SAI NA AURI MARUBUCI (Nafseen)
PAGE 1/2
BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM.
_*FEJIN FARKO SADAUKARWANE GAREKU FAUZIYYA TARE DA JANNAT YAR BABA KUJI DADINKU🥰🥰🥰*_
........Wata Yar matashiyar yarinya na hango da bazata huce shekara goma sha bakwai ba aduniya, kwance take tana barci cikin nishadi da walwala domin da zaran an kalli yadda yanayin murmushi ke bayyana afuskarta wannan ka dai ya isa laburta cewa tana cikin yanayi na farinciki,ta kankame littafin Hausa akirji tamkar tana gundu a kwace mata, mafarkine Wanda ta sabayi kamar kullum Amman ko wanne da salonsa ko na yau din ya yake? Bara mu lekye cikin mafarkin Nafeesa.
"Nafeesa kin San cewa ba jin cewa akwai Wata 'ya Mace da zan so kamarki? Kina jin cewa zan iya furta Kalmar so ga Wata 'ya Mace bayan ke?, Hmm babu tantama cewa ke ce zabina sannan kuma kece burina,ina miki so fiye da yadda majnun ke son laila,ina kaunarki fiye da yadda kifi ke bukatar ruwa domin rayuwa." Cewar Nafseen da ke zaune gaban Nafeesa.
Gyara zama tai tare da kara kura mai kallo tai murmushi kan ta fara da, "Da ace ana Iya kidaye adadin soyayya a sikeli na tabbata cewa wadda nake yi maka bazata taba kidayuwa ba,kamar yadda Dan Adam ba zai Iya rayuwa batare da ruwa haka Nima nake jin cewa ba zan iya rayuwa batare da kai ba, ka zamemin jinin jikina,numfashina da walwalata, ada nakan ji cewa ka fi karfina ba zan taba samunka arayuwata Amman wai yau nice tare da kai har kake furtamin Kalmar so? Dan Allah Nafseen ka rayu da ni karka barni karkacemin wannan mafarkine nake yi."
Rik'o hannunta ya yi,yana kokarin yin magana.
Karaf Mama ta shigo tare da bugawa Nafeesa dundu abaya.
Sambatu take,"Ka kara cewa kana so na ko da sau dayane Dan Allah kar ka tafi."
Dukan da Mama ta kara kai mata ne ya sa ta saurin razana tare da dawowa hayyacinta, "Mama kin kuran min shi, Mama kice ya dawo yau ya fadamin cewa yana sona mama Dan Allah kice ya dawo."
Tsaki Mama tayi, "Ki bar min wannan shirmen tun kan na kai miki mari maza tashi kije kiyi sallah wawiya kawai."
Kara kallon dakin tai da kyau ta ga da alamar gaske dai daga itane sai Mama, kuka kawai ta fara tana, "Mama wallahi in ban gan shi na aure shi ba mutuwa zan yi, ni kan sai na AURI MARUBUCI." ta kara fashewa da kuka.
Wani irin bakin cikine ya kara tirnik'e mahaifiyarta ta, ta fice batare da tace komai ba illa azuciyarta da take fadin, "Ban San wannan wani irin bala'in so bane ga mutumin ba ba a taba gani ba, daga karatun littafi kawai, anya kuwa ba aljanune suka shiga jikin Nafeesa ba kuwa? Ya Zama dole in sanar da Abhee abin da ke faruwa adaren yau."
Ta shige daki.
Ita kuwa Nafeesa kara kyankyame littafin tai tana kuka sai da tai mai isanta kan ta dauro alwala tai sallah, tana idarwa ba abun da ta fara rok'a illa Allah ya nuna mata marubucinta Nafseen Sanan kuma Allah ya bata ikon auransa.
Bayan ta kammala addu'ar tashi tai ta fita waje da littafinta ahannu, zama tai afilin tsakar gidan na su tare da chok a hannunta Zane ta farayi tana waka Wanda da farkon zanen duk Wanda ya kalla zai dauka cewa shirme take zanawa,Amman ahankali kyahun zanen na fitowa,da mamaki duk da kasancewar Nafeesa ba ta San Nafseen ba Amman tsaf yanayinsa da kamaninsa take zanawa,ba musu duk Wanda ya San Nafseen kuma ya ga zanen Nafeesa zai dauka cewa ta San shi kuma kyakkyawan sani ma, azahirin gaskiya ko bata taba ganinsa ba bin abun da zuciyarta ke rada mata kawai take ya yin zanen tundaga farko har karshe.
Kallonsa ta tsayayi tana mai farinciki ji take tamkar na gasken ne agabanta, cikin littafan da ta fito da su ta dau daya mai suna YAR AUTA NA JAMEEL NAFSEEN, Karatu ta fara cikin nutsuwa da zakuwa akowanni feji ganin ta riski gaba, labari Indai na shi ne ko wani irin salo na tafiya da zuciyar Nafeesa.
Gabadaya hankalinta ya tafi ga karatun kaninta da ba zai huce shekara Takwas bane ya fito yana buga boll ta gabanta ya huce ba tare da sanin Sa ba har ya goge mata zanen Nafseen.
Ji tayi ajikinta hakan ya Sa ta saurin kallon kasanta gani tai tamkar na gasken ne ya yi hatsari hakan ya sa ta Jan dogon numfashi tare da suma awajen nan take.
✌️YAWAN SHARHI YAWAN TYPING
Urs Xayyeesherth _*SAI NA AURI MARUBUCI📝📝📝*_ _(Nafseen)_ 12/1/2021
_GAJERAN LABARI📝_
NAH
AISHA MOHAMMAD SANI (Xayyeesherthul-humaerath)
_*SAI NA AURI MARUBUCI...Kirkiraren labarine, mai dauke da nishadi na mussaman, al'ajabi tare da ban tausayi,tsantsar soyayya da kauna mai ban mamaki*_