HASASHE KO BURI

Page1️⃣1️⃣⏩1️⃣2

by @prettys01

*KANO* Bayan ta isa gida, ta tadda ƙanwar mahaifiyar ta ta zo, da yake a nan take ita ma, ta yi tafiya ne zuwa Abuja dan kasuwancin ta, business take yi kuma ita ke rufa musu asiri kamar yadda suka rufa mata ita ma, domin mijinta ya rasu, kuma ba ta haihuba, danginsa suna ƙi ba ta komai, shine ta dawo gidan na su.

“Na yi kewarki.” ta faɗa amma ta hannuwa, matar ta fahimta sai ta rungume Ameeratulkhairi ɗin tana faɗin. “Ni ma haka, wallahi duk lokacin da na kalle ki, sai na ji wani tausayinki na taso min, insha Allah maƙiyanki sai dai su mutu, sun rabaki da abin da ya ke na ki, wanda Allah ma ya baki suna so su ƙwace.”

“Ke dai bari, yanzu haka daga gidan Tvn take, wai za ta yi ɓangaren ɗauko rahoto.”

“Mubarta, idan suna tsammanin ta nakasa kenan to akwai wani baiwar ai. Ƴata ko ina ne ni zan tsaya miki sai dai karki kuskura duk rintsi ki bayya wa duniya jikinki, hatta fuskarki bansan ta bayya wa kowa.” Ameeratulkhair ta ɗaga mata kai tana mai ɗauko abinci dan yunwa take ji, farin ciki ne fal ranta dan tana da yaƙinin wannan ƙyakkawan bai karanta littafin ta ba.

“Yanzu wannan ne ake nuna kishinsa haka, tab ni kuma sam bai mun ba......uhm shan koko kwanciyan rai.” ta faɗa a zuciyarta dan tina matar da ta kira C.E.O, shi kuma har da rawar jiki ana ce mata Darling. Murmushi take tana mai bar wannan tunanin a cikin ranta........

Babu page ɗin da ya tsaya sai *Zuciyata* , murmushi ya saki yana mai fara karantawa. “Ban tsammanin zan yi aure a rayuwata amma idan har zanyi, ina buƙatar don wasu abubuwa akan mijin. Bayan ilimi, nagarta, hali mai ƙyau, akwai wasu abubwan da na ke so. Misali Namiji mai suna Namiji, natsana Mata-maza, ban san namiji ya zama kaman yaro, na juya sa yadda na ke so, a'a na fison namiji mai izza, mai cika ido, mai zafi, mai ƙarfi (ba wai dan mu yi faɗa ba, dan in na taro faɗa ina da shi.)” Ajiye wayan ya yi yana mai jin abubuwa biyu na taso mai, na farko tamkar da shi take magana, kamar dai yadda Darling ke juyasa.

“Dama ni Mata-maza ne?.” ya tambaya kansa, wani zuciyar nasa ya ce masa 'Eh' tsaki ja yana mai miƙa wa, ta ku biyu ya yi sai ya tsaya cak, yana duban jikinsa, ko zai ga duk abin take faɗa, ya jima a tsaye sannan ya ƙara karanta sauran layikan.

“Ƙyau, sanyi-sanyi, taushin murya, tafiya a natse, fara'a mai yawa, da kuma iya soyayya, *Duk bansan namiji da su* wallahi banso.” daga nan shafin ya ƙare, sai ya kasa motsi, dan da fari komai ta faɗa, sai ya auna kuma yaga yana dashi amma at end wai ta tsana hakan. “To ya take son Namiji?.” ya tambaya kansa, dan akwai aikin da zai yi da ya zauna karanta shafin gaba, ɗan uwan wannan.

*ABUJA*

Washegari tare suka je office, bayan sun shiga kowa ya shiga nasa office ɗin dan yin aiki, basu suka tashi ba sai misalin 6. Haka suka juyo dan dawowa gida, ta cikin motan ne, Ukasha dake gefe ya hanga wata budurwa tsaye daga tsallake tana siyan abu a sago, da yake utone ne, sai suka zagayo ta gafen da take, take yarinya ya bar shagon tare da shiga wani layi.

“Umar bi wancan yarinya.” ba musu ya karya kwanan motan tare da bin ta a hankali, wani gida ta shiga dan haka suka faka, take wani yaro ɗan saurayi ya fito daga ciki, da sauri Ukasha ya fito yana ma yaron magana. Bayan sun gaisa ya ce.

“Dan Allah yarinyar da ta shiga yanzu, kasanta?.”

“Eh yayata ce.”

“Ma sha Allah, in ba damuwa ina son na ɗan tambayeka a kanta.” bayan saurayin da ba zai wuce 20yrs ba ya ɗaga mai kai sannan Ukasha ya dasa magana.

“Ya sunanta? Kuma dan Allah an mata miji ne?.”

“Sunanta Fillo, ko ka ce Fatima, da yanzu an yi auren amma aka fasa saboda ko kwanji ne, ko menene.... Na dai manta.” sai ya ɗan yi murmushi, yana maimaita sunanta Fillo, ba ƙyarya daga nesa ya hangi haksenta, kuma ga wannan ƙanin nata shima fari ne.

“Ka mana sallama da ita.” bayan yaron ya shiga sai can ya fito tare da faɗin.

“Ta ce sai ka fara samun Baba am(Baba), in ya ba ku izini sai ta fito.” number Baba am ya amsa tare da wuce wa.

“To Allah ya sa, munyi da cen ɗaya, dan ga alamu, akwai tarbiyya a gidan.” Umar ya faɗa yana fita daga layin, shi kuma Ukasha yana ta maimaita sunan ta *Fillo* .

*****Omo ta siyo, dan haka wanke-wanke ta shiga yi, ko da ƙaninta ya faɗa mata wasu na neman ta sai ta mai magana cikin fillanci.

“Kace su nema Baba am, in ya amince to.” aikinta ta ci gaba da yi, can sai ya dawo yana murna an bashi dubi biyar. Bafullatanar da ke wanke-wanke ta kalla ƙaninta da suke kama da juna sosai, kafin ta ce komai sai ga wata mata ta fito tana magana da fillancin.

“Ban kuɗin.” yaron ya kalleta tare da juyawa ya fice, yana ji tana kiran sunan sa 'Moddi.' amma ya shareta. Budurwa da ba za ta wuce shekara 20 ba ta yi murmush. Take ta wani haska, dan a lokacin na mata kallon tsab. Ƙyaƙƙyawace ajin farko, tana haske mai sosai, sannan ga uban hanci ma sha Allah, duk da ta ɗauka ɗan kwalli amma gashin mai uban tsayi ya sauka har gadon baya.

“Dada am (Mama) ya gudu ai, kinsan Moddi da son kuɗi.”

“Zai dawo ai.” matar ta wuja ta koma ciki. Su huɗu suke rayuwa, Ita Fillo, Dada am wato mama amma ba ita ga haifesu ba, kishiyar Mamarsu ce, mahaifiyarsu ta rasu tin suka yara, Dada am ce ta raine su, ita ma ta haihu amma yaron ya ɓace tin yana ƙarami, ko ita Fillo lokacin tana jaririya ya ɓa ce, an dai ce lokacin shekarunsa 6 ne.

Alhamdulillah domin suna rayuwa cikin ni'imar Allah, ba sa samun matsala da Dada am, domin Fillo yarinya ce natsatstsa shuru-shuru. Da dai shiga wani hali sosai da aka fasa aurenta da wani da take mutuwar so, saboda ƙwajin jini dukka 'AS' ne, daga lokacin ta ɗaura aniyar ba za ta ƙara soyayya ba sai bayan ta yi aure, da faruwan al'amarin wata na uku kenan, sannan kusan kullum sai anyi sallama da ita amma ba ta fita sam. Sai ta ce su nema Baba am.................

*KADUNA*

Su uku ne suke zaune suna raha kwanin sha'awa, sam babu mai damuwa a cikin, dan a yanzu suka ƙara tabbatar da Allah yana matuƙar ƙyaunarsu. A yanzu I.B ya riga ya rikita Mymoon da zazzafar soyayyarsa. Yadda kasan asiri koma ya ce sai ta yi, domin kuwa ya iya sarrafa mace fiye da lissafi, hatta mota ta mallaka mai. Shi dai yana cikin alheri dumu-dumu. Sun zama wasu manyan mutane, dan ko su Shamo suna jan kuɗi ba wasa suna target ɗin su mallakar mota. A dai-dai lokacin Abbas ya dawo daga garaji dan alhamdulillah yanzu yana samu ba laifi, wata rana dubu uku ko biyu. Kuma yana jin daɗi in ya samu, kuma yana fatan nan gaba ya fi haka dan haɗama Merry lefe. Bai manta ba a lokacin da ya faɗan masu Abdul ba, dariya suka sa mai suna ganin wautarsa ƙarara amma ya share su dan shi yasan mai ya taka, kuma ya dogara ga Allah.

“Assalamu Alaikum.” suka haɗa baki suna amsawa. Shamo ne ya kalla kayan jikin Abbas ya yi murmushi yana faɗin.

“Aboki, kana wahalar da kanka wallahi, dan Allah ji yadda ka kamo duk ka yi ɓaki ma........... Ka bar wahala Merry nasan za ta taimaka maka amma kai dan aci da Gumi ka ƙi......”

“Shamo bar ɓata miyanka, kasan Abbas, in ya faɗa abu baya sauyawan mu dai mu tayasa da addu'a. Ga wannan wallahi bansan ganinka cikin kayan nan, kuma wannan aikin.....” da sauri Abbas ya fizge rigar da I.B ke miƙa mai yana faɗin.

“Good da ka san ban sauya ra'ayi. Kuma in addu'a ce ku zan yi ma wa.”

“Abbas wallahi muna sonka, bamu son ganin kana aikin mai wahala, kafimu haske amma jibi yadda ka koma, mukan sai wani fresh muke yi.” sai dai ya kalla Abdul da ƙyau, kaman zai ce abu amma ya fasa tare da shigewa bayi dan yin wanka. Yasani ba sai sun faɗa mai ba, suna sonsa sosai, kuma ba sa son aikin da yake yi, suna yawan faɗa mai, su za su nema amma shi ya wuta sai suba shi amma ya ƙi sam. Kuma ba ƙarya wani fresh suke dan kuwa ba ƙaramin daɗi suke ci ba. Haka zai dawo ya tadda uban leda tsire, balango, drinks, marada kuwa hmmmm, sannan komai suka ci sai sun aje mai, wani lokacin ya ci in sun matsa. Bayan ya fito wanka ya samu suna shirya wa tare da cika ɗakin da ƙamshi.

“Ka shirya mu ajeka a ƙofar gidan su Merry.” I.B ya faɗa yana taje ɗan gemunsa. Dayake yana son zuwa, aikuwa suka shirya dukkansu. Sun yi ƙyau kaman za su wani taro, Abbas ne ya zura wata jallabiyarsa, sun mai tsiya da ya cire amma ya yi banza da su. Mota suka hau, a hanya Abbas ya ce su tsaya bayan Abdul ya faka dan duk sun iya mota hatta Abbas ya iya. Bai jima ba ya dawo riƙe da leda baki.

“Mutumina me aka siyo ne?.”

“Merry na son awara shine na siya mata.” dariya suka kwashe suna kallon Abbas da hankalinsa ƙwance kuma ya yi banza da su. Shamo da ke gefensa ya dafa kafaɗarsa yana faɗin.

“Abbas, da baka siya ba, taya mace kaman Merry ta ci awaran bakin hanya.”

“Hmmmm za ta ci.” ya faɗa da confidence ɗin sa dan yasan duk abin da ya ba ta cike da nishaɗi yake amsa kuma bai ta ɓa ganin sauyin yanayin a fuskarta ba, shiyasa ko ba yawa yake siya mata abu in dai yasan tana so. Yanzu haka awaran dari biyar ya siya mata............✍️ END.

> Tab akwai ƙura fa, hmmmmm mudai na mu ido, 🥱🙄🙄🙄🙄🙄

> Hmmmmm ✍️✍️✍️✍️ ba wasa *HASASHE KO BURI* tafiyar wannan na daban ne domin akwai abubuwan ban mamaki, taɓa zuciya, ruɗani da zalama irin na ɗan adam. Mu daihe zuwa.......... PAID BOOK ne 😏 by PRETTY SK NOVERLIST 🥰

🔥 *Let’s goooo!* 🔥 Hit that LIKE 👍 if you're truly *ready for the ride*! Because *HASASHE KO BURI* isn’t just a story — *it’s an experience.* 💭✨📚

✍️ _By PRETTYN JAJIRTATTU_ 💕

***

*_HASASHE KO BURI_*

_SADAUKARWA_ *🌟 I proudly dedicate this platform to all the strong and creative minds of our team — JAW (Jajirtattu Writers Association).* You are more than just writers — *you are voices, strength, and inspiration!* ✍️💪

🕊️ *May Allah keep us united, uplift us, and make our pens a means of positive change.*

Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥 *Keep shining, JAW family!* 🌺

*** 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.

💔 *_HASASHE KO BURI_* 💔

> 📖 A powerful story filled with dreams, struggles, and destiny!

💡 *Ka shirya?* Wannan ba labari bane na wasa — *it’s a journey into the heart of dreams and reality!* 😍

🛤️ *Rayuwa tana tafiya...* _Kowa na da *burinsa*, amma ba kowa ne ke iya cimmawa ba. Some dreams are *sweet hopes*, others are silent battles_💭⚔️