PAGE 1️⃣9️⃣⏩2️⃣0
by @prettys01
*KADUNA*
Washegarin ranar, tare suka shiga makaranta, yau suna da lecture, bayan an tashi, a haraban da suke zama suka zauna su uku, dan I.B yana can class suna magana da Mymoon.
“Baby a ina shi yake Taj ɗin?.”
“Yanzu yana Dubai ne, tamkar yaro haka Dad ya ɗaukesa, marayane, yaron abokin sa ne."
“Hmmm har na harbo jirkin.” I.B ya faɗa yana ɗan murmushi.
“Me ka gane.” ta faɗa tana ƙare mai kallo, ya yi ƙyau sosai, yana sanye ne da ƙananun kaya sun mai ƙyau sosai, ba ƙyarya Ibrahim ƙyakkwane.
“So yake ya aure ki, ya mallaka duk abin da yake na ki, wasa yake so ya yi da hankalin ki da na Dad, shin idan kun haɗu yana sake miki sosai.”
“Ina ɗan ɗacin rai ne, rabon sa da Nigeria ina ga 3yrs kenan, amma Dad ya ce soon zan dawo.”
“Okh, to bara kiji, kuɗinki yake so, so yake ya mallaka duk abin da yake naki, na tsana naga namiji a haka, mutum ya dage da guminsa, ya fi. Hmmm ina da shawara in za ki yadda.” sai ta kalla ƙasa saboda irin kallon da ya cilla mata na soyayya, a zahiri ne yake a natse amma daga ta ciki, wani mugun razana yake, domin yaga samu kuma samun na neman ƙwace mai.
“Baby ina jinka?.” sai da ya ƙara gyara zama, amma ba su mannu ba duk da kujera ɗaya suke kuma gaba da juna, sannan ya ce.
“Ki buɗe kunnuwanki da ƙyau, ki ji duk mai na ce, sannna ki yi shawara duk abin da zuciyarki ta yanke miki, shawara shine, account ɗin ki nawa?.”
“Guda biyu ne.”
“To zan buɗe miki wani, amma da sunana za'a yi komai, kuɗi kawai za ki dinga tarawa, domin goben ki, domin kuwa nan gaba zai iya bijirowa da mallakar kuɗin ki, to a lokacin sai ki nuna kema fa kina da madafa, hatta filaye lokaci ya yi da za ki mallaka abubuwa da yawa.” murmushi ta saki dan shawararsa ta yi mata.
“Haka za'a yi, hatta su filayen duk sunan ka zamu sanya, idan nan gaba Dad yaƙi ɗaura mana aure, sai mu nema wasu su wakillce mu.” wani farin cikin ya mamaye zuciyarsa sannan suka miƙa, da motarta suka bar school ɗin, dan a ranan sai da suka buɗe bank a access, sanna ta tura dubu ɗari uku, sai misalin 3:30pm ta kaisa unguwar su, yau kam ta biya sa dan wani farin cike ne fiye da za to.
“Ka fara neman filaye dan zuwa next week kuɗin za su iya haɗuwa.”
“To shike nan, Baby kin yi tinani mai ƙyau sosai, kuma nan gaba za ki ga amfanin haka."
“Hmmmm, ina alfahari da kai, na gode, ka nuna min hanya mai ƙyau.”
“Baby ai ke tawa ce, sannna wannan ya zama secret domin kuwa in Dad ya ji zai miki iyaka da wasu abubuwan."
“Insha Allah Baby.” daga haka suka yi sallama sannna ya fita ita kuma ta tada motar tana barin layin.
*ABUJA*
Sai dare Baba am, ya shigo gidan, da yake har sallan isha'i ya yi, sai ya kulle gidan, yana shiga parlourn aka kawo nepa, sai ya sanya wayansa a caji yana nufan ɗakinsu. A ciki ya tarda Dada am na salla, bayan ta isar ta mai sannu da zuwa sai ya amsa. Watsa ruwa ya fara yi sannna ya dawo parlour, a lokacin har Dada am ta haɗa mai abinci sannan Fillo ta dama mai fura da nono, sai bayan da ya ƙoshi sannan ya kalla Fillo ya ce mata.
“Ƴata, na amince idan wannan saurayin ya zo da ki fita, sunansa Ukasa. (miɗo acci so gorko on wi’i Ukasa ardataa, so mo yahi ardataa.)...........Na ya ba da hankalinsa sosai, sai dai ya faɗa min wani abu wanda da ƙyar za ki yadda. (Mo ɗaɗi mo waawi yeddu, kono mo wi’i min koɗɗo mo jogii, tee ko on woodani ɗum, miɗo tuugii on)."
“Baba am, miɗo naati. ( Babana, Ina jinka).” sai da ya sauke ajiyan zuciya sannan ya ce.
“Mo wi'i: gorko ɗum yiɗi ammbude rewɓe nayi ɗiɗi e jam. A acci sabu don ɗum walla a woodani? Mi yaafa ɗum wi'i min goonga, tee gorko ɗum naatata mi. (Yaron yana da burin auren mata huɗu lokaci guda. Shin na amince da hakan ko kuwa ba zan iya ba? Na ji daɗin gaskiyar da ya faɗa min, kuma yaron ya shiga raina).” sai ta saki murmushi, ta yi mamakin jin haka amma ita za ta yadda, domin a aladarsu ta fulani yarinya na kai shekara 13/16 ake mata aure amma ita ta kai 20, duk da ba ta haɗa ba dukka.
“Shike nan na amince.” ta faɗa tana miƙewa tare da barin wajen da sauri.
"Fillo akwai kunya. (Fillo ena heɓɓude semteende).”
"Aikam, ai ta gado jinin mu. (Ato, ko mo lootii ɗuum ndiyam.)”
"Da fa Yayansu na raye, da shima ya yi aure ko ya kusa. (So rewɓe mawni ɗum woni, mo ɗuum kadi yoo mbaɗi ngam jooni.).” ta faɗa tana mai jin kewan yaronta, shi kaɗai ne gudan jininta, amma ta rasa tin daga zuwa makaranta a can Allah ya yi sanadin, dan jin shuru shine suka je school ɗin amma babu shi, da yake wasu a layin ke tawo da shi to a ranar su an koresu school fees, shine da aka tashi yaron ya kama kansa shima.
"Eh, daya kusa Allah dai ya jiƙan Jauro. (Ee, mo jooni, Alla yo yaaru Jauro).”
"Ameen."
*****Bayan sun koma gida aikin gida suka yi, sannan suka ɗaura girki, ba laifi gidan madaidaici ne, gidan zaman mutum ɗaya, amma two bedroom ne, ɗaya na Ashake da yarinyar da Uncle ɗin ta suka haifa. Bayan isha'i suka zauna suna hira a parlourn, su biyu ne amma Amira ta yi barci.
“Yóò kam, sáákí Hamdalah, we made some sales today, not bad at all.” Maman Amira ta faɗa tana ƙirga kuɗin hannunta.
“Rárá o, weekend is tomorrow — no work, Insha Allah I go wake up do laundry." "Okay, do you even know your brother said someone talked to him? And he said the guy will come tomorrow to greet you." Take ta haɗe fuska "Uhmm, I just hope it’s not one Hausa guy o, because me I no fit marry Hausa guy abeg."
"Ashake, seek God's will o, look at me now — I married your brother and I’m Igbo!" "True, but Hausas can be wahala sha."
"Uhm, that’s it. This your shirt fit me small sha." Ta faɗa tana cilla mata sata doguwar rigarta, dan ya matseta sosai
“Wow, I like it — thanks!" Ta faɗa dan rigar na burgeta sosai.......✍️ END. > Kun fara hasashen me zai faru kuwa. Ukasha dai buri ya kusa cika tunda ga Fillo da Ashake a hannu, ko ya zasu yadda da wannan haɗin oho..... *SHAMO* anya kana da imani, ke kuma so ya rufe miki eyes ko! Hmmmmm tafiyar yanzu aka fara, na faɗa muku labarin mai tsawo ne...... PRETTYN JAJIRTATTU ce ✍️
🔥 *Let’s goooo!* 🔥 Hit that LIKE 👍 if you're truly *ready for the ride*! Because *HASASHE KO BURI* isn’t just a story — *it’s an experience.* 💭✨📚
✍️ _By PRETTYN JAJIRTATTU_ 💕
💔 *_HASASHE KO BURI_* 💔
> 📖 A powerful story filled with dreams, struggles, and destiny!