SAI NA AURI MARUBUCI (Nafseen)
PAGE 8
BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM
*Wannan fejin Sadaukarwane Gareka Yaya Jamilu (Nafseen) tare da Antyna Iklima❤️Ina mai yi maku fatan alkairi tare da cigaba da rayuwar aurenku cikin farinciki,amana da Yarda,Allah Sa Anty Sa sambado mana an biyu🤣amin takwara*
Karatun tai hankali kwance sunfito ke nan dai,dai gate din makaranta zasu fita wata Yarinya da zata kai shekara ashirinne ta dumfarota da sauri, bangaje Nafeesa tai har sai da glass dinta ya fadi kasa, "Maga tayi ai,ke har kin isa ki tabamin Mutansir a makarantarnan,yar matsiyata, ko me kika masa ma ya nace miki oho, da alama dai ba a barsa haka ba, anga 'Ya'yan masu dukiya ana Neman hanyar shige masu Amman tsoro ya hana,to wallahi ahir dinki, ko da gaske ko da wasa naji cewa kina son Mutansir kin Riga kin kade yarinya ba ma ke kadai ba hatta Shi wannan driban da wannan ma'aikaciyar asibitin,makauniyar banza da wofi,wata yar shila da ke ,ko inama abun so ajikinnan ? Mtsww." Cewar Fatima tare da cigaba da yiwa Nafeesa wani mummunan kallo.
Tunda Nafeesa ta durkusar da kanta bata dago ba,ban da hawaye ba abunda ke zuba daga idanunta, Magana ta farayi cikin ruwan Sanyi, "Habibbty Bani Glass din nasaka bana gani."
Ita kan ta Maryam sai da hawaye ya fara bayyana daga fuskarta tsabar tausayin Nafeesa da take.
Karfan Glass din Nafeesa tai tare da sawa a idonta ta rik'e hannun Maryam suka cigaba da tafiya.
Tsaki Fatima tai domin bata so hakan ba Sam ta lura kamar Nafeesa bataji zafi sosai ba,hakan yasata kara tunkararta cikin sauri tare da shan gabanta, Glass din fuskar Nafeesa ta kwace tare da cigaba da tafiya batare da tace komai ba.
Maryam ba kokarin yin Magana Nafeesa ta rik'e mata baki, "Habbibty kar kice komai, wannan kaddaratace, kisa anafe kawai kar drebanku ya gaji da jiranki."
Kallon kawartata tai cike da tausayi, "A hakan zan Sa ki Anafe bayan nasan ba gani kike sosai ba, ki bari in karbo glass din wajenta sai dreban ya kai mu duka, wani iskancin ma Dan sunga ana barinsune."
Nafeesa ta kank'ame hannun Maryam , "Dan Allah ka da ki tada rikice akaina ni ba yar kowa bace kamar yadda ta Fada Amman na San cewa watarana zatayi nadamar abun da tamin,ni kawai akai ni Asibiti Gun Mammah ta nemamin wani glass din,Idon ciwo yake min habibbty wallahi ciwo ya faramin."
Cikin sauri Maryam ta laluba Jakarta tare da Ciro wani karamin glass , "Sorry Habibbty barin Sa miki wannan kan muje asibitin to."
Bayan ta sa mata glass din haka Maryam ta rik'e Nafeesa suka Shiga mota.
Suna shiga Mota Nafeesa ta Sa hannu ajakarta tare da lalubo wani littafi mai suna *Ajaliin mace* Fasihin marubucin nan nata ne dai ya rubuta, kallon littafin tayi tare da rugumarsa tamkar mutum, wani kayataccen murmushi ta sake,domin ji take duk damuwar da ke ranta ta kau,indai tana tare da littafin da Farincikin ranta ya wallafa,rubutunsa tamkar muryasa gareta,sunansa tamkar hotonsa ne garesa, bangon littafin kuwa ji take tamkar bugun zuciyartane, ji take gabadaya ta nemi damuwar da ke ranta ta rasa,cikin murmushi ta ce, "Habibbty Dan Karantamin kinga bana gani da kyau Dan Allah, kan mu isa."
Murmushi Maryam ma tayi ganin cewa damuwa ta fice daga fuska har zuciyar Kawartata,karban littafin tayi tare da fara karanto mata.
Da mamaki Nafeesa ta haddace littafin tsaf a kwakwalwarta domin kan Maryam ta kai Aya Ita ta karasa mata, Maryam na kuskure wajen furuci zata gyara mata.
"Kai Habibbty ai kin gama haddace littafinnan to miye kuma na sai na karanta miki?"
Murmushu Nafeesa tayi, "Na haddace littafin nan tamkar yadda na haddace Al'Qur'ani mai girma,ko ina kika tabomin zan Iya karasa miki batare da na kalla ba,Amman kin San me? A kullum ina so akarantamin ko ni na karanta,domin aduk lokacin da nake sauraren kalaman banajin muryar kowa akunnena sai na Marubucina,sautin Muryarsa kadai ke sauka acikin kunnuwana, Habibbty mutane da yawa na fadin cewa karyane dan wani ya ce zai iya rasa ransa in ya rasa masoyinsa ko? To ni nasa araina cewa duk ranar da na tabbatar da cewa bazan Taba samun Yaya Nafseen ba, ba makawa zan Iya mutuwa nan take, Ina yi masa so fiye da yadda kowa ke tsammani,in ana maganar soyayya sai kije ana Sa Majnoon da Laiyla to ni ko Kadan basa gabana domin ji nake na ninnkasu natakasu a soyayyata,ko da ace Nafseen ba zai soni ba,akwai wani sirri tsakanina da shi, kuma inada tabbacin ya sani a ko ina yake ma duk da cewa ba mu San juna ba, kin san menene Habibbty?"
Maryam na gyara zama domin jin me Aminiyarta ta zatace dai,dai da lokacin da dreba ya tsaya domin sun iso asibitin batare da ma sun sani ba.
Nafeesa ta ce, "Yawwa Mun Iso."
Suna fita Maryam ta kalli Aminiyarta ta, "Habibbty fadamin sirrin."
Murmushi Nafeesa tai, "Sirrin,kina son jin Sirrin Habibbty?"
Maryam ta ce, "Sosai ma ."
Nafeesa ta ce, "
✌️😁 MY GROUP MEMBERS ANA TARE AYAU MA KUWA? RUWAN COMMENTS YADDA AKA SABA MUTANEN KWARAI😘😘
Urs Xayyeesherth _*SAI NA AURI MARUBUCI📝📝📝*_ _(Nafseen)_
NA XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH
6STARS INDEED✨
_*SAI NA AURI MARUBUCI...Kirkiraren labarine, mai dauke da nishadi na mussaman, al'ajabi tare da ban tausayi,tsantsar soyayya da kauna mai ban mamaki*_