SAI NA AURI MARUBUCI (Nafseen)

PAGE-23

by @xayyeesherthulhumaerath

_*JASMINE,RANO ON TOP,MAMAN SHUKRA,MR MUBARAK,AISHATUL-HUMAERAH,MAMAN KHRT,MAMAN IHSAN,NAFEESAT,DAMA SAURAN DANA MANTA🚶‍♀️🤸‍♂️DUK KAN KU YAYA JAMILU (NAFSEEN NA GAIDAKU KYAUTA😂AMMAN FA YACE BAN DA NAFEESA😓ABUN TAUSAYI*_

BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM

Tsorata, abun ya bata mamaki kawai jikintane yafara rawa, Maryam ido ya yi zuru-zuru ga dalibai an fito kowa idonshi Kansu.

Wata irin kara Nafeesa tai nan take aka ajiye Mutansir gefe, tausayinsane ya kamata nan take,ta karasa gareshi duk jikinsa ya kurkuje.

Ganin Nafeesa gabansa maimakon yaji tsoro ko yaji da radadin jikinsa,murmushi ya fara sakewa yana kallonta.

Ita kuwa cikin dimuwa take fsdin, "Sannu kaji, nikam dai ban ma komai ba,ka gani ko? Sannu ban San waya Tabaka ba."

Kasa magana yayi ban da murmushi ba abun da yake saki.

Maryam ce ta karaso tare da rikye hannun Nafeesa tana, "Habibbty mu tafi kinji."

Nafeesa ta fara kuka, "Habibbty kin gani fa,ina ni ban masa komai ba."

Maryam ta ce , "Eh tashi muje."

Dakyar Maryam ta janye Nafeesa daga gun Mutansir ba su ma tsaya lectures din Yamman ba,Maryam ta lura da yanayin Nafeesa hakan yasa kawai suka nufi gida.

Mutansir kuwa sai da aka kai shi asibiti.

Fatima takaici kamar tayi yaya, kara duban kanta tai,shin wai da me figiggiyar yarnan tafita ne, da har mutansir zaiki ta,tsaki taja azuciyarta tana , "Sai shegen karyar iskanci ga dukkan alamu yarinyarnan matsafiyace, Dan haka nima yanzu aka fara daga ita har Mutansir din sai na basu mamaki wallahi."

****Suna fara tafiya Nafeesa ta mance da abun da ma ya faru gabadaya ta dawo hayyacinta tamkar ba ita ba, dukkansu sunyi shiru sai kallon hanya suke kawai,tsayuwar da mai nafensu yayi ne ya ankarar da su.

Kabeer ne ya tsayar da mai nafe din.

Maryam na ganinsa taji wani Abu ya tokareta akirji tsaki tayi azahiri sannan ta kawar da kai.

Nafeesa ta kalle shi cike da fara'ah , "Ah Yah Kabeer kai ne?"

"Eh Wallahi Nafeesa na ga yau kun kammala da wuri gashi nima gida zani mai zai hana in rage maku hanya?" Cewar Kabeer

Nafeesa ta ce, "Ayyah Yah Kabeer Karka damu wallahi ai mun kusa gidanma."

Kabeer yace, "Eh ai ba Matsala ko Mallam? Nawane kudin in ba da?"

Mai nafe yaga alamun za Adan samu cikin Sauri ya ba da amsa, "Eh yallabai."

Cikin Fada Maryam ke magana,"kinga Habibbty nifa bazan Iya ba,kai me nafe in zaka kai mu ka kai mu haba, wannan ai wulakancine in baxaka ba mu sauka ai ga wasu nan ma hau.".

Maganar take tana kokarin fita a nafen.

Nafeesa ta rikota, "Miye haka Habibbty? Ni dai ban sanki da irin wannan halinba,kuma sai mun hau motar Kabeer ko kinki ko kinso in kuma ba za ki hau ba ki ta tafi ni ya kai ni."

Ko da wasa Maryam bazata Iya barin ta ba domin tana gudun bacin ran Nafeesa fiye Da nata.

Ba yadda ta Iya haka ta shiga,da zata shiga baya Nafeesa ta ce aa, bata da zabi da yafi na Nafeesa hakan yasata shiga Amman fuskarnan amurtuke.

Kabeer ya ba mai nafe dubu daya kan ya dawo suka fara tafiya, murmushi ya yi yana kallon Maryam ya ce , "Niko Nafeesa kun San cewa in kuka bata rai ba karamin kyau kuke karawa bane?"

Dariya Nafeesa tai, "Lallai Yah Kabeer,yo kaga mukai kyau ma in mun bata ran bare mun sakesa, ina tabbatar maka cewa Habibbtyna ta mussamance, yanzu ma da zatayi murmushi sai ka kusan suma."

Saura kiris Dariya ta subucema Maryam Amman ta basar domin ban da kara jin tssnar Kabeer ba abun da take.

********Nafseen ne yafito daga cikin daki cike Da murmushi afuskarsa, wata yar matashiyar Mata ta biyo bayansa tana, "Umm Husband ban fesama turaren ba fa."

Kwaikwayon yadda ta shagwabe yayi shima, "Umm Wife kina gani lokaci na kuremun kuma inna biye ki wallahi sai in makara yau fa zamu fara daukan sabon film dinnan So akwai bukatar na isa Kano kan lokaci, kuma na fesa turaren nan fa wai bai isa bane nikam."

Murguda masa baki tayi, "ni dai ka daina kwaikwayona,kuma ai naka ka fesa ni baka fesa nawa ba,Allah ba zan Yarda ba." Ta karasa maganar cikin sigar shagwaba.

Dawowa yayi kusa da ita, yana magana ahankali, "Fesamun Amman indai yayi yawa kika janyo yau na miki kanwa shikenan ba ruwana."

Dariya tayi kan ta ce , "Kanwa! Allah kawota ai a kujera zata zauna ba kaina ba,kowa ya Iya allonsa ya wanke,in yasoma ya sha ruwan."

Hade rai yayi, "Wato ma ko irin kishinnan nawa bakya yi ko?"

Fara fesa masa turaren tayi tana sakin murmushi, "Ina kishin Mijina fiye da kowa, kishi Mara misaltuwa Amman ban isa in sauya kaddarata ko ince zan musa ikon Allah ba,Ina Sonka Mijina,fiye da numfashina, fatan nasara,Allah Sa afita asa'a adawo lafiya, Zan yi kewarka."

Hannunta ya riko suka fito tare, ji yake tamkar kada ya barta domin kuwa yafi kowa Sanin cewa yayi dace da mace ta gari, mai hakuri,hankali da tunani.

Kallonta yayi,yana, "Maddala da matar kirki,Amin Amin Na gode, Allah ya miki albarka,byrrbyee."

Kamar za ta yi kuka ta ce, "baka fadamun ba."

Cikin tsokana ya ce, "Me zan Fada?"

Hawayene ke kokarin fito mata, da sauri yadawo tare da rada mata wata magana akunne,murmushi tayi kawai.

Ya kara da, "I Love You Wify."

"Love you more husband,byeebyee."

Hanyar kano suka kama,da yake tafiyar ranane har dare basu isa ba.

Kwatsam wata babbar mota tayo kansu,ba damar kaucewa haka ta danne motarsu

Innallillahi-wa'inna-ilaihir-raji'un

🤭🤭KUNA SO NAFSEEN YA MUTU???🤸‍♂️🤸‍♂️A TSARE KOMAI YAKE AMMAN YAU ZAN GA MASOYAN YAYANA.

Urs Xayyeesherth_*SAI NA AURI MARUBUCI📝📝📝*_ _(Nafseen)_

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° _Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu._ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ***

NA XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH

✨6STARS INDEED

_*SAI NA AURI MARUBUCI...Kirkiraren labarine, mai dauke da nishadi na mussaman, al'ajabi tare da ban tausayi,tsantsar soyayya da kauna mai ban mamaki*_