SAI NA AURI MARUBUCI (Nafseen)

PAGE-33/34

by @xayyeesherthulhumaerath

*FEJI NA BIYUN KARSHE*

_*SADAUKARWA GA DUK MASOYANA HARMA DA MAKIYANA ADUK INDA KUKE🥰*_

""""

Ba kowa cikin falon illa tashin kamshin turarenta dake kara shige mata hanci,aranta taji tabbas akwai wani Abu na mussaman,ji tayi kamshin na kara tunkarota,tsantar kanta da cigaba da tayi tayi batare da tasan inda ta dosa ba,ji tayi an rike mata hannu.

Juyowan da zatayi taga Maryam ce cikin fara'a ta sake mata wani kyataccen murmushi tana, "Habibbty Muje Abhi Mammah,har Ma da Ummi,Dadyna duk suna jiranmu afalo."

Nafeesa ta ce, "Tam Muje."

Suna zuwa falon kuwa aka kara dauke huta dib.

Nafeesa ta ce, "Habibbty kin San bana son irin wasan,bana son duhu Dan Allah Ku fito, rufe ido tayi tare da fara kuka."

Jin kamshin Turarene yasata saurin bude idanunta, Nafseen ne tsaye agabanta tamkar amafarki.

Wani irin yanayi Na Farinciki Nafeesa ta shiga Mara misaltuwa wanda ko baki yayi kadan wajen bayyanawa bare hannu da zai yi rubutu,Hawayene Farincikine kawai ya fara bayyana afuskarta.

Nafseen kuwa ban da wani kayataccen Murmushi ba abun da ke bayyana afuskarsa.

Hawaye take Amman kasa rufe bakin,kara gwalalo ido take domin kara tabbatar da cewa ba mafarkin take ba.

Nan take Mammah,Abhi da su Maryam,Ummi harma da Kabeer duk suka fito.

Da gudu Nafeesa ta karasa gun Abhi tare da rungumesa tana kuka, "Abhi Dan Allah shine? Kada kucemun mafarki nake, in kuma mafarkine kada Ku farkar dani Dan Allah.

Gabadaya Nafeesa ta fita ahayyacinta tamkar wadda ta zauce.

Kara rungumarta Abhi Yayi , "Ammiena,bude idonki,ki daina kuka,tabbas ba mafarki kike ba,Shine dai kike gani,zo Muje."

Riko Hannunta Abhi Yayi ya kaita har gaban Nafseen ya ce, "Ammiena nace ki bude ido kinji."

A hankali Nafeesa ta fara bude ido,kamar yadda Abhi ya Fada kuwa ba mafarki bane tabbas Zahirine,domin kara tabbatarwa bata San lokacin da ta rike masa hannu ba,gani tayi bai bace ba kamar yadda yasaba mata,wani irin Murmushi tayi tare da fadin, "Alhamdu Lillah."

Sai lokacin ta lura da mutanen falon cikin sauri ta sake masa hannu tare da rufe fuska Dan kunya.

Da Sauri Maryam ta karaso Gareta,tare da cire mata hannun,Jan ta tayi gaban Cake din da akayi mata mai hawa uku,shima tsarin fari da golden ne kamar kayan jikinta,ba karamin kyau yayi ba.

Kabeer ya ce, "Oya mudai ayanka mana cake."

Murmushi Nafeesa tayi kawai tana bin yan falon duka da kallo,mussaman Jameel da ta kasa dauke idonta kansa, aduk lokacin da suka hada ido ya kan sake mata kayataccen Murmushi.

Rike mata Hannu Maryam tayi dukansu suka ,Zagaye ta suna waka "HAPPY BIRTHDAY TO YOU,,HAPPY BIRTHDAY,HAPPY BIRTHDAY DEAR NAFEESA...... suka karasa da tafe nan aka yanka cake.

Mammah ta ce, " To zan ga wa za afara ba cake dinnan Abhine ko wa,daman ni ansabamun wariya."

Dariya dukansu sukayi Abhi ya ce, "Ban so ana takurawa Ammiena fa tam,Oyaaa Ammiena fara ba Wanda kika yi niyya cake dinnan,kin San ni bana kishi."

Nafeesa ta dauki Cake tare da yin gaban Mammah,da sauri Mammah ta bude baki tana jiran saukan cake,dariya Nafeesa tasa kan ta wuce,tsayawa tayi gaban Nafseen ta kasa hada ido dashi ga cake ahannu, da kanshi ya doga hannun tare da sawa abakinsa,gabadaya tafi ne ke tashi adakin, Kabeer kuwa Video yake masu,sunyi kyau matuka tamkar ango da Amarya,mussaman yanayin shigarsu da Nafseen yasa farar shadda mai adon golden kamar Nafeesa.

Kunya tasa,takasa daga fuskarta bare su hada ido.

Maryam ce ta karaso tare da mika mata gift da akayi rafin ta na "Happy Birthday Habibbty, Allah ya dauwamar da farinciki mai inganci arayuwarki,Allah baki lafiya tare da ikon aikata abun alkairi duniya da lahira,."

Murmushi Nafeesa ta sake ma Aminiyartata tarasa abin cewa.

Sabir ma ya karaso da gudu, "Happy birthday Anty mai glass,ina sonki kinji,kada ki kara tafiya barci ki barmu kinji,ni da Mammah da Anty Maryam za mu yi kuka, Promise ba za ki kara ba."

Murmushi tayi tare da rike hannun kanin nata, "Ba zan kara ba Sabir in sha Allah,nima ina sonka kaji."

Mammah ma ta karaso , "Appy Bornday Ammien Abhinta mai kunyar Karya mudai an hanamu cake," shiru tayi na Dan lokaci kan ta kara magana , "Allah ya albarkaci rayuwarki Ammiena,Allah ya yaye miki lalurar da ke damunki,Allah kawo karshen wahalarki." Mammah ta fashe da kuka.

Da Saurin Ummin Maryam ta karaso tana, "Yanzu lokacin Farincikinmu ne bana bakin ciki ba,So Kada ki bata mana shgali,."

Murmushi Mammah tai tare da share hawayen da ke fuskarta.

Nan Ummi,Daddy,Kabeer duk sukama Nafeesa fstan alkairi,sai Nafseen Wanda ya kasance karshe.

Karasowa yayi gabanta, Nan Su Mammah duka suka watse illa Maryam da Kabeer da suka tsaya gefe.

"Barka da zagayowar Haihuwar kanwata,kuma jaruma, ina miki fatan alkairi,Allah ya dauwamar da farinciki arayuwarki duniya da lahiya, Allah kara miki ilimi da basira,fatam nasara ga dukkan aikin alkairin da kikasa agaba na rayuwarki."

Ban da hawayen farinciki ba abun da ke zuba a idanun Nafeesa,Yau kunnenta ne ke sauraren zantuka daga bakin Wanda ta fifita sonsa afadin duniya,yau idontane ke yin tozali da Wanda ta saba gani cikin barcinta, yau itace tsaye gabansa inta daga ido tana kallonsa yana kallonta.

Wata Yar Jaka ya mika mata wadda banace ga abun da ke ciki ba,Amman ga dukkan alamu ba Abu dayane ba,ita kanta Jakar ma abun kalloce bare kayan da ke ciki.

Rusunawa tai ta amsa tare da fadin, "Na gode." cikin sanyayyar Muryarta, .

Tsayawa sukayi gaban juna duka batare da sun kara fadin komai ba, Kabeer ya yi gyaran Muryam, "Eheem Madam ni fa Yunwa nakeji ko zan Iya samun abinci?"

Maryam ta sake Murmushi , "An gama yallabai, yanzo za aci abinci in sha Allah."

Kabeer ya ce, "Kanwata ba fa guduwa zai ba,ya kamata anemi wajen zama aci abinci."

Cikin Kunya Nafeesa ta rufe fuska da gudu ta nufi dakinta, kan gado ta Fada tana tsalle da ihu, tare da rawa, ta rasa ma abun yi, lekyansu takoma yi ta window ta na sakin Murmushi, ji take tamkar ta dauwama ta na kallonsa, zanen ta ta kalla,ta kara kallonsa,tabbas basa da banbanci ko kadan wani irin farinciki takeji har cikin ranta,alwala tayi tayo sallah raka'a biyu domin godiya ga Allah.

Duk Wanda ya ga fuskar Nafeesa ya tabbata yau ranarce ta mussaman domin Farincikinta ya kasa boyuwa.

Sabir ne ya shigo, "Anty kizo kici abinci inji Abhi."

Batare da ta amsa ba rike masa hannu tayi suka fita tare.

Kowa ya zauna an fara cin abinci,Direct wajen Abhi ta nufa tare da zama gefensa.

Kallonta yayi cikin fara'a "Har Yanzu dai halin Na nan Ammiena? Ba za ki ci ba? Kin girma fa Yanzu,ko so kike Jameel ya miki dariyar rama baki cin abinci?"

Dagowa tayi suka hada ido ya sake mata Murmushi da sauri ta kawar da kai tare da girgizama Abhi kai.

Ranar dai kan Nafeesa taci abincin da kowa yayi mamaki, wadda bata huce chokali shidda karkari tace ta koshi Amman yau kam sai afawa take,Abhi da Mammah sai kallon diyar tasu suke suna masu jin dadi har cikin ransu, Ashe zasuga wannan rana da Nafeesa zatayi rayuwa cikin walwala? Tabbas Nafseen shine jigon rayuwar Nafeesa.

Ita kanta Mamakin yadda take cin abincin take,domin bstasan inda abincin ke shiga ba kawai zurawa take.

Anci an sha,anyi wasa da dariya Wanda Nafeesa komai akayi sai dai tayi dariyan batare da tace komai ba.

Ummi da Abban Maryamne suka fara tafiya kan Kabeer da Nafseen da sukayi azamar tafiyan suma,Maryam ta riko hannun Nafeesa, "Habibbty muje mu rakasu."

Nan take Ran Nafeesa ya baci,ji take tamkar ta bisa su tafi Amman ba yadda ta Iya.

Har zasu shiga Mota Ya juya tare da fadin, "Sai da safe mai tsoron duhu tun da baza amana sallama ba."

Murmushi kawai tayi ta na kallonsa gani tai da gaske dai motar zai shiga kuma zasu tafi cikin sauri ta ce, "Uncle......

*💃💃💃💃💃💃Last Page Zai kasance goron sallahne gareku masoya😁😁saura feji daya, Wanda zan sake ranar Sallah in sha Allah, akwai abubuwa na mussaman da zasu kasance awannan fejin domin duk sirrukan da ke cikin littafin daga farko har karshe yanaga wannan fejin, zai kasance tamkar taron kammala littafina Wanda zai gudana a media in sha Allah, tarone na mussaman Wanda ba ataba irinsa ba,Dan haka nake Neman alfarmar duk wata masoyiyar littafinnan ko kuma sauran littafaina tamun magana inyi saving numberta tare da mun magana kan littafin kan wannan ranar👏👏Dan Allah ku min magana aduk inda kuke,kamar yadda kuke nunamun soyayya gareni da littafaina mussaman wannan da ya kasance na mussaman nima zan nuna maku,kada amanta amin magana koda baki taba sharhi ba,in kuma kinayi in kinmin magana ki fadamun,cikakken suna da kuma bayani kan bibiyar littafinnan,ina Fatan dukkan masoyana zasu fahimci ni kuma suyi maraba da da wannan tsarin,kada amanta amin magana,mussaman wa inda basa GRP dina😁*

🥰🥰Xayyeesherthul-humaerath Marubuciyar: MATAR POLICE KUCHAKAR KISHIYA AZZAWAJUL-MUKADDAR WASA DA SO KWADAYI BABU RUWAN SO JAMEEL SAI NA AURI MARUBUCI😁🥰

Ina alfahari da masoyana aduk inda suke💃💃

FATAN ALKAIRI OLL,ALLAH SA AYI AZUMI LAFIYA,A GAMA LAFIYA👏

***

Urs Xayyeesherth_*SAI NA AURI MARUBUCI📝📝📝*_ _(Nafseen)_

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° _Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu._ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ***

NA XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH

✨6STARS INDEED

_*SAI NA AURI MARUBUCI...Kirkiraren labarine, mai dauke da nishadi na mussaman, al'ajabi tare da ban tausayi,tsantsar soyayya da kauna mai ban mamaki*_