PAGE*50
-------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------- Washe gari tunda safe Alhaji ya fito ya kira hajiya momy yace " Kishirya zamuje gidan Alhaji babba".
Tace "to Alhaji" tashiga ciki ta kimtsa sannan ta fito suka fita.
Ashe duk abun nan da ake amsard yana jinsu yanata murna azuciyarsa. Suna fita shima ya fito falo ya zauna dan yakira fayal. Kafin ya fito da wayarsa naji tana ringing yana fiddo ta yaga princess ce nan yaji wani sanyi aransa, ya daga tareda fadin. " Aminci, karamci, halacci da mutunci sukara tabbata agareki ya saraunmiyar kyawawa" Saida fayal taji wani sanyi batasan lokacin data lumshe idoba.
Tace " tareda kai habebe na. Fatan rabin raina ya tashi cikin koshin lfy "
Amsard yace " ina lfy kanwata daman yanzu nake shirin kiranki"
Fayal tace" ai naji hakan azuciyata shiyasa nace bari narigaka"
Amsard yace" gaskiyane Masoyiyata Ammanfa yau kin dan ban mamaki"
Fayal tace "uhum uhum yayana menayi uhum "
Amsard yace" uhum uhum kalamanki sukaban mamaki ashe kanwar tawa gwanace a kalaman soyayya "
Fayal tace " uhum yayana ai soyayyarka ce tasani nazama haka domin banma san yanda akai naji ina furtasuba"
Amsard yace" Lallai kanwata kice naci gari? ".
Fayal tace "sosaima."
Amsard yace " gaskiya naji dadi babyna."
Ahaka sukayi sallama zuciyar kowa cike da shaukin kaunar junansu.
A bangaren su Alhaji da hajiya momy kuwa. Sun isa gidan Alhaji babba. Sunkuwa yi sa'a Alhaji babba baifitaba. S Suna shiga Alhaji babba yataso da murna yace " Alhaji kaine yau agudanmu ba ko waya Allah dai yasa lfy"
Alhaji yace " wlh kuwa Alhaji ai abundake tace damu yafi qarfin waya"
Alhaji babba yace" to to zauna zauna Allah yasa lafiya"
Alhaji yace" wannan tafiyar ta dankace Alhaji. Nazone mu tattauna don danka amsard yasamu mata"
Alhaji babba yace " Alhamdulillah kai amman gaskiya nayi murna sosai kace amsard angirma kai masha Allah "
Alhaji yace " to yanzu halinda ake cikima so nake muje neman auren nasa a jigawane, yaushe kake ganin yakamata muje"
Alhaji babba yace "ai ba abun jinkiri nan gobe goben nan zamuje insha Allah. Asanar dasu kawai"
Ahaka sukayi bankwana akan gobe insha Allah zasuje jigawa neman auren amsard.
A bangaren usman kuwa yana isa gida. Ya yi sallama Amina ta taso da gudu tatarbesa cikin murna tace "honey katafi kabarni inata zullumi fatan kadawo lfy."
Usman yace " lfy kalau uwargidana nazo miki da Albishir abokina ankusa angwabcewa. Kuma Dadynsa yabani sabuwar mota hajiya momy kuma tabani one million boron Albishir."
Amina tace" kai Alhamdulillah gaskiya nima naji dadi matuqa kace su yaya amsard ankusa zama ango".
A bangaren su fayal kuwa. Dasafe amnah tatashi tacewa momy "yau inada Albishir da zan baku keda Dady." Momy tace "Kaii harkinsa nafarajin dadi dagaji Alkhairi ne. To fadamin"
Amnah tace" noooo mommy sai mun je yin breakfast zakiji "
Momy tace " to shikenan "
Bayan su momy da amnah sungama hada kayan breakfast. Momy takira Alhaji suzo an shirya breakfast.
Sun zo an zazzauna amman fayal bata fitoba dady yace "wai ina fayal dita? " Amnah tace "tana daki." Dady yace" jeki kiramin ita tazo mu karya"
Amnah tace "to dady"
Amnah tatashi tanufi dakinsu tana zuwa tatarar da fayal sai dariya take tana wayarta da amsard. Amnah ta kalleta tace" ohni su fayal har an zama yan gari a birnin love. Toki taso muje dady nakira muyi breakfast "
Fayal tace " to ganinan zuwa. " Tai sallama da amsard tatashi suka tafi. Suna shiga ta zauna inda tasaba zama akan dining set ta gaishe da dady da momy.
Suka amsa cikin farin ciki. Dady yace" ina kika shige ne ko barci ake? " Fayal tace"a a dady kawai ina zaunene. " tafada tana kallan Amnah tana mata alamar tayi shiru karta tonata. Amnah tai shiru kawai tana murmushi.
Kusan mintuna 10 dafara cin abincisu sai amnah tace " dady da momy albishirinku".
Sukace" goro atare suna dariya" fayal najin haka tai zunbur tamike ta ruga ciki tana rufe fuska domin tasan me Amnah zata fada. dukkansu suka fashe da dariya.
Amnah tace" dady zakuyi baqi gobe "
Dady da mumy sukace" baki kuma Suwa zasu zo mana?"
Amnah tace "dady su Abban amsard ne zasu zo neman auren Fayal" Dukkansu cikin farinciki sukace "Alhamdulillahi kaiii masha Allah. Allah yakawomu lokaci Kaii gaskiya munji dadi"
Momy tatashi dagudu tashiga ciki tana kiran fayal fayal zozo manaaa 'yataaaaaaa.