya.
Duk da sunyi waya da ranA amman hakan bai sa sun fasa ta dare ba sai Da sukayi kamar yadda suka saba.
washe gari
Jikin amsard dana fayal yakara sauki sose.
Misalin karfe 2 na ranah usaman yakira amsard awaya.
Amsard nagani yadauka cikin farnciki tare da masa sallamah.
Usman ya amsa sallahma .
Bayan sun gesa usman yke cewa"ya dramar nan neh anya tana tafiya daidai kuwa?
Amsard yace"hmm kedai kabari kawai ashe mu mun mata mummanan kallo ne ba haka take ba yarinyr tana da saukin kai fa" .
Usman yace"ba wani nan kawai kai dai ka fada tarko neh".
Amsard yasa dariya tare dacewa"Allah magNar gaskiya nke fadama kuma maganar tarko kam nafada daman inaso nakiraka musan nayi".
Usman yace"Alhmdlh wallahi naji matukar dadi to yanzu ka fada mata neh?.
Amsard yace"a'a wallahi ni tsoro nkeji".
Usman yace"haba dai saikace ba namiji ba haba mutumina karka badamu mana".
Amsard yace"hmm bazaka gane band".
Sai da usman yatabbatar da amsard ya gamsu zai yi abin da yace sannan yasamu sukuni.
Dazasuyi sallamah amsard yama usman alkawarin insha Allah zai mata magana yau da dare.