Page 007
by @oumaphnan
Izzah😎 Sanye take cikin doguwar riga ruwan jinin kare (Maroon) ya yi azaban kwanciya a lafiyayyen fatar jikinta mai matsatsen hannu rabin cinyar hannu an masa adon madaidaitan botuta masu shape din diamond . Ta saka siririn silver agogo silver abun wuya da silver dan kunne designers masu arnan kudi ,takalminta baqaqe masu matuqar tsini da baqar jaka er cifcif ta sagaloshi a kan tsintsiyar hannunta tayi rolling da lallausan baqar mayafi da ya hankade sirrin cikar gashin kanta saboda yanda rabin kanta yake a bude wanda bacin arzikin tarin tuntun gashin da ta kame da ribbon da tuni mayafin ya fadi a kafada saboda yanda ta masa wasareren yafawa.
Cikin wani irin takun gadara ta turo kai cikin kofar shiga reception din tana kallon wajen daidai cikin tangamemen baqar glasses din fuskarta irin na models din nan.
Tuni wajen yayi wani tajin tajin ,sakamakon gimbiyar da suke tsumayi ta samu damar qarasowa .
"Welcome ma....Good morning ma"
Haka kikaji gabadaya wajen ya rikice da mata Barka da zuwa gamida gaisheta .
Ya Salam! Dage giran sama da qasa ta cigaba dayi tana taku tinkis ! tinkis !!
Sir Nuruddeen da sauri ya qarasa gabanta "Barka da zuwa ranki ya dade ,sunana Engnr Nuruddeen Ahmed nine HR manager na wannan companyn" ya qare maganarsa yana mika mata hannu da nufin ya amshi jakan hannunta ya rakata zuwa designed office dinta.
Lahaula wala quwwa! Yanda Yusrah tayi zaka rantse da Allah bataga ɓurɓushin halittansa a gabanta ba bare kuma har yayi mata magana .
Taku daya biyu tayi ta isa gaban table din receptionist din ,inda aka tanaji hand senitizer don tsaftace hannu daga kamuwa da qwayoyin cuta .
A gadarance tasa hannu ta matsi ruwan hand sanitizer din tana rubbing akan tafukan hannunta zuwa bayan hannunta.
Mutuwar tsaye kafatanin al'ummar wajen sukayi sai ma wannan ya kalli wannan ,wancan ya kalli wannan .shanye komai Nuruddeen yayi ya washe dukkan hakoransa.
"Amm ranki ya dade Bari in nuna maki ofishin ki ko?"
Sai sannan tayi magana da daddadar muryarta mai kama da busar sarewa amma mai cike da izgilanci da gadara
"Why not show me dama?🤨😎"
Bai tsaya bata amsa ba yayi gaba da sauri tana bin bayansa tinkis tinkis cike da matuqar izzah ,er firirit da ita sai IQ din international arrogant women. Yanda take tafe haka bodyguard dinta ta mace ke bin bayanta a jehjehly.
Suna isa qofar glass din office din mai amfani da numfashin mutane ya wangale da kansa .daga nan suka shiga wargajejen reception din office dinta wanda shi kadai zai dauki set din kujeru bakwai.
Dage kai tayi tana kallon zubin tsarin adon reception din nata da wajen zaman PA dinta da wajen zaman baqi na wuccin gadi kafin su shiga asalin office dinta .
Yes evrything well well steady .
Dage kanta tayi tana bin bangon wajen da kallo inda aka jera hotunan manyan mutanen qasar an kama daga shugaban qasa da sauransu sai hoton mamanta da babanta ,hotuna dai kusan guda takwas rinkis manya manya .
Waigowa tayi ta kalli Nuruddeen da fuskar shanu "why my picture is not here?" (Me yasa banga hotona ba anan)
Bakinsa na rawa yasoma magana yana qoqarin kare kansa.
Wani irin shan gaban maganarsa tayi da nata maganar "Oh fix it"(A saka shi) Ta bashi umurni da kakkausar murya gamida taune haqoranta waje guda.
"An gama ranki shi dade"
Tass. Tasss tasss ta cigaba da tafiya suna biye da ita.
"Wannan office din fa?"
"Na Mr. A A ne"
"Oh the One that will be deputizing my work?" (Oh mataimaki na?)
"Ofcrs No!" Da sauri ta juyo ta kallesa shaqe da mamaki sai kuma ta kautar da kai "Hajiya bata yi maki maganar sa ba?..."
"Oh shut up ,Dont exceed Your line ok? "
"Sorry ma'am"
Ko kallonsa batayi ba har ta dangana da office dinta ta zare hannunta daga masagalin jakanta ta ajiye akan tangamemen table dinta kamar irin mecin mazaunin mutum 6 din nan sai qyalqyali yake .
"Ina buqatar list din sunan duk wani wanda ya kwana ya tashi a cikin kamfanin nan ,be he a leader ,cleaner kai ko massanger ne ma ,ina da emergency meeting ga dukkan ku noww***"
"Yes ma'am"
Nuna masa qofa tayi da hannunta ,a firgice ya fita daga office din ita kuma ta kewaya ta dauki bottled water daga cikin firinji ta kwankwada ma cikinta "ohhh washhh,this is really hectic ,ko yawan magana yasa maqoshin mutum bushewa..."
Nuruddeen kam saida ya tabbatar ya rabu da ita salin alin sannan ya fara magana a sarari "Ji yarinya er firirit kamar tsinken sakace sai bala'in ɗagawa? Lafiyayyen Giant man dani duk na rude a gabanta tana bani umurni baki na na kyarma.wai me take taqama dashi ne?"
_AKWAI FA TARIN GWARAMA,DONT DARE MISS THIS BOOK ....BABIN FARKO MA NA LITTAFIN BAA FARA BA...KEEP ON TOURCH BYE💃_
Oum Aphnan [6/10, 10:23 PM] Chuchu👻: *GWARZON* _NAMIJI_
Romantic Seductive Erotic Crazy marriage.
Ana babbakar Giwa wazai jiyo qaurin Zomo ,Nayi *Jarababben namiji* ya bada vibes🫦Nayi *Harijin Namiji* was given😘Bare kuma uwa uba *Gwarzon Namiji* . Hajiya a karkade zani a sha karatu ,littafin bai fito ba saida ya shirya 😍 Plz Labarin ma'aurata ne Don Allah in ke ba matar aure bace na haramta maki siya 🙏🏽 _Savoda haka mutum 50👌🏾 kadai zan siyar ma book din Daga Yau_ *01/06/2024 har zuwa 07/06/2024* Damarkine ki biya in saki a Group in aka wuce mutum 50 bazan siyar ba coz in anyi yawa ake samun ɓarayi masu fitar dashi🙃 ₦1000 ne zaki biya ta nan bank din ki karanta cikin salama ba hakkin kowa 7782217014 Mohammed Hassana,Fcmb. Shaidar biya ta nan Number *** ________________