Page 008
by @oumaphnan
An hour later. "Mr Nuruddeen ,gabadaya wannan kamfanin a hargitse yake dole in sauya tsarinta from up to bottom.....I see😏Ma'aikatan cikin wajen nan ko cancantan zama masu goge goge basu kai ba,talkless of being a staff...Ma'aikata fa a hakan? Dole zan kori wasu in sake debo wasu a yayin da wasu za'a rage masu matsayi daga office din da suke zuwa wajen dake qasa da nasu a halin yanzu ,Dole in samu in tidying kamfanin nan within sati Daya kacal"
"Yes ma'am" jujjuya list din sunayen ma'aikatan ta cigaba da yi mai dauke da sunan mutum da rank dinsa
Jujjuyawa kujeran ya cigaba dayi da ita a kai .idanuwarta na kafe a kansa ,shikam banda innalillahi wainnailair rajiun ba abinda yake karanta mata
"Mr Nuruddeen kace kaine HR manager?"
"Yes ma'am" Ya jinjina mata kai cikin tsumewa gabadaya yayi gumi sharkaf ta cikin riga
"Inaso inga takardunka,don in tantance wether You Are qualified to be or not..."
"Yes ma'am! thank you ma'am🙏🏽" ya dan sunkuya zai fice daga office din.
"Mr Nuruddeen ?!" Da sauri ya waigo yana amsa wa "i need a photocopies of these documents " ta ajiye masa list din da ya bata na ma'aikatan da wasu takardun.
"...and ka fada ma seceretary dina bana son ganin kowani baqo har zuwa qarfe 1 na rana ,ko wanene ya juya,saidai in Mr AA ne in yazo a barshi yashigo i've a meeting with him..."
Kafin ya bata amsa aka turo qofar da sallama gamida cewa "Hello Miss Yusrahhhhhhhhh"
Ɗif ya ɗauke wuta ganin wacce take hakimce akan kujeran manager wanda ya tabbata itace yusran da yazo nema.
Yanda ya ɗan kaɗu tabbas ta fishi kaɗuwa . saidai ita tuni rashin kunya yayi overshadowing mamakin ta.
Waigawa tayi ta kalli Nuruddeen "Mr Nuruddeen jeka shigo mun da securities"
Major Adeel kallonta yayi fuskarsa a sake tamkar ba da ita bane din nan suka samu rikici "I cant imaging seeying You here"
Hade rai tayi kamar zata kai masa mari. "Ya akayi ka binciko Ni wannan wani irin baqar naci ne?"
"Na binciko ki kuma?kema anan kike aiki?"
Saida tayi wani irin girgiza tayi balance akan kujeran ya juya da ita hauni zuwa dama kana ta kafe hannunta akan table ta tsaida idanuwarta a kanta "I own it!,wannan kafatanin kamfanin mallaki na ne"
A rude ya nuno ta da document din hannunsa "dont tell me say ke yarinyar Hajiya Juwairiyya ce" caɓe baki tayi a maimakon ta bashi amsa.
"Kai kam na lura na mamajo ne mayen mata ,kuma ka rasa ranar zuwa bibiyan mace sai early morning monday ,Iskanta Ni kake son yi ? Oh tell me iskantani za kayi???"
"Sub__subhanallahi me ya kawo maganar iskanci kuma ana zaune lafiy..." Kafin ya qarasa magana wayarsa ta fara ringing
Daga mata yatsa yayi with due respect ☝🏼ina zuwa plz "
Da sauri ya daga wayar ya kanga a kunne
Daga zubby's kitchen ne "Hello sir ina zamu kai shawarma and other stuff din da kayi order din ,your order is ready and is with me right now"
"Ok kanaji ko wallahi na rigada na fita gida amma Matana tana gidan zaka iya kiranta ga number wayarta....*** ....Bara in maimaita" Zaraf Yusrah ta dauki wayar gefenta ta fara binsa yana fada ma mutumin number tana rubuta mwa a nata wayan
Saida ya gama wayar ya jiyo with full of excitement yace "yawwa muna maganar menene ma?"
Daure fuska tayi kamar dare "Second ashirin kadai na baka kaja sillallun qadafunka wajen nan ,if not wallahi zan kirata...."
Oum Aphnan [6/11, 9:31 PM] Chuchu👻: *GWARZON* _NAMIJI_
Romantic Seductive Erotic Crazy marriage.
Ana babbakar Giwa wazai jiyo qaurin Zomo ,Nayi *Jarababben namiji* ya bada vibes🫦Nayi *Harijin Namiji* was given😘Bare kuma uwa uba *Gwarzon Namiji* . Hajiya a karkade zani a sha karatu ,littafin bai fito ba saida ya shirya 😍 Plz Labarin ma'aurata ne Don Allah in ke ba matar aure bace na haramta maki siya 🙏🏽 _Savoda haka mutum 50👌🏾 kadai zan siyar ma book din Daga Yau_ *01/06/2024 har zuwa 07/06/2024* Damarkine ki biya in saki a Group in aka wuce mutum 50 bazan siyar ba coz in anyi yawa ake samun ɓarayi masu fitar dashi🙃 ₦1000 ne zaki biya ta nan bank din ki karanta cikin salama ba hakkin kowa 7782217014 Mohammed Hassana,Fcmb. Shaidar biya ta nan Number *** ________________