SAI NA AURI MARUBUCI (Nafseen)

PAGE-25

by @xayyeesherthulhumaerath

_*TUKWICI GAREKU YAN team DIN YAYANA🥺DUK DA DAI INA KISHI KUNFI SONSA AKAINA,JASMINE, MRS MUBARAK,RANO ON TOP,AMATULLAH,FATIMA ZAHRA,BELAR MAXARE,XEE XEEN BABA,FATIMA SULAIMAN,UMMU NIHEEL, DA MA SAURAN ,I HEART U OLL🥰*_

🤔🤔 _*WATO ANGA NA DAGE DA TYPING SHINE ZA AFARAMUN ISKARAN BARANCI🥺TO DAGA WANNAN FEJIN SAI BAYAN SALLAH TUNDA HAKA KUKESO🚶‍♀️*_

*****

Sallama Kabeer ya yi cikin sayayyar murya.

Amsawa tai tamkar mai ciwon baki.

"Ba zan gaji ba,domin ina Sa ran cewa wataran wannan kiyayyar zata koma so, Ina Miki so tsakanina da Allah Maryam, Ina son nai rayuwa dake rayuwa ta farinciki irin ta masoya,kowa na miki kallo acewa ke Maryam ce kadai Amman anawa bangaren ke tamkar taurarice da ke haskaka sararin samaniyi,aduk lokacin da nai kewarki kallon sama Kadai kan sani nishadi bare kuma ace ke din da kan ki na gani,Dan Allah ki amshi muradin raina ko da sai dayane,tare da sakarmin murmushi komin kankantarsa,duk da kasancewar bama tare Amman hakan ba zai hanani siffata kyakkyawan murmushi da zai bayyana afuskar gimbiyata ba."

Maimakon bayyanar murmushi afuskar Maryam wani irin hamshakin takaicine ya turnike mata azuciya, ji take tamkar zaginta yake, kamar yadda ta tssni Kalmar so haka ta tsani kalaman so.

Ba ta San lokacin da ta sake wani kasurgumin tsaki ba,Wanda sai da ya ratsa cikin wayar tamkar agaban kabeer tai.

Yaji tsakin Amman so da kauna ya hanashi jin haushi ko ganin laifinta illa murmushi da ya sake,domin kuwa yaune rana ta farko da har ta Iya amsa kiransa.

Maryam ta ce, "Ka gama?"

Jiki asanyaye ya ce, "Ba zan taba gamawaba,Amman ganin cewa baki cika son yin maganar ba yasani dakatawa."

Wani tsakin dai ta kara sakewa kan ta ce, "OK Na gode." Batare da ta jira amsar shi ba ta datse wayar.

Masalin karfe goma na safiya aka sauke Nafseen Kofar gidansa.

Rukayya zaune tai tagumi ban da tunanin Mijinta ba abun da take.

Da sallamarsa ya shigo ta karasa gareshi da gudu ,yanayin ta ganshi ne yasa jikinta yin sanyi.

Duk jikinsa plaster koba,a fada mata ba ta San wannan hatsarine yayi.

wani kuka ta fashe dashi tare da rungumarshi tana da kyar ya lallamata tayi shiru .

falo suka shiga ta tayashi ya zauna tana hawaye tace Bari na hada maka ruwan wanka ji take kaman ciwon yadawo kanta.

Taimaka masa tayi ya yi wanka,tare da gasa masa jiki,kwanciya yayi ita kuma ta fito cikin hanzari ta hada masa abinci kawo masa tai ta ce, " bari na baka kar kaji zafi ."

Murmushi kawai yayi aransa yana kara jin tsantsar so da kaunar matar ta shi,tana bashi tana hawaye kaman ciwon a jikin ta yake.

"Yanzu dama abinda yasa meka Kenan kako fada min?"cewar Rukayya

Nafseen ya ce, "kiyi hakuri banso hankalinki yatashine, kuma kinga ma ai abun yazo da sauki mussaman yanzu da nai wankannan naji dadi sosai, Mah Yar Lukata." Ya karasa maganar cikin zolaya.

Hannu ta kai zata dakeshi, sai kuma ta tsaya tare da murgada baki , "Yasin ni ba yar lukutace ba,kuma zan rama yau Dan baka da lafiyane."

Murmushine kawai ya bayyana afuskarsa batare da yace komai ba.

Rukayya ta kara da , "yanzu wayarkan fa?

Nan ya ce, " Ban gani ba fa tun adaren jiyan, Allah kadai ne yasan meyake nufi da hakan, zanyi amfani da dayar wayar kawai,kinga yanzu ba,a welcome back kan lokaci ga sabgogi sunmin yawa wancan sim card ba kowa yasanni dashi ba zan dai rasa wasa daga contacts Dina."

Rukayya ta ce, "Allah Sa hakanne mafi alkairi."

Ya amsa da "Ameen."

GIDAN SU MUTANSIR

Daddy ne yadawo Momy take sanar masa halin da Mutansir ke ciki nan da nan tashin hankali ya bayyana a fuskarsa.

Batare da ya ce komai ba,bangaren Mutansir din yayi tare da nufan dakinsa.

Ban da rawa ba abun da jikinsa ke yi duk ya fita a hayyacinsa.

hankalin Dady ya tashi,matukar gaske.

" Son Wai akan Mace ne nake shirin rasa ka? ka fada min ko yar waye bazan bar komai yasameka ba, na maka alkawarin haka son, Dan Allah kacire damuwar komai ka tuna cewa kai waye kuma waye mahaifinka,inka cutar da kanka ba zan yafe ma ba."

Kokarin Mikewa Mutansir yake kaman ba abinda ke damunsa, Dady ya yi kokarin tallefa, ya rungumer dadyn ya yi yana "Dady da gaske Dan Allah? Wallahi ina son Nafeesa, na San zaka auramin ita."

" In Sha Allah Son, yanzu ka taso mu ci abinci."

Haka Dady ya rike shi suka wuce dining Momy ta zaunaddashi,Sannan suka fara cin abinci,Dady kuwa ya kasa ci tunanin yadda zai bullowa lamarin kawai yake.

***Mammah ta gama shirya kayan break tasan tunda taga Nafeesa bata fito ba,to tabbas bata farko awannan barcin nata ba, dakin ta shiga domin dubata.

Tana nan dai kamar yadda ta barta, addu'a ta shafa mata cikin yanayin damuwa kan ta fice daga dakin.

Haka RANAR Mammah ta zauna agida bataje asibiti tana jiran ko Allah yasa Nafeesa ta farka Amman shiru har Yamma, Maryam ma taje skul gsshi har sun tashi Amman ba Nafeesa, kuma ta kira wayarta akashe hakan yasa ana tashi ta nufi gidan.

Isarta kuwa Mammah ta samu zaune tai tagumi afalo.

Ta sanar da ita halin da ake ciki,cikin damuwa Maryam ta shige dakin,kuka take tana mai yiwa kawar tata addu'ah,Mammah ce ta kara gyara mata kwanciya tare da kokarin cire mata glass din kar ya dameta,abun Mamaki glass din ko motsawa bai yi yaki fita, ba yadda Mammah ta Iya haka ta bar mata.

Maryam ta ce, "Mammah wai me ya farune ma har ya janyo barcinnan nasan dole sai an mata wani Abu."

Mammah ta ce, "Hmm nima dai ji nai tana kuka ina zuwa ta ce mun wani Abu ya sameshi daga nan bata kara magana ba."

Maryam ta ce, "To shi wa?" Sai kuma ta tuna.

Kukan ta kara fashewa da shi.

Sallama akayi agidan Maryam ta fito wa zata gani......??

Urs Xayyeesherth[4/7, 9:51 AM] Xayyeesherthul-Sweery: _*SAI NA AURI MARUBUCI📝📝📝*_ _(Nafseen)_

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° _Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu._ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ***

NA XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH

✨6STARS INDEED

_*SAI NA AURI MARUBUCI...Kirkiraren labarine, mai dauke da nishadi na mussaman, al'ajabi tare da ban tausayi,tsantsar soyayya da kauna mai ban mamaki*_