MATAR GIDA

MATAR GIDA PAGE 21

by @maimunabala209

MATAR GIDA 021


SHUUKRAN/022




P21






Bayan ya kwashe yara daga makaranta ya wuce da su gidan Muhsin inda ya ba matar Muhsin hakuri ya ce ta kulan masa da yara kafin safe zai zo ya kwashe su matar Muhsin me suna Hafsah ta ce ba damuwa ya bar yaran amma ya kawo suturar su ba tare da ɓata lokaci ba Ɗalha ya koma ya kwashi suturar yaran ya kaiwa matar Muhsin,office ya koma ya sami Muhsin bai tashi daga aiki ba haka ya dauki Muhsin daga office karshe waya Muhsin ya bugawa matarsa ya sanar da ita zai tafi Kano amma zasu dawo a yau,cikin hikima Amirah ta fidda wayarta rabon da ta kunna tun ranar talata da ta gabata,layin Ammi ta shiga ta rubutawa Ammi saƙo bayan ta yiwa Ammi gaisuwa ta sanar da Ammi zasu wuce Kaduna yanzu, insha Allah ko zuwa karshen sati zata kawowa Ammi ziyara,Ammi dake zaune cikin parlour tare da Abba ta ji saƙo ya shiga wayarta ba tsaya ɓata lokaci ba ta dauki wayar ganin sunan Amirah yasa Ammi gyara zama da sauri ta shiga wajen sakon taga abinda Amirah ta tura mata cike da mamaki ta yi wa Abba bayanin saƙon ta ce ''ikon Allah Alhaji kaga yaron nan ya bi dare ya je ya dauki matarsa na ce masa ya bari zuwa gobe amma kaga ya ƙasa hakuri'' Abba ya yi wani murmushi kafin ya ce ''kirasa ki ce masa su zo su kwana a nan in ya so zuwa gobe sai su wuce'' Ammi ta ce ''to'' daga haka ta kira layin Ɗalha bugu ɗaya ya amsa kiran bayan sun gaisa ne Ammi ta tambaye sa ina yake shiru Ɗalha ya yi bai bata amsa ba hakan yasa Ammi faɗin ''ku zo nan ku kwana zuwa safe sai ku wuce'' cike da girmamawa Ɗalha ya ce ''to'' bayan ya kashe waya ya kalle Amirah ta madubi yaga ta zubawa titi ido,muryar Muhsin ne yasa Ɗalha mayar da hankali kan tuƙin da yake ya ce ''na faɗa maka is not safe mu bi hanya da daren nan,yanayi tsaron ƙasar nan sai a hankali'' shi dai Ɗalha bai ce komai ba har suka yi parking a kofar gidan mahaifinsa horn ya yi mai gadi ya buɗe masa gate













Nan cikin parlour sun tadda Ammi da tare da Dady(Abba) zaune bayan shigar su Ammi ta sakar wa Amirah murmushi bayan idonsu ya haɗu,itama ma Amirah murmushi ta yi ta tako har inda Ammi ke zaune ta zauna Ammi ta buɗe mata hannu alamar oyoyo,a hankali Amirah ta faɗa jikin Ammi murya can ƙasa Ammi ta ce ''welcome my daughter'' Amirah ta yi lamo jikin Ammi yayin da Ammi na buga mata baya a hankali sun dauki a ƙalla sakan biyar a haka kafin a hankali Amirah ta ɗago ta mayar da dubanta ga Abba taga ita yake kallo fuskarsa dauke da murmushi a hankali ta tashi ta je kusa da Abba ta durkusa har ƙasa ta gaida Abba fuska sake Abba ya amsa mata gaisuwa,bayan ta gama gaida Abba ne ta koma kusa da Ammi ta zauna sai a sannan ta samu damar gaida Ammi bayan sun gama gaisawa ne Abba ya mayar da dubansa ga Ɗalha ya ce ''ku je ku huta dare ya yi da safe zamu yi magana kafin ku wuce Ɗalha da tun shigarsu parlour ya zama ɗan kallo ganin babu wanda ya bi ta kansa daga Ammi har Abba duk hankalinsu na kan Amirah hakan yasa bayan sun gaida Ammi da Abba shi da Muhsin ya samu waje ya zauna kamar baya cikin parlour bayan Amirah ta gama gaisawa da su Abba ne Abba ya kalle Ɗalha ya ce ''me yasa baka bari sai gobe ka zo ba? akwai haɗari a tafiyar dare'' Ɗalha ya yi shiru bai ce komai ba Abba ya ce ''ku je ku huta amma ina son magana da ku gobe da safe kafin ku wuce'' Ɗalha ya ce ''to Abba''















Ɗalha da Muhsin sun yiwa Abba da Ammi sai da safe sun tashi da niyyar barin parlour Amirah na biye da su bayan ta yiwa Ammi da Abba sai da safe,Ammi ta ce ''ina kuma za ki je? tare zamu kwana a ɗakina mun yi kwana biyu bamu yi hira ba'' a hankali Amirah ta waiga ta kalle Ammi fuskarta dauke da murmushi ta ce ''to Ammi'' daga haka ta wuce ɗakin Ammi shi kuwa Ɗalha taɓe baki ya yi bai ce komai ba ya fita daga parlour bai tsaya ko ina ba sai part ɗinsa parlour ne da ɗakuna uku sai kitchen a nan suke sauka da Amirah da yaransa duk sanda suka zo Kano,a nan Kano aka yiwa Amirah jerenta tun lokacin aurensu daga can gefen part ɗin wani sabon gini ne ɗakuna biyu da parlour sai kitchen wanda a nan za a yiwa Unaisa jere,kusan raba ɗare Ammi da Amirah suka yi suna hira wanda da yawa daga cikin hirar tasu shawarwari ne da dabarun zama da kishiya Ammi ta yi ta koyawa Amirah,can wajen Ɗalha kowa bacci ɓarawo ne ya dauke shi ganin abin yake kamar a mafarki bai taɓa kawo Amirah zata dawo da wuri haka ba,sosai ya yi nadamar abubuwan da ya yi mata ya kuma daukarwa kansa alƙawarin bazai sake wulaƙanta Amirah ba kula da gida da yara ba ƙaramin abu bane a ce gaba ɗaya mutum baida lokacin hutu tabbas mata suna ƙokari,sai yanzu ya yarda da maganar da Muhsin ke yawan faɗa masa cewar mata jarumai ne suna da wata baiwa ta musamman da Allah ya yi masu yanzu kam ya yarda,mayar da dubansa ya yi ga Muhsin ya ga yana baccinsa hankali kwance,misalin ƙarfe biyu na dare Amirah ta farka daga bacci idanunta cike da bacci ta shiga bathroom ɗin Ammi ta yi tsarki daga haka ta dauro alwalah bayan fitowarta daga bathroom ne ta dauki hijab da darduma ta shimfiɗa saƙo ya shiga wayarta kamar baza ta duba ba sai kuma ta dauki wayar ta ga Nailah ce ƴar kawo Abubakar,kawo Abubakar ƙanin Abba ne (Dady) a can ƙasan Maroco yake zaune tare da iyalansa matar sa mai suna Nazaaha ƴar ƙasar Maroco da ƴarsa Nailah,sosai Amirah ta saba da Nailah,tun bayan auren Ɗalha da Amirah Allah ya haɗa jinin Amirah da Nailah kamar yaya da ƙanwa haka suke,dogon rubutu ta turawa Amirah wanda ke nuni da tsantsan ɓacin ran abinda Ɗalha ya aikatawa Amirah,cikin saƙon ta rubuta insha Allah ko Ɗalha ya aure Unaisa,ita da Husnah da sauran dangi sai sun koyawa Unaisa hankali tunda saboda ita Ɗalha ya sake Amirah,duk wulaƙanci da cin mutunci da Ɗalha ke yiwa Amirah kenan saboda Unaisa yake duk iskancin da yake za su ko gyara mata zama,a karshen saƙon ta rubuta jiya Dady ya kira mahaifinta ya sanar masa da abinda ya faru yana tambayarsa ko Amirah ta kira Nailah,nan Nailah ta samu labarin abinda ya faru,wata doguwar ajiyar zuciya Amirah ta sauke daga haka ta rubutu da bai wuce layi biyu zuwa uku ba ta turawa Nailah,bayan ta tura mata ta kashe wayar gaba ɗaya,daga haka ta tayar da sallah,tun bayan sallar asuba Amirah ta shiga kitchen tare da ƴar aikin Ammi alale da kunu suka yi na kari,Amirah tasawa Ɗalha da Muhsin nasu ta cewa mai aikin ta kai masu ita zata shiga wanka













Kamar yadda Abba (Dady) ya faɗa karfe tara daidai ya kira Ɗalha da Amirah cikin parlourn sa ya yi masu nasiha sosai ya kuma gargaɗi Ɗalha da kar ya sake maimaita kuskure sakin Amirah in kuma ya sake zai saɓa masa Ɗalha ya yi godiya ya ce da yardar Allah hakan bazai sake faruwa ba,Amirah da Ɗalha na shirin barin parlour ne Ammi ta ce ''kai kaɗai zaka koma Amirah zata zauna a nan bayan kwana biyu da kaina da mayar maka da ita,ba iya Ɗalha ba har Muhsin dake tsaye kofar parlour ya yi mamakin furucin Ammi,wani irin farin ciki ne ya ziyarci Amirah lokaci guda bata yi tunanin Ammi zata ce ta zauna ba duba da irin nasiha da rarrashi da ta yi mata daren jiya,shi kuwa Ɗalha wani irin zufa ya feso masa lokaci guda me hakan ke nufi horar da sa Ammi ke son yi ko kuwa? lokaci guda idanunsa suka rikiɗa suka yi ja saboda tashin hankali da damuwa da ya shiga lokaci guda,wani irin bugu zuciyarsa ke yi kamar zai fita daga kirginsa Ɗalha na cikin wannan yanayi ya jiyu muryar Abba ya ce ''tashi ka tafi kar ku yi rana,yau zaka tafi aiki ko?" Ammi ta ce ''zai ji mana'' da ido Ɗalha ke bin Abba da Ammi kamar wani wawa Ammi ce ta yi magana yayin da ta dauki kofin kunu dake gaban ta ta ce ''dan Allah ka ƙara kula min da ƴan jikokina'' Ɗalha nason yin magana amma ya ƙasa kawai ya tashi jiki babu kwari ya fita daga parlourn,yana jin lokacin da Ammi ta cewa Amirah ''tashi ki kai kayan ki ciki za ki min rakiya zuwa anjima zamu je barkan Hasila ƴar Hajja kaka'' Hajja kaka wata ƙawar Ammi ce ƴar miduguri,Amirah ta ce ''to Ammi''daga haka ta tashi ta wuce ɗaki,tun daren jiya bayan Abba ya shiga bangaren sa Ammi ta bi bayan ta roƙesa ta ce dan Allah ya bar Amirah ta yi kwana biyu kafin ta koma,Abba ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce ''na yi mamaki sosai da mahaifinta bai nuna ɓacin ransa ba ya ce Amirah ta koma ɗakinta ina tunanin ya yi hakan ne saboda mutunci da zumunci dake tsakaninmu'' Ammi ta ce ''ni ma na yi wannan tunanin''Amirah na kwance ɗakinta hannuta riƙe da waya,waya take da Rumaisa,ta faɗawa Rumaisa abinda Ammi ta yiwa Ɗalha,Rumaisa dai har cikin zuciyarta bata ji ɗadi ba saboda abinda ya fi dumunta shine yara da wa zasu zauna harda Ɗalha na tare da yaran amma hankalinta ya ƙasa kwanciya,amma sai ta ɓoye damuwarta bata nunawa Amirah ba sai taya Amirah murna ta yi







SHUUKRAN/022