BABU RUWAN SO

PAGE* 47

by @xayyeesherthulhumaerath

------------------------------------------------------------------------- Fayal tace"na amince!"

Tana fadar hka kuwa takashe wayar wai ita adole kunya takeji.

Amsard yayi matukar farincikin jin hakan.

Hakan kuma yasashi kiran usman awaya. Bayan sun gesa amsard yake cewa"ya maganar fadawa Alhajin ne?

Usman yace"oh mutumina ba hakuri toh yanzuma ina hanyar katsina ne domin nazo nasanarw da alhaji. Nasa nabaka mamakine hakan yasa ban fada ba".

Amsard yace"woow amman gaskiya ka kyauta kuma Naji dadi".

Usman yace"toh nidai karka dameni sai na iso kawai".

Amsard yace"a iso lafiyA".

Sukayi sallamAh

Usman yashiga tunani wai yanzu har amsard ne yake iya damuwa akan mace! Abinda da ko kallo basu ishesa bama!

Oh ikon Allah kennan Gaskiya wanda baisan so ba bai iya farawa ahankali ba.

Da wannan tunanin usman yacigaba da driving.

Afannnin fayal kowa farincikinta kara karuwa yake sai murna take moy da dadyma sai farinciki suke barin dadyma yaji dadin jin labarin zuwan amsard.

Misalin karfe 1usman ya isa katsina ba inda yahuce illa gidansu amsard.

Usman yana isa cikin gida yashiga batare da bata lokaci ba. Aiko yana shiga yaga su sameer n wasa dayake weekend ne kowa nagida .

Suna ganinsa sahala tashiga ciki da gudu tana hjy momy ga yah usman nan yazo.

Hjy momy tace"wo kice yau munyi babban bakwo agidan namu".

Tafito shiko sameer tuni yayi dakin amsard yasanar dashi.

Atare amsard d momy suka fito palo. Momy nafadin a lallai yau munyi bAbban bakwo".

Shiko amsard sai washe baki yake.

Usman ya geshe da momy. Ta amsa cikin sakin fuska tare da tambayar ya iyalen?.

Usman ya amsa dacewa"suna lafiya".

Hjy momy tace"toh sahala adaukowa yaya abinci ko?. Sahala tace"owk momy.

Sahala taje tadibowa usman da amsard abinci atare sukaci.

Sai da suka gama sannan sukatafi massallaci sukayi sallah .

Bayan sun dawo neh usman kecewa "hjy momy ina Alhaji ne?

Momy tace"aiko ynzu yadawo daga sallah yana daki".

Usman yace"toh bara naje mu gesa" .

Momy tace"toh abokin naka yaraka ka mana".

Usman yace"toh suka tashi shida amsard.

Suka shiga dakin dady bayan sun gesa ne sai amsard yace"yana zuwa".

Zai fita sai usman yace"ka dan cewa momy tazo zAmuyi magananeh".

Amsard yace",ok". Yana fita sai yakira momy sannan ya nufi dakinsa.

Momy na shiga usman yace"toh daman alhaji sanadiyar zuwana ba nakome bane illa muna neman alfarma da aje jigawa nemawa abokina aure".

Hjy momy tayi saurin cewa"wani abokin naka?!

Usman yayi murmushi sannan yace"amsard".

Alhaji da hjy momy atare sukace"Alhamdulillah".

Alhaji yakara dacewa"gaskiya naji dadin jin wannan kalmar daga gareka dole nabaka tukwici".

Hjy momy tace"kodai nina basa".

Usman yayi murmushi sannan yace"alhaji zan turoma da number baban yarinyar sai asa ranar zuwa" .

Alhaji yace"hakanma yayi".

Sannan usman yace"bara naje muyi sallamma nakoma domin banson nayi dare".

Alhaji yace"ah tsaya ga tukwicin ka motace wadda jiya aka kawomin daga dubai .

Bansan me zAnbaka ba ga key din ayi hakuri da wannan ".

Usman yakasa rufe baki anacikin hakan momy tace"niko kabani account no dinka zan turo maka da million daya".

Usman yace"woo momy 'alhaji bansan dame zan gode muku ba".

Sukace bakome ai munsan kafi karfin hakan ma awajenmu.

Cikin farinciki sukayi sallama sannan yaje yasami amsard domin yin sallam ah.