SAI NA AURI MARUBUCI (Nafseen)

PAGE-19

by @xayyeesherthulhumaerath

BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM

*Jinjina Gareka Haruna Birniwa👏ina godiya da goyon bayanka gareni tare da tallafamun wajen dauruwa a hanyar rubutu mafi inganci,Allah ya kara basira da haza❤️*

*Saudaukarwa gareku Deeymusah,tare da Walida Rano🥰ina yinku irin sosai dinnan*

*SAI NA AURI MARUBUCI FANS GROUP,Duk da kasancewar gajren fejine amman ina tsammanin ganin ruwan sharhi🤷‍♀️*

Messages ne suka fara shigo mata, zuba ido kawai ta fara yi tare da jiran sakon abincin ruhinta, da mamaki har sun gama shigowa amman ba ta ga nashi ba, sannan ko nuna alamar yana online ko ya zo online din ma babu.

Wata ajiyar zuciya Nafeesa ta sauke, ta dafa hannu a bangaren kanta, tsintar kanta da karanto INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN ta yi. Nan take ta ji wani sanyi a ranta.

"Allah kenan!"

Abun da ta iya furtawa kenan, sannan ta kara riƙe wayar hannunta gam, group din marubuta ta leƙa, ai ko ban da zuba ba abun da marubutan ke yi kamar 'ya'yan kanya, hira cikin nishadi da barkwanci suke, wani sa'ilin su juya wa'azi ko wani bangaren na daban a cikin wannan group, kai duk tsegumin da kuke tunani to ya fi karfin hakan.

Murmushi ta sake a zahiri tare da fara bin hirar cikin group din, aranta tana sa ran cewa za ta iya gamo ko cin karo da hirar masoyin nata amman kash, har ta kai ga karshe ko alamar gilmawarsa ba ta gani ba.

Sallama ta yi cikin group din, cikin sa'a kuwa a amsa mata wajen mutane biyar a lokaci guda.

Cikin hirar da suke kawai ta tsinduma inda aka sa daya daga cikin marubutan a gaba da tsokana, SAIFULLAHI MUHAMMAD LAWAN duk da kasancewar yana da baki amman taron dangin da aka yo masa ya sanya shi yin tsit, ita kuwa Nafeesa abun nema ya samu tuni ta shige masa fadan tare da ba kowa amsa daidai da shi.

Dariya ya fara yana mai jin dadin ya samu 'yar team, tun dai ana gabzawa har da karshe fadan ya juye izuwa barkwanci da hira mai cike da nishadi da walwala, har ta rufe datarta kasancewar dare kuma gobe tana da skul, a zahirance bata da wata damuwa amman cikin zuciyarta damuwa ce fal domin tana da muradin jin lafiyar sahibinta, sai da ta yo alwala tare da sallah raka'ah biyu kan ta kwanta cike da yin addu'o'i kamar yadda ta saba kullum.

A bangaren NAFSEEN kuwa, gabadaya aiki ya yi masa yawa ba shi da lokacin wani abu ban da aikin da ke gabansa, a duk lokacin da aiki ya masa yawa irin haka bai samun damar hawa social media bare ya yi chatting sai tsakar dare yayin da komai ya lafa masa, mussaman in bai gaji da yawa ba.

Yau ma kamar kullum, karfe sha-biyun dare daidai ya kunna datar wayarsa domim duba sakonni yadda ya saba.

Abun mamaki da bai karewa dangane da Nafeesa Cikin barcinta hakan ya zo mata, abun da ke faruwa azahiri.

Daukan wayarta tai kamar yadda shi ma ya yi, messages din da yake tsammani gun abokan aikinsa ya fara dubawa tare da yi masu reply kan ya dawo kan 'yan uwa da abokan arziki.

Idon Nafeesa na kan Numbersa mussaman da ta ga yana yi mata typing gyara zama tai ji take tamkar ta kwato ta ji abun da yake rubutawa alokacin, ban da murmushi ba abun da ke bayyana a fuskarta.

"Iyee Antynwa? See dis rigima girl, an ki ace Antyn." Reply din NAFSEEN.

Cike da yanayi irin nata na shagwaba ta ce, "Ni ko? To ma ka daina kulani, kuma ba ruwana da kai, Uncle mai kan gwangwanni kawai."

Dariya maganarta ta ta ba shi har cikin ransa ya ce, "Sorry, dawo Momy Nafeesa ma ba Anty Nafeesa ba, shikenan ina mun shirya?"

"Yeess mu kulla tunda da mun kunce ne ma." Nafeesa ta yi masa reply cike da dariya tana mai jin dadi.

Ya ce, "Ok, to amman waye mai kan gwangwannin? Momy Nafeesa ce ko? dan ni dai na san Uncle ba ya da kan gwangwani."

"Umm... Umm... Ni dai yasin ba ni ba sai dai Uncle, shi ne mai katon kai irin na gwangwani."

Murmushi ya saki, har a zuciyarshi yana jin dadin yanda suke chat da yarinyar nan, ga barkwanci kamar 'yar mahauta, ga uwa-uba shegiyar shagwaba. Ya sake murmishi a karo na biyu kan ya tura mata da, "Byee Momy mai kan gwangwani aiki zan yi yanzu, kuma kin ga dare yayi sha biyu daidai, a yi barci kar Mama ta miki fada ko ki kasa ta shi sallah."

Ba ta so hakan ba ko kadan domin ji take zata iya kwana sannan ta yini in dai suna hira ne ba tare da ta taba gajiyawa ba, amman a yanzu ba yadda ta iya ko dan farincikinsa yadda ya bukata dole ta sauka.

"Nyt Bye, bye Uncle mai kan bera, kuma yasin ni ba na makara ni ke tashin limamin unguwarmu ma." ta rubuta ta tura masa, ji take rabuwa da shi tamkar rabuwa da numfashinta.

Batare da ta bare ta ga sakon da zai turo ba ta kulle data tare da gyara kwanciya, ta so kam ta ga amsarsa amma gudun kar ya fahimci tsananin kaunar da take a gare shi ya sa ta sauka, tana jin wani sashe na zuciyarta yana mata radar ta sake kunna datar amma ta basar saboda tsaro.

Duk hirar da Nafeesa tai kar ku ji mamaki in na ce maku a cikin barcinta ne batare da ta farka ba har yanzu, to shin da wa Nafseen ya yi chatting? Nafseen ce ko kuwa?

Al'amura boyayyu suna da yawa wanda muna bukatar saninsu.....

Kada ku gaji🥰ku biyoni a feji na gaba,love yhu oll❤️

Urs Xayyeesherth[3/16, 2:23 PM] Xayyeesherthul-humaerth: _*SAI NA AURI MARUBUCI📝📝📝*_ _(Nafseen)_

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° _Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu._ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

***

NA XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH

✨6STARS INDEED

_*SAI NA AURI MARUBUCI...Kirkiraren labarine, mai dauke da nishadi na mussaman, al'ajabi tare da ban tausayi,tsantsar soyayya da kauna mai ban mamaki*_