SAI NA AURI MARUBUCI (Nafseen)

PAGE-21

by @xayyeesherthulhumaerath

BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM

_*Koda ke kadai mahaifiyarki ta Haifa kada ki taba sawa aranki cewa bakya da yan uwa, tabbas akwai yan uwa aduniya da suke kasancewa tamkar garkuwa garemu yayinda wata matsala ke kokarin kunno mana,Ina matukar alfahari tare da farincikin kasancewata da ke ANTYNA FARIDA MUSA (SWEERY) bana da kallaman godiya agareki domin sunyi karanci illa fatan alkairi😍*_

🙌😂 _*SAI NA AURI MARUBUCI FANS GROUP DA SAI NAGA MARUBUCI FANS GROUP ARADU INGA RUWAN SHARHI FIYE DA TAMBAYAR DA KUKEMUN KO IN TAFI HUTU😍*_

Kallonsa kawai ta tsayayi cike da Mamaki, Wanda ya bayyana karara afuskarta, ba kowa ta gani ba face NAFSEEN tsaye yana sake mata murmushi ba tare da ya ce ko mai ba.

Ta kasa tafiya kokarin fara Jan kafarta tai domin karasawa garesa, gabadaya ratansu ba zai wuce taku takwas Amman tafiya take ta kasa karasawa garesa, ga shi kusa da ita Amman Sam ta kasa iskansa, har yanzu ban da murmushi ba abun da yake sake mata, daga fuskarsa har kayan jikinsa ban da sheki ba abun da suke.

Daga hanunsa ya yi yana mata nunin cewa tazo hakan ya bata damar mika nata hanun kamar yadda ya bukata.

Ta mika kenan yana kokarin rikyewa karaf ,Mammah ta ce, "Nafeeesa Miye haka? Kina hankalinki kuwa."

Juyawan da zatai ba tare da ta ankare ba Ashe har ta shigo cikin gida, ba tare da taba Mammah amsa ba,saurin juyowa tai domin mika hannunta ga muradin ranta,Amman kash bata ga kowa ba.

Kuka ta fara tana fadin, "Mammah ya tafi,Mammah kin koreshi,Dan Allah ki ce ya dawo Mammah zan bisa, wallahi ina son shi."

Dafa kanta tai tare da kokarin faduwa da sauri Mammah ta karaso tare da tallefata, addu'ah ta fara karanto mata alokacin cikin sa'a kuwa Nafeesa ta fara dawowa, cikin raunanniyar murya take fadin, "Mammah zan kwanta ki kai ni daki."

Murmushi Mammah tai , "Ok Ammien Abhi Amman Please kada ki wannan barcin mai dadewa ban so kinji?"

Girgiza mata kai kawai tai.

Mammah ta kaita daki,ta kwantar da ita tare kunna mata karatu.

A bangaren Nutasir kuma tun da ya shiga mota yana tafiya ba abin da yake tunawa sai Nafeesa .

ba abun da yake tunawa illa ranar da ya fara ganin Nafeesa.

tun daga farkon kallon ta dayayi a makaranta zuwa abun da ta masa a yau , da wannan tunanin ya iso wani unguwa koda kallon unguwan kasan na masu arziki ne layin gidan su ya shigo daga farkon layin yake danna horn da karfinsa domin dabi'arsa kenan kowa yaji wannan horn din yasan Mutasir ne yadawo.

mai gadi ko tunda ya fara jin horn ya fito da gudu ya fara kokarin budewa Dan yasan idan Mutasir ya iso be bude ba yau shima yasan makomansa .

Yana isowa ya shiga da gudu domin baya driven a hankali bare ma yau dayake jinsa duk zuciyan shi ba dadi Talle mai gadi yana gaidashi Amma ko kallon sa beyiba nan da nan yasha jinin jikin sa.

Dan haduwa gidan su Mutansir ya hadu tunga wajen gidanma bare an shiga ciki .

apartment biyu ne a gidan na farkon ya nufa yana shiga Babban falon ya fara Momy" Momy" ya zauna akan kujera daya daga ciki ya kwantar da kansa tare da rufe idonsa wata matashiyar yar aiki ne ta fito ta ce, " tana sallah." Ransa ba dadi ya nufi apartment dinshi toilet ya shiga ya watsa ruwa ya dawo kan gado ya kwanta tareda Jan dogon numfashi.

Tabbas ya kamu da son Nafesa har yana jin idan har baj aureta ba komai zai iya faruwa .

yanzu taya zai tunkare ta gashi tsoron ta yake sosai da ace yasan zai so Nafeesa irin haka da bai mata abinda ya mata. Ban da juyi ba abun da yake agadon domin ko idonsa ya rufe ita yake kallo yanayin ta da yadda take magana yana kara birgesa a gaskiya, Dady ya dawo asan abinda za,ayi .

Abun da yake ta sakawa acikin zuciyarsa kenan. L

WAYE MUTASIR ?

Mutasir Dane ga Alhaji Abdallah Adam da hajiya balkis Ahmad tun bayan auren su suke son haihuwa Amma Allah bai basu ba sun jima a haka tun suna rai har suka cire Alhaji ba Irin abin da beyi ba amma shiru sai kawai ya fara tunanin aure Dan Kawai yasamu haihuwa Allah da ikonsa kuwa sai ga hajiya da ciki zokaga murna wajen Alhaji tun daga wannan lokacin ya daina fita ko Ina yana tayata zama Hajiya ta samu kulawa sosai har Allah yasa ta haihu aka samu namiji Wanda yaci suna Mutasir, Alhaji ya dauki so da kauna da duk wani burin sa na duniya akan dansa akan sa ba da Wanda ba zai iya Fada ba. koda ko hajiya ce, duk da bata son Abun da Dan nata yake Amman ba yadda ta Iya domin kuwa tsaf Alhaji ya shirya rabuwa da duk Wanda yaso taba masa farincikin Dansa.

haka Muta sir ya taso a sangarce besan fada ba duk abinda yayi shine daidai momy na iya kokarinta Amma Dady yafi karfinta kuma yaro duk Wanda yake nuna abin da yake yi shine daidai to yafi son shi idan an masa fada zai ga kaj ba masoyin shi bane .

Daddy yaso kaishi kasar waje karatu Amma shi yace yafi son a bashi yayi anan a haka ya Karasa secondary harya shiga tertiary institutions inda ya hadu da Nafeesa, wannan kenan.

Maryam ko Nafe na ajiye ta motan Kabir na parking a kopan gidan su sarai ta ganshi Amma ta basar dashi tana kokarin shiga gida yazo da sauri yasha gabanta, " haba Maryam mesa kike min haka ne kina wahalar min zuciya, narasa gane me zanyi miki ki gane irin son da nake miki kodai saj ranan da kikaji ance na kamu da ciwon zuciya ko ko na mutu zaki yadda da cewa ina kaunarki, Maryam Dan Allah ki taimaka min ki Kara bani Dama kiyi hakuri."

Maryam ko kallo bai isheta ba ta ce, " Malam matsa zan wuce inaga kaman gidan mune ko?"

Ya ce, " Hakane Maryam Amma ki saurareni Dan Allah ." kafin tayi wani abu Kabir ne ya Saka gwiwowinsa a kasa yana , "Maryam ki tausayi min please."

ta bi ta gepan sa ta shiga gida Kabir besan sanda hawaye ya fara zubawa daga idanunsa ba kaman ba namiji ba da kyar ya kai kansa mota yaja tare da barin unguwar jiki asanyaye.

Maryam na shiga gida Ummi ta dara mata fada danko duk taji abin da Maryam tayi ma Kabir

"Maryam ba kyau wulakanta mutum fa idan ma baki sonsa bata haka zaki masa ba ki bi shi a hankali,ni zai ban koya miki wulakanta kowa ba."

Maryam ko ban da hawaye ba abin da take Dan ita bata ga Me zatayi da soyayya ba bare tasa wani aranta harta bashi kulawa bazata iya ba gaskiya daki ta shiga ta zauna tana jin haushin Kabir har cikin Ranta, ko Nafeesa dake Soyayya ma tausayinta takeji hakan ya sa take kallon cewa soyayyarma bakidaya bata lokacine.

******

Nafeesa ko bata farka ba sak da aka fara kiran sallah magrib Mammah taji dadin hakn sosai Dan yau baccin beyi nisa ba sallah tayi duk tana jin jikinta ba dadi yana mata ciwo,ko abinci bataci ba ta dauko wayarta tare kunna data...

Urs Xayyeesherth [3/16, 2:24 PM] Xayyeesherthul-humaerth: _*SAI NA AURI MARUBUCI📝📝📝*_ _(Nafseen)_

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° _Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu._ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ***

NA XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH

✨6STARS INDEED

_*SAI NA AURI MARUBUCI...Kirkiraren labarine, mai dauke da nishadi na mussaman, al'ajabi tare da ban tausayi,tsantsar soyayya da kauna mai ban mamaki*_