SAI NA AURI MARUBUCI (Nafseen)
PAGE-18
BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM
🥰🥰🥰INA KEWARKU MY GROUP MEMBERS KAMAR YADDA KUKE TAWA SON SO SABODA ALLAH, INA TSAMMANIN GANIN RUWAN SHARHI ALLAH SA KAR KU BANI KUNYA❤️😘
*SADAUKARWA GAREKI LEEMAH😍 GA GROUP DIN REALL SHAXEE FANS, THANKS FOR D LOVE ND CARE*
Dai,dai da lokacin da ya sauka online .
Murmushi ne ya fara bayyana afuskarta, tamkar tana gabansa take jin kan ta alokacin.
Kara gyara zama tai tare da karin sakar wani murmushin mai banbanci da na farkon domin wannan na mussamanne, shagwabe fuska tai tare da yo masa repy mai nunin ga yanayin da take ciki, wato emojin Shagwaba ta fara sawa kan ta ce, "Umm Uncle Allah ni fa jarumace,kuma in ka cigaba da mun dariya kuka zan yi, mu yi baram-baram ba ma ruwana da kai,sai ka ce min SORRY Anty Nafeesa."
tana gama turawa ta kalli online status dinsa minti hudu kenan da saukansa,bataji dadi ba sam har cikin ranta, wani irin yanayi ta tsinci kanta da bata san dalilin hakan ba, rufe datar wayarta tayi kawai tare da daukan Al-Qur'ani ta fara karatu, sai da ta karance Surutul TAUBA tas kan daga karshe tayo addu'o'i nan take taji wani irin sanyi na ratsa mata zuciya tare da shaukin so na mussamman, Murmushi ne ya bayyana afuskarta da ka kanga zaka fahimci cewa tana cikin wani yanayi na mussamman wanda za a iya alkantashi da shaukin SO!
Ajiye Qur'anin ta yi tare da daukan jerin littafan Masoyin nata da ta saba karantawa a kullum batare da ta gajiya ba.
Falo ta fito ta tattarar da Mammah,Sabeer da Maryam sun kunna wani hausa film.
Har zata zauna sai ta tashi tare da gyatsine fuska tana fadin, "wannan kallon naku ma ba bari na nai karatun zai ba gwamda na fita fasej hankali kwance."
ta kare maganar tare da gyara glass dinta.
Ba wanda ya kulata, kamar ance ta jiyo kawai sai taga an rubuta STORY AND SCREENPLAY BY JAMEEL NAFSEEN.
Gabadaya suna gani kallonsu ya koma ga Nafeesa suka bar ta T.V
Wayancewa tayi cikin salon shagwaba tare da tebe baki, "Umm nama fasa fitan,anan zan yi karatun kuma kar kowa ya dameni."
Mammah ta kalli Maryam kan ta ce, "Maryam Anya MARUBUCIN NAN zai yi kyau kuwa? chanja mana wani kawai."
Maryam ta tashi zata chanja Nafeesa tai sauri tare da tare gaban TVn "Ayyah Mammah zai yi kyau wallahi ku tsaya mu kalla nima kallon zan yi shine ya rubuta fa." ta rufe fuskarta batare da ta kara fadin komai ba.
Mammah ta dalla mata harara , "Shi wa? Ammien Abhi ki kiyayeni fa tam."
Nafeesa ta tabune baki, "Umm Mammah ni yau kallo na ke son yi ko abarni ko in fadawa Abhi ya zane mana ke."
Mammah ta sake baki, "Iyeee? Lallai Mamana, Allah shiryamun ke, na san zaki iya hada bom din da yafi hakama asha kallo lafiya."
Gwalo ta ma Mammah tana, "Hhhh Ashe ana jin tsorona ma."
Murmushi Mammah kawai tai azuciyarta tana kara jin son yartata matukar gaske,mussaman inta dubi halin da Nafeesa ke ciki ta fannin Ido tana matukar tausayin 'yartata, abu daya ke kwamtar mata da hankali yadda Nafeesa ke cire damuwoyi aranta, ta nuna kamar komai bai faru.
"Laaah Mammah ba an Hana Anty kallo ba saboda idonta?"cewar Sabeer.
Nafeesa ce ta kallesa cikin sauri, "To daman ni ina kallonne dan dai yau zan yi shine ake bakin ciki."karasa maganar tai tamkar zatayi kuka.
Da sauri Mammah ta katseta , "Miye na kukan? ki rufamun asiri dan Allah muyi kallo na yau dai daya, ni ai ina son ganinki cikin walwala Mamana kinji, oya SMILE."
Tasowa tai daga inda take tana gyara glass dinta ba inda ta nufa sai wajen Mammah kifa kanta tai akan cinyarta tare da dasa idonta ga talabijin din domin yin kallo.
Mammah ta ce, "Allah Mamana mijinki ya shiga uku da son jiki, ni kam anya zakina aiki ma kuwa?"
Nafeesa ta ce, "Umm bayan tare za mu je kina yi mana ko kin mantane?"
Duka Mammah ta daka mata abaya , "Mara kunya kawai."
Dariya Nafeesa tasa, "Umm daman so nake ki bar ni nai kallona."
kallo suka farayi abin Mamaki yau ga Nafeesa gaban Tv na kallo har bata so wani yayi magana akatse mata, ban da murmushi ba abun da ke bayyana afuskarta da ka ganta zaka fahimci cewa tana cikin yanayi mai dadi, mussaman in ta ga ALI NUHU wanda yafito da sunan jaruminta NAFSEEN aciki.
Suna cikin kallo dif nefa suka dauke huta,gwalalo ido Nafeesa tai tare da karewa falon kallo shin da gaske daukewan sukai ko kuma ya?.
ta shi tai ajikin Mammah ta zauna tare da yin tagumi tamkar wadda akayiwa rashi,hawayene kawai ya fara bayyana daga fuskarta.
Mammah tsabar Mamaki ta ma rasa bakin magana,Sabeer kawai kallon Antyn nasa yake, Maryam ce ta tashi tare da karasawa ga aminiyarta ta.
Cire mata hannun tai daga tagumi tana, "Habibbty miye haka? miye na kukan kuma?"
Shiru Nafeesa bata da niyar yin magana.
Maryam ta cigaba d magana tare da share mata hawayen, "Haba Habibbty kan kallo wai kike kukan nan? to kalli Mammah kiga itama kukan take."
Gabantane yafadi ras jin cewa Mahaifiyarta na zubda kwalla
Can kuma tintsirewa da dariya tai ta tashi tana tsalle, "Yau dai naga kukan Mammahna, daman ban taba gani ba ysn."
Da taga abun dai da gaskene Mammah kuka take tsayawa tai shiru kan ta durkusa gaban Mammah,hawaye ta fara share mata, "Mammah na, Allah wasa nake ki daina kuka kinji in kika cigaba nima zan yi,am sorry Mammah." ta kare maganar cikin shagwaba tare da riƙè kunnuwanta da hannu.
Mammah ta kawar da kanta daya barin, Nafeesa ta riƙè hannun mahaifiyarta ta tana,"Smile Lovelyn Abhi, ni ba ruwana inya dawo ya ga kina kuka dariya zai yi yasin,kuma ma yace shi baya son mata mai kuka kinga kenan za akaro mana Anty ko?" ta wangale baki alamar murna zance ko mamaki ma.
Harara Mammah ta fara bin Nafeesa da shi kan ta tashi tana, "Ki rabani da maganar Wata Anty in ba so kike inyi jajjagenku daga ke har Abhin ba."
Nafeesa ta bita tare da rungumar bayanta, "Mammahna tafi ta kowa, Am so sorry please, ban san zaki shiga damuwa bane kin san da ba zan yi hakan ba, Ki yafemun kinji,kada Allah ya yi fushi dani sanadina kin zubda hawaye, Ki yafemun sannan kiyi murmushi kinji."cikin salon shagwaba take maganar
Mammah ta juyo da Nafeesa gabanta tare da kallon fuskar 'yarta ta cikin salon so da kauna.
"In sha Allah,Allah ba zai yi fushi dake ba tamkar yadda nima ba zan yi fushi da diyar kirki ba,ina son ki Mamana,Allah raya mun ku cikin aminci,ba na so kina damuwa da kananun abubuwa kinji,Abhinki ba kowa bane sannan Mammanki ma ba kowa bace,duk da na san kin sa hakan aranki amman a kullum ina kara yi miki tunine domin ban da burin da ya wuce rayuwarki ta inganta, na san wa ki ke so,na san burinki amman ba abunda muka isa yi,mun barwa Allah zabi,ba zan hanaki bin muradin ranki ba,amman ina so ki sani ki kara sani mutuncin ki na 'Ya mace ya fi komai mahimmanci arayuwarki,ki rike kan ki,ki san darajar kan ki ako ina ako da yaushe kuma,ki lura ,a yanzu kam ke ba yarinya bace kinji ko Mamana." Cewar Mammah tana shafa kan diyarta ta.
Murmushi Nafeesa tayi , "Maddallah da samun uwa ta gari,ina alfahari da ke Mammana,ina sonki,so mara misaltuwa,Allah sa inga tsufanki."
Mammah tayi gaba tana, "Allah shiryamun ke ni ma din ba abari ba a tsokanar,Maryam kawar nan taki tana bukatar ganin likita."
har cikin ran Maryam tsarin gidansu Nafeesa na matukar birgeta, ba su da kudi amman sunada wadatar zuci ga rayuwa cikin farinciki gwanin sha'awa maganar Mammahne ya katse mata tunani, ta sake murmushi tana fadin, "Mammah ai inaga Asibiti za mu kai Habibbty aduba mana ita."
Nafeesa ta tebe baki, "Yasin ras nake, na ma fi ku lafiya ehee."
Maryam ta ce, "kyaji da shi nikam ki rakani, muje in tafi gida."
Nafeesa ta ce, "Tab ai sai dare."
Har Mammah zata shiga daki ta juyo tana, "Aa fa kul ta tafi gida yanzu, kina gani anbarta ta kwana tun jiya yau kuma ta kai dare,maza rike hanun Sabeer ya rakaki ku rakata."
Nafeesa ta shagwabe fuska tana kokarin kuka, Mammah ta kara da, "Laa kar ki, kuskura Gobe ai da kwai makaranta kwa hadu acen amman yanzu kam Maryam na da bukatar komawa gida."
Ba ason ran Nafeesa ba haka ita da Sabeer suka raka Maryam ta hau nafe. Tana komawa gida sallah tayi tana idarwa kuwa da zumudinta ta dauki wayarta tare da kunna data...
Urs Xayyeesherth _*SAI NA AURI MARUBUCI📝📝📝*_ _(Nafseen)_
*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° _Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu._ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ***
NA XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH
27 feb 2021 10:5am
✨6STARS INDEED
_*SAI NA AURI MARUBUCI...Kirkiraren labarine, mai dauke da nishadi na mussaman, al'ajabi tare da ban tausayi,tsantsar soyayya da kauna mai ban mamaki*_