Page3️⃣⏩4
by @prettys01
*KADUNA*
*Bayan an kammala text, suka aka yi lecture sannna aka tashi, a parking lot suka tsaya suna ɗan tattauna daga baya Mymoon da Ma'ishat suka hau motan Mymoon suka bar school ɗin, sannna ita ma Muhibbat ta shiga motar Maryam dan sunfi kusa suka bar school ɗin.
Da idanuwa suka bi motan Maryam da ya bar makaranta, wani ɗan sanyi ne ke ratsa zuciyar Abbas in dai a ga wani abu na Maryam balle da ya hangi fuskantar ta. Trekking suka sha har gida duk da akwai nisa sosai, bayan sun shiga layin nasu, wani gida suka shiga ina da ba za ka yi tsammanin ganin su ba, ɗakin dake zaunen gidan suka zazzuna kan katifa. Gidan su Abbas ne da Shamo dan su gidansu ɗaya imfact yaran kishiyoyine amma babu mai ganewa dan wata muguwar shakuwace tsakaninsu, Ibrahim da Abdul kuma duk maƙotane amma ana suke ƙwana in da suka yi ƙofa ta waje, da yake ɗakin ba laifi akwai girma, katifar biyu suke amfani da shi sannan ga tsohuwar wardrobe ɗin su, wanda ana suka sanya kayansu, sai kuma renting da suke yi wajen Ado mai wanki.
“Na samo Numbers ɗin M-Ladies, na tura muku ta whatsApp.” Shamo ya faɗa tare da ciro arniyar wayansa.
“Wow mutumina, a gun Zubaida ka samu ko?.”
“Eh mana, sai ku fara gina love tin yanzu, balle kai I.B kasan Mymoon akwai ji da kai.” dariya suka yi sannna Abbas ya ce.
“Hmmmm Allah ya ganar da ku, dan wannna hanyar akwai matsala.....”
“Kul, kar ka mana mugun baki, yadda kake son Maryam haka muke son namu.”
“Dena tada jijiyan wuya, ni kunga na fita dan yau zan fara zuwa gareji.” dariya suka kwashe suna mai a dawo lafiya. Shikam ko a jikinsa ya yi waje tare da nufan gajeri dan fara aikin da ya sha wuya aka bashi dan wai ya girma sosai.
*Ma'esh*
A ƙofar gidan su Ma'esh ta faka, sannan suka yi sallama tare da rabuwa, ba ƙwarya, gidan su Ma'esh ya haɗu sosai, ciki ta shiga a in da ta hangi mota baƙa a harban gidan tana mai cin burin ta fara zuwa school da ita. Wani parlour ta shiga wanda ya gaji da haɗuwa, a kujera ta zauna tana kallon TVn dake aiki, ta jima babu motsin kowa sai daga bisani wata mata ta fito daga ɗaki.
“Ma'esh kin dawo?.” matar da a kallo ɗaya za ka ga mugun kaman da suke yi, sai dai shekaru su banbance.
“Aunty na dawo.” ta faɗa da kyar.
“Lafiya!? Me aka miki?.” wacce ta kira da Aunty ta nufeta da sauri, dafata ta yi tare da sanya hannu ta share mata hawayen idanunta.
“Faɗa min, what's wrong?.” Aunty ta faɗa.
“Na faɗa miki I need my own car but.....” sai wasu hawayen, da sauri ta miƙe tare da barin parlour, da idanu Aunty ta bi ta, tana mai jin zafi a ranta, dan idan kana so ka kanta a wani hali ka taɓa mata Ma'ishat.
“Bara Alhaji ya dawo dole yasan abin yi, domin buri na shine faranta miki rai.”
Tana shiga ɗakin ta kulle tare da hawa kan gadonta, wanda ya gaji da tsaruwa. Tasan dole Aunty ta ɗau mataki.
*Merry*
Merry tana yin horn aka buɗe mata, sannan ta shiga, tana yin parkinga ta nufi cikin parlour su, masu aiki ne kawai ta tadda dan har lokacin Mom ɗin ta ba ta dawo ba. Ba laifi nan ma gida ne mai sunan gida, dan a kwai komai na more rayuwa, kuma ko ina ya ji kuɗi, kana isowa za ka gane gidan sojoji ne dan uku suna gadi ta waje haka ciki akwai mutane biyar, manyan sojoji masu ƙarfi.
*Muheey*
*Kwance take kan kujera tana latsa waya cikin nishaɗi, dan tin bayan da ta shigo daga school ta haye kujera tana chart da wani wanda ba ta san waye ba, murmushi ne kwance a kan fuskarta. Sai dai muce Alhamdulillah, domin kuwa a kallo ɗaya za ka ma gidan ka fahimci akwai rashin wadata kaman na sauran amma akwai rufin asirin Allah, kiran sunanta a ka kuma yi dan haka ta miƙe da nufi ƙaramin tsakar gida amma a ɗan gyare yake.
“Haj. gani.” ta faɗa tana isa gaban matar dake zaune kan tabarma tana yankan kabeji.
“Na faɗa miki ki sha gari ki zo ki amsa girkin nan, kafin ki fice, yau Allah ya yi kin leƙo mu.” wani abu ne ya tsaya mata a rai, amma ta kasa magana, ganin haka bai da amfani shi yasa ta koma ɗaki dan shan gari ta amsa aikin kafin ta bar gidan zuwa in da take ƙwana.
*Mymoon*
Wani haɗaɗɗen place ne mai matukar haɗuwa, yana bene haka kuma ya tsari, stairs Mymoon ta fara takawa zuwa bedroom ɗinta, bayan ya shiga aljannar duniyar ta, ta shiga bayi ta yi wanka sannan ta fito ɗaure da towel tana tsane dogon gashin dake kanta. Zama ta yi tana mai kallon chocolate ɗin da ke kan bed, da sauri ta dauka tare da yaga ledan ta kai baki, dan ita akwai son kayan zaƙi.
*************************************
*KANO*
Bayan ta shiga wajen direct in da jiya ta shiga nan ta nufa tana da maimaita addu'oi a cikin ranta. Ta riga ta saba duk in da ta bi sai an zuba mata saboda irin shigarta, dan a yanzu ko a jikinta dan an bi ta da kallo. Bayan ta shiga wajen da kai ta gaishe su, sannan ta hau layi, in da mutane huɗu ne gabanta. Daga kallon wajen ta fahimci wanda ake jira yana nan. Wayarta ta ciro tare da rubutu sai ta miƙa ma wacce ke gefanta, da yake jiya sun haɗu to tasan ba ta magana dan haka ta amsa ta karanta sai ta ce.
“Hmmmm Sister, wai ce wa ya yi da baki zai mana tambayar kuma mutane biyar zasu ɗauka dan suna da mutane.” da jinjina kai tana kuma wani typing ɗin, bayan ɗayar ta duba ta ce.
“A ƙalla mutane 15, sun shiga kuma gamu mu huɗu.” alaman godiya ta mata tana mai da wayan tare da tsare ƙofan da kallo har wanda ke ciki ta fito, sannan wani ya shiga, haka haka har wacce ke kusa da ita ta fito rai ɓa ce, a kallo ɗaya ta fahimci akwai matsala, dan haka ta dafata tana ɗaga mata kai.
“Na haƙura nikam, ki shiga Allah ya sa ki da ce.” daga haka ta wuce, take jikinta ya yi sanyi, sannan ta nufi ƙafan ta tura a hankali, tana sallama a cikin ranta.
Duk da tana cikin niƙaf amma sai da lafiyyan ƙamshi ya dake ta, lumshe idanunta ta yi, sannan ta kalla officer ɗin, ba laifi ya haɗu, duk da akwai abubuwa da ko ina na da ga na'urori, cameras da dai sauransu. Namiji ne ta hanga tsaye jikin glass yana kallon haraban gidan tvn, matsawa ta yi ta zauna tunda ya ji ya tashi. Tsaye yake cikin manyan kaya, hannusa riƙe da flask tea yana sha a tsaye, juyowa ya yi tare da nufo in da take tsaye sannan ya mata alama da ta zauna, a ɗan daburce ta zauna dan ya mata ƙwarjini. Guy ɗin ya haɗu ma sha Allah, dogo mai cikar kamala. Shima zama ya yi. Yana mai kallonta dan ko ƙyayar idanunta ba ya gani.
Take wayarsa ta kuma yin ringing sai ya ɗaya.
“Darling still mace ce......” take ta jiyo muryan mace ta cikin wayar tana cewa.
“Ta yi waje, na faɗa maka maza zalla.”
“Wanan matar aure ce fa.” ya faɗa yana kuma kallon yarinyar da ke zaune.
“Juya cameras kanta ya yi.” kafin ya yi magana ta katse, sannan ya yi latse-latse a System, ba'a jin ba ma wayar ta kuma yin ringing.
“Ka mata interview ɗin.”
“Okh my Darling.” daga haka ya sauke ajiyan zuciya yana mai faɗin.
“Takaddu.” da yake ta ciro sai ta miƙa mai ba tare da ta falle rubutun ba, ya amsa yana dubawa.
“Uhmmm your full name.” da sauri ta miƙa mai wani paper ya amsa ya kalla. (My name is Ameeratulkhairi. Sa'adatu Jibril) shine a rubuce sai ya ɗago da ɗan faɗa.
“Ba ki da baki ne, dan kina matar aure, ba za ki yi magana ba?.” da sauri ta kuma miƙa mai wani, kamar ba zai amsa ba sai ya amsa. (Bana magana, Bebiya ce.) Take ya ji wani abu ya tsirga a zuciyar sa. Sannan yaji tausayinta sai ya aje.
“Na fahimta, kinsan kafin na baki aiki dole kiban labarin ki, da dalilin son aikin journalist, da kuma irin gudummawar da za ki ba da sai kuma wani fanni dan na ga ba ki yi zurfi a karatu ba.” ɗaga mai kai ta yi sannna ta cori wani littafi tana miƙa mai. Ya amsa yana mai buɗe wa. ( Buri na shine zama ƴar jarida) shine ya fara cin karo da shi sannan ya ɗago ya kalleta.
“Ki je gobe ki dawo, misalin 1:30pm, in dai labarin ki ya gamsar shike nan.” godiya ta mai da hannu sannna ta yi fara tafiya, sai ya samu kansa da bin bayanta da kallo da sauri ya ɗauke kai yana cewa.
“Ki gaidamin mijinki, bangan shi ba amma ya burgeni da yake sa ki yi wannan shigar.” murmushi ta yi tana mai ɗaga kai tafice. Take ya hasaso Darling cikin shigar nan za ta yi ƙyau amma ko mutuwa zai yi ba za ta sanya ba, yara sa maike yawo a kansa ne, da zarar ya bar gida yakan ta jin wani yanayi akan ta da kuma abubuwan da baya so ta na yi, amma da ya ji muryanta ko ya koma gida shike nan sai ya mance. Kallon rubutun ya yi da ya yi mai mugun ƙyau, ita ce ta ƙarshe dan haka ya buɗe shafin gaba. (Labari na mai ɗauke da darasi da haƙuri.) Sai ya yi murmushi ganin rubutun da yawa ya sa ya miƙe sannan ya hau kan sopa ya hau karatu.............
*ABUJA*
Office ne wanda yake cike da takkadu, zaune yake kan kujera yana latsa system sannan yana kallon screen ɗin, knocking aka yi ya ba da umarnin shigowa. Take aka shigo, wani saurayi ne sa'ar shi, yana rike da laptop ya ce.
“Aboki na kammala.” sai ya kalla abokin na sa ya ce.
“Good job, yau za ka raka ni wani waje.”
“Hmmmm na san yanzu burinka kawai kake so ka cika, amma a ganina Ukasha ka sauya shawara please.” sai ya bar latsa system ɗin ya zuba ma abokin na sa idanun.
“Umar, dole na cimma wannan burin na wa, a yanzu biyu na ƙasa saura biyu, na tambayeka, burina zan fasa? ko na Hussain ɗina?.”
“Haka ne, shike nan, Allah ya cika maka burin na ka.”
“Ameen Umar, nan da watan biyu nake so na yi auren.” sai Umar ya ja numfashi yana kallon Ukasha take magana a cikin ransa.....
'Shin kunsan waye Ukasha?, Kunsan labarin rayuwarsa? Kusan ya halinsa? Kunsan ya nake haƙuri da rayuwa da shi? Kunsan ya yake ɗaukan Burinsa? Wai ma kunsan menene Burin? To Bara na baku labarin a kan Ukasha da kuma Burinsa...........✍️
> To Umar za mu haɗu next page. Still C.E.O muna jiran labarin Ameeratulkhairi. Sai jama'ata kunsan ina yin Ladies kuwa, haka su Abbas ma..........hmmmmm......akwai aiki...... PRETTYN JAJIRTATTU ce ✍️🥰🤗.
***
*_HASASHE KO BURI_*
_SADAUKARWA_ *🌟 I proudly dedicate this platform to all the strong and creative minds of our team — JAW (Jajirtattu Writers Association).* You are more than just writers — *you are voices, strength, and inspiration!* ✍️💪
🕊️ *May Allah keep us united, uplift us, and make our pens a means of positive change.*
Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥 *Keep shining, JAW family!* 🌺
*** 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.
💔 *_HASASHE KO BURI_* 💔
> 📖 A powerful story filled with dreams, struggles, and destiny!
💡 *Ka shirya?* Wannan ba labari bane na wasa — *it’s a journey into the heart of dreams and reality!* 😍
🛤️ *Rayuwa tana tafiya...* _Kowa na da *burinsa*, amma ba kowa ne ke iya cimmawa ba. Some dreams are *sweet hopes*, others are silent battles_💭⚔️