SAI NA AURI MARUBUCI (Nafseen)
PAGE-35
Juyowa yayi tare da sake mata wani hamshakin murmushi,"Naam Kanwata lafiya dai ko?"
Batasan lokacin da ta shagwabe tare da fadin, "Zan bika,kar ka tafi Dan Allah, Za....... Ta fashe da kuka.
Fitowa yayi tare da rike mata hannu yana, " Kukan fa? Ki daina bana so,ko kina so nima nayine?"
Ta girgiza kai.
Ya ce, "Yawwa tam ki daina kukan bana so kinayi kinji? Smile."
Share hawayen tai tare da sakin murmushi kamar yadda ya bukata.
"Yawwa kinga ma kinfi kyau haka,yanzu dare yayi ki koma gida gobe zan dawo kinji." Cewar Nafseen.
Cikin shagwaba ta ce, "Promise?"
"Yes Promise." Nafseen ya Fada yana kokarin tafiya.
Ta ce, "Byee,byeee."
Har ya fara tafiya Juyowa yayi ya kalli yadda ta kyankyame masa hannu ya saki murmushi kan ya ce, "Nafeesa!
Ahankali ta dago ta kallesa.
Ya kara da, " Hannun fa baza asakemun in tafin bane? Ko dai in fasa tafiyanne?"
Da Sauri ta ce, "Eh Please Uncle."
Tana fadin Uncle,Nafeesan WhatsApp ta fado masa.
Cikin sauri ya ce, "Antyna jaruma?"
Wata kunyace ta kamata batare da ta sani ba tasake hannun tare da shiga cikin gida,Da gudu.
Binta da kallo yayi kawai yana sakin Murmushi.
Kabeer da Maryam ban da dariya ba abin da suke.
Jameel Ya kalle su, "To Mallam tsuntsu in an gama azo mu tafi ko? Kasan abun da ke gaban mu."
Tare suka karaso garesa,Kabeer yayi sallama wa Maryam, ya yin da take ta faman godiya.
Murmushi Kawai Jameel yai batare da ya ce komai.
Suka Shiga Mota, Maryam ma ta shiga gida.
Nafeesa na shiga gida ba inda ta nufa sai dakinta,jinta take ayau tamkar wata sarauniya,farinciki take har cikin ranta Mara misaltuwa, duk yadda zan kamanta yanayin da Nafeesa ta shiga bazan Iya misalta maku shi duka ba saidai in fadi iyaka abun da zan Iya fadi,Amman Nafeesa kam yau ta shiga Farincikin da zan Iya cewa bata taba shiga irinsa ba arayuwata.
Fadawa kan gadonta tai tana wani irin numfarfashin dadi.
.
Maryam na shigowa ta kalleta dariya tayi ta kalli Jakar Da Nafseen ya kawowa Nafeesa dauka tayi ta na kokarin budewa,karaf taji an fisge,Daga Idon da zatayi Nafeesa ce ta galla mata harara tana murguda baki, "Habibbty Dan mareki Fa,Uncle ne ya kawomin Abu kika wani dauka."
Maryam ta kara kyalkyalewa da dariya, "Anya Nataba ganinki cikin yanayi irin na yau?"
"Uhum kyaji da shi dai nikam bara inga abuna." Cewar Nafeesa dake tafiya.
Kan gadonta taje ta zauna tare da bude jakar.
Wani Agogo ta fara gani,Cikin Wani Abu Shiba akwati ba kuma ba kwantene ba,flsatic ruwan garau shi kan shi abun kallone bare agogon dayake golden mai kyalkyali da kaga agogon kasan yaci kudi zabar kyalkyali da shekin da ke jikinsa,agefe kuma An rubuta NAFEESA tana gwadawa ahannunta tamkar Dan ita akayi agogon cif-cif ita,ba karamin kyau ya yi mata ba, hannun ya kara kyau matukar gaske,kara zura hannunta tayi acikin jakar shima dai wani Dan akwati ta dauko Amman shi yanada duhu bazaka ga abun da ke ciki ba Amman yafi na agogon girma, Maryam ta fisge , "Dilla bani induba kin tsaya wani kalle kalle."
Sake mata tayi tare da sakin murmushi,Farinciki yasa ko magana Nafeesa bata Iya yi.
Maryam na budewa ta ce, "Wooooooo." Ita kanta sake baki tayi domin abun ya matukar kyayarta da ita,"
Wata Irin Sarkace mai chain da Dan kunnenta,gefe kuma Rank Dan karami,ga glass din wani turare Dan karami, Anrubuta BlackBerry ajiki. Ga wata karamar takarda an yi rubutun wishes na birthday.
Maryam ta ce, "Gaskiyane Habibbty gabadaya gifts dinnan sun tafi dani wallahi,"
Takardar ta dauka ta dunga karantawa tana kara maimaitawa,kallon kayan tai kadai kan kara sata cikin nishadi,atakaice Rugume da kayannan Nafeesa tayi barci awannan Ranar,Maryam ban da dariya ba abun da take yi mata.
Wa she gari..........
Mammah da Abhi zaune afalo Nafeesa da Maryam suka fito da shirin tafiya Skul.
Abhi ya kalleta, "Ammie Zaku Skul kin manta munada bakone?"
Ta shagwabe fuska, "Abhi Karfe 11 zamu fito lectures kuma Habibty ce ta matsamun muje ni bana son zuwa."
Mammah ta ce, "To zaman me daman zakiyi? Ai gwanda kije Dan nasan su Kabeer kan su da gidannan sai wajen 2pm."
Ta kara shagwabewa zatayi kuka, "Mammah har 2pm taf ni kam Aa nidai."
Mammah ta bata rai, "Kaniyarki Mara kunya kawai,shige Ku tafi."
Jikin Abhi ta Fada zata fara kuka, "Abhina kaga Mammah ko?"
"Sorry Ammien Abhi Maza tashi Ku tafi na miki alkawari Uncle ne zai zo ya dauko Ku,ina kince 11am ai ba jimawa zakuyi ba." Cewar Abhi.
Tana jin hakan Da sauri Nafeesa ta mike , "Byee,Byer Mammah,Byyeebyerr Abhi,Miss u,ina sonku kunji byee natafi,Mammahna kidaina fushi dani am Sorry, Byee." Tayima Mammah kiss afuska kanta fita tana dariya,daga Mammah har Abhi Dariyar suma suke.
Tana fita Mammah ta kalli Abhi ido ya cika fal da kwalla, "Abhi Nasan Nafeesa inbata samu yaronnan ta aura ba tabbas xamu Iya rasa ta wallahi,ina tsoro,ina tausayin halin da zata Shiga koda bata rasa ranta ba to zamu shiga cikin wata matsala,Dan Allah ka nemamun alfarma awajensa ni kam na amince, wallahi tayi aurennan indai zatayi farinciki, nasan yanada mata Amman ya dubi kuruciyar Nafeesa rayuwarta na cikin hatsari ban San wani irin so bane wannan tun abun na bani mamaki har na daina, Abhi Dan Allah ka taimakamun." Ta karasa maganar tare da fashewa da kuka .
Abhi ya rike hannun Mammah, "Kiyi Hakuri bamu isa karewa kaddararmu ba ace ma iyaka Farincikin da yasa 'Yar mu jiya koda bai karbi kokon baranmu mun gode, ke kin sani,ni nasani, tun da Nafeesa tazo duniya bata taba Shiga yanayi na farinciki irin jiya ba,kuma hakan ba karamun faranta mana yayi ba,Dan haka kisa aranki ko Nafeesa ta rayu ko ta mutu,ko ta samu wani Matsala duk daga Allahne,kinji ko? Smile."
Share mata hawayen tai,, ta sake masa murmushi yadda ya umarta, "Allah zaba mana mafi alkairi." Cewar Mammah.
Abhi ya ce, "Yawwa Matar Aljanna,Amiin."
"""""''''''''''
Mutansir kuwa kan su karasa asibiti Allah yyi mi shi rasuwa, Dady da Mumy sunyi kuka iyaka kuka, daga nan suka chanja tsarin rayuwarsu tare da mai talaka mutum Wanda yake da Rana,sunyi matukar nadama,mussaman Dady....
Nafeesa na Skul ana masu lectures Amman gabadaya hankalinta baya jikinta,ban da Nafseen ba abun da take kallo a idanunta,murmushi kuwa yaki barin fuskarta da kaga Nafeesa zaka fahimci cewa tana cikin yanayi na Mussaman.
11am cif suka fito daga lectures zama sukai agefen wasu flowers suna yar hira,har da Rabi yayi, Maryam ta ce, " Habibbty kizo mutafi gida kawai,inaga fa bazasu zo ba."
Nafeesa ta Dalla mata , "Harara , Dilla zasu zo ni nasan zasu z.... Bata karasa maganar ba ta tsaya can kuma ta ce, " Sunzo." Ta fara tafiya batare da ta ce ko mai ba,Maryam ta bi bayanta Dan ganin ikon Allah, tafiya take Amman turaren da take sheka shike mata jagora,kamshin turarensa kawai taji tafara wannan tafiyar ahaka kuwa sai ga Nafeesa da Maryam gabansu Kabeer da Nafseen.
Maryam ta wage baki, "ikon Allah ya akayi tasan kunzo ta kawomu nan oho."
Kabeer ya kyalkyale da dariya, "Salon son kenan,keda kika ki so na ai baxaki fahimtaba."
Kunya Maryam taji ta kulle fuska,domin har ga Allah yanzu kam son Kabeer ya gama Shiga zuciyarta.
Nafseen ne ya katsesu da fadin, " kunbarmun kanwa tsaye kunata shirme,kinga zo ki shiga mota."yakarasa maganar yana bude mata kofa shiga, Kabeer da Maryam ko suka Shiga baya.
Tafiya suke Amman shiru ba mai magana amotar , kallonta yyi ya saki murmushi kan ya ce, "AntyJaruma sai surutu a chat Amman nan kinmun tsit ko?"
Kunyace ta kara kamata ta rufe fuska tare da fadin, "Ina Kwana." Cikin sanyayyar murya.
Amsawa yayi kawai tare da cigaba da murmushi.
"""" Suna Isa Gida Falon Abhi suka sauka,Mammah ta Sa su Nafeeesa suka kawo masu abinci sannan suka fita.
Bayan sun gama ci Abhi da Mammah sukaxo,sunyi magana sosai domin adiba lokaci ana zantawa Amman banace me suka tsayarba kan maganar,nasan dai tabbas kan Nafeesane Amman ban san matsyar zancen ba.
Kabeer ne ya fara fitowa tare da kiran Maryam ta fito waje.
Yace, "Maryam kina sona?."
Kunyace ta kamata ta rufe fuska tare da girgiza kai alamar eh.
Godiya Kabeer yayi mata sosai da kaban soyayyarsa Da tayi.
Daga nan suka bige da hirar masoya.
Kamar wasa Nafeesa na kwance taji wayarta na ranging da kamar bazata daga ba,wata zuciyar ta rada mata ta dauka.
Tana karawa akunne taji anyi sallama.
Daga jin Muryar tayi saurin gyara zama tare da amsawa.
Ya ce, "ko zan Iya ganin Antyna kan in tafi."
Batasam me zatace ba illa tsintar kamta da fadin, "Tom."
Hijabinta ta dauko ta zura ta fita waje.
Tsaye yake jikin motarshi,su ko Kabeer suna gefe.
Ahankali take tafiyar harta karasa.
"Kodai sai Nazo na karaso da ke ne?" Cewar Nafseen.
Murmushi ta yi ta ce, "Aa."
Ya ce, "to ni indai bazaki na mun magana nikam zanyi fushi."
Cikin shagwaba ta ce, "Uhumm Sholly zannayi fa."
Ya ce, "Yawwa,ko kefa, yanzu ki tsaya muyi magana kinji."
"tam." Cewar Nafeesa.
Nafseen ya gyara tssyuwar tare da fadin, "Kiyi hakuri da duk abun da zan Fada,ba Wanda ya isa ya kerewa kaddararsa saidai muyi fatan zuwanta da sauki,ina fatan duk abun da zai fito daga ba kina zakiyi hakurin jinsa."
Gaban Nafeesane ya fara faduwa tana kokarin dibibicewa.
" *ZA KI AURENI?* ," abun da ya fito daga bakin Nafseen kenan
Afirgice batasan lokacin da ta dago tana kallonsa ba, murmushin da ya sake mata yasata dawowa hayyacinta da sauri ta rufe fuska tare da zurawa aguje, har taje zata Shiga cikin gida ta juyo tare da fadin "Eh." Kan ta kara zurawa aguje.
Murmushin dai ya kara sakewa, Maryam da Kabeer kuwa sai hamdala suke mussaman Maryam da farinciki ya mamaye mata zuciya.
Nafeesa na shiga daki ta tsayi tare da fadin, " *ALHAMDULILLAH ALLAH NA GODEMA, SAI NA AURI MARUBUCI ZAI TABBATA ZAN AURESHI TABBAS IN SHA ALLAH* tsalle tayi kawai ta haye kan gadon tana murna.
*TAMBAYARNNAN NA YAWAN XUWAMUN DAGA MASOYA WANNAN LITTAFIN, SHIN NAFEESA NA DA ALJANUNE?HARMA DA SURUKAN DA KE CIKIN LABARIN*
GA AMSARNAN
_Nafeesa Nada Aljanu ajiki Amman basu shafi Nafseen ba,Abu daya nasani suna taimakonta ne aduk lokacin da wata Matsala ke kokarin kunno mata kai ne,misali wajen da Amina budurwar mutansir da mata ture da hatsarin da Nafseen yayi, aduk lokacin da tayi wannan barcin to kariyane gareta,domin kuwa Nafeesa tamkar da son Nafseen tazo duniya ta kan Iya jin duk wani Abu da zai sameshi ajikinta,haka kuma aduk sanda Nafseen ke waje kamshin turarensa kadai ya wadatar Nafeesa ta fahimci ya zo wajen ko yana wajen wa innan suna daga cikin surukannan labarinnan,Soyayyar Nafeesa da Nafseen soyayyace ta ban mamaki,batare da tasan shi ba Aljanun jikinta sunyi kokarin taimakonta wajen zanen hotonsa sak. Batare da kuskure ba,sun tayata son shi batare da illatata ko illatashi ba, Soyayyar ce tsaftacciya batare da sirki ba_
ALHAMDU LILLAH
Allah na rokeka👏na kara rokekonka,na godema na kuma godema,Allah kasa littafinnan ya nishadantar ya ilamantar tare yadda ya dace,👏👏😭😭Nayi kuka kan littafinnan kuma nayi dariya kansa Allah shi kadai ya boyewa kansa sanin dalili😰innayi kuskure acikin wannan littafin Allah ka yafemun👏👏,Allah na godema🥰🥰
Ku kara tunawa da shagalinmu
Dear Fans and fellow writers.
Please join xayyeeshathul-humaerath for a night of fun, and party as her successful completion of her book SAI NA AURI MARUBUCI (NAFSEEN)
Which schedule will take place insha Allah as follows.
Date:1 Shawwal 1442 Time:7:30pm Group:SAI NA AURI MARUBUCI FANS GROUP
Sannam Ku Adana zafafan sharhinku zuwa dare💃 domin cire taurarin sharhi.
Phone no:***
Urs Xayyeesherth_*SAI NA AURI MARUBUCI📝📝📝*_ _(Nafseen)_
*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° _Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu._ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ***
NA XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH
✨6STARS INDEED
_*SAI NA AURI MARUBUCI...Kirkiraren labarine, mai dauke da nishadi na mussaman, al'ajabi tare da ban tausayi,tsantsar soyayya da kauna mai ban mamaki*_
*FEJIN KARSHE NAKINE ANTY FARIDA (Sweery) Can't luv yhu less🥰*
BARKANMU DA SALLAH🎉🎉🎉
13/May/2021 🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚