SAI NA AURI MARUBUCI (Nafseen)

PAGE-32

by @xayyeesherthulhumaerath

_*HAUSAWA SUKA CE DA BABU GWARA BA DADI,My Grp Mmbrs🤗Sai Na Auri Marubuci 1,2 Son so saboda Allah,Ayi Hakuri da guntun fejinnan hanunna ciwo yake😟kuma anki siyamun chocolate bare ya daina😩Ku siyamun pls😉*_

"""""""""

Fadi kasa, Hasken da kyalkyalin da bayyana ne ya tsaidata cike da Mamaki take kallon falon wanda kyalkyali tare da ado ya mamaye,ta ko ina ta kalla Abu daya take gani, hotunanta an sanyasu a firem tare da rubutu, HAPPY BIRTHDAY NAFEESA (Ammien Abhi).

Murmushin da ke fuskarta ya kasa boyuwa,fararen hakorannan duk sun bayyana waje,ta ma rasa abun yi,domin an bala'in surprising din ta,atakaice ma ta manta da cewa yaune zagayowar ranar haihuwarta kwata-kwata sai yanzu,gani take kamar amafarki, Abhi ne ya katse mata tunani tare da fadin, "Barka da zagayowar ranar haihuwar Ammiena,Allah ya yi miki albarka,ya albarkaci rayuwarki,Allah Sa sauran shekarun da suke rage miki aduniya su kasance mafi alkairi gareki da mu tare da duniya ma baki daya,Allah ya shiryamun ke,ya kara miki ilimi da basira fatan alkairi,ina alfahari dake Ammiena."

Har Yanzu Nafeesa ta kasa magana illa baki da ta bude kawai da farko an shammaceta na birthday ga kuma na dawowar Abhi din ta.

Maryam,Mammah,Sabir ne suka fito atare,cike da fara'a Maryam ta rike Nafeesa tare da fadin, "Oya Madam Mamakin ya isa haka,muje muyi wanka sannan muyi sallah lokacin shagalin zai fara."

Nafeesa ta kalli Abhi, "Thank You Abhina,Word can't express How Happy am I,You are d best father in d world,can't love you less,really proud of you."

Abhi Ya yi Murmushi, " Ashe 'Yar tawa ta zama baturiya,bama wannan ba yanzu maza bi Maryam kiyi abin da ta ce."

Dariya tayi ssnnan ta rufe fuska. Rike mata hannu Maryam tai har sun fara tafiya Nafeesa ta tsaya,"Wait Habibbty ni fa ina kara jin kamshin turarena kuma kamar adayan falon cen muje ingani kan mu tafi."

Maryam ta ce, "Madam bama da lokaci koma miye bari kiyi wanka zaki gani shikenan ai."

Bata bare Nafeesa ta kara magana ba ta ja ta fuu suka shige daki.

Nafeesa kuwa gabadaya hankalinta ya yi falon tsintar Kanta tai cikin zakuwar son ganin meke faruwa da turarenta.

Wankan suka fara dukkansu kan sukayi sallah suna idarwa Nafeesa ta ce, "Habibbty yau narasa irin farincikin da nake ciki tun safiya har izuwa yanzu,Ashe yau ne birthdayna wallahi na manta shaf kun bala'in surprised dina,ba na da kalaman godiya gareku illa fatan alkairi,Allah bani ikon faranta maku kamar yadda nima kuke faranta mun akullum."

Maryam ta galla mata harara, "Yen Yen ,yen naji ni ungu ga kayannan kisa yanzu ba time."

Bude baki Nafeesa tai ganin doguwar rigar da take mutuwar so,ta sha fadin Mammah ta siya mata ta kan ce ba ta da kudin wannan Riga.

"Habibbty! wa ya siyamun?"

Maryam ta ce, "Ni na fadama Dady ya sayo mana tawa ma na gida ke kam yau zaki Sa taki maza tashi kisa."

Rungume kawarta tai tana, "Allah bar mun ke Habibbty na gode."

Farar doguwar rigace mai adon golden tasha kyalli da bit ga stons ta ko ina, ko da ido kaga riganrnnan kasan ba ta karamun kudi bace.

Ba karamin kyau Nafeesa tai cikin wannan rigarba,tamkar dan ita akayita,light makeup tayi kamar yadda tasaba,sannan Maryam tayo mata rolling din gyalen, Nafeesa ta fito tamkar sarauniyar kyau Wanda tabbas yau in gasa za afita sai ta cinye.

Golden din takalminta mai tsayi tasa Wanda ya kara dago da kyawunta Dama na rigar,Maryam kuwa bakar abaya tasa simple duk da hakan itama tayi kyau dai,dai nata.

Gaban mirrow Nafeesa ta tsaya tana gyara glass din ta tare da kallon yadda rigar ta tsaya mata ajiki,farinciki takeji har cikin ranta,turarenta ta dauka zata fesa sai kuma ta tuna da kamshin da taji afalo,batare da tayi ma Maryam magana ba,da gudu ta fita sai falo......

Mai zata gani???

🤪🤪NEXT PAGE🚶‍♀️

Urs Xayyeesherth [4/14, 9:34 AM] Xayyeesherthul-humaerath💞: _*SAI NA AURI MARUBUCI📝📝📝*_ _(Nafseen)_

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° _Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu._ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ***

NA XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH

✨6STARS INDEED

_*SAI NA AURI MARUBUCI...Kirkiraren labarine, mai dauke da nishadi na mussaman, al'ajabi tare da ban tausayi,tsantsar soyayya da kauna mai ban mamaki*_