PAGE 2️⃣1️⃣⏩2️⃣2
by @prettys01
*KANO*
Bayanin komai ya musu sannan ya musu fatan sa'a dan zuwa gobe zasu tafi, a ƙalla sati ɗaya za su ɗauka sannan da sun dawo za su shiga tace hotohutana tare da gyarasu. Barin su ya yi yana mai nufan office ɗin sa.
“Yanzu ƴan gidan ku, za su yadda ki yi sati ɗaya a wajen aiki, gashi yau kika fara zuwa." Ajiyan zuciya ta sauke sannan ɗaga mai kai.
“Shike nan, gobe misalin 10:30am za mu ɗau hanya." Nan ma ɗaga mai kai ta yi sannan ta miƙe, da sauri ya bi bayan ta yana faɗin.
“Ameeratulkhairi, ki zo da wuri saboda harda I.D card zamu baki sannan ki tawo da passport.” sai ta tsaya cak, sannan ta ci gaba da tafiya, tare suka hau Napep, sai magana yake mata amma ta yi banza da shi, shi ya fara sauka sai a lokacin ya tina bai da kuɗi dan haka ya koma cikin Napep ɗin, sanna mai Napep ya ci gaba da tafiya, a dai-dai in da ta buƙata aka sauke ta, bashi kuɗin ta yi sannan ta wuce, da idanu yake bin ta har mai Napep ɗin ya juya, har gida aka kaishi, wani babban gida mai ƙyau, wajen mai gadi ya amsa 5k sannan ya ba mai Napep ɗin, aikam ya dinga godiya dan kuɗin 2k ne. Transfer ya yi ma Sule mai gadi na 10k, aikam shima shima ya yi mai godiya sosai, motarsa ya hanga har an dawo da ita, da sallama ya shiga babban parlourn gidan, amma ganin mata ne zaune kawai kuma kishiyoyin Ummin sa sai ya haɗe rai, a rayuwar nan ya tsan ya shigo ya taddda su domin munafukai ne, sannan suna yawan sanya Ummarsa zubda hawaye, da dai yasan kishi suke yi da Ummi amma yanzu ya fahimci tsabar hassada ce, dan shi kaɗai ne namiji a gidan, gashi mahaifinsu ya tara maƙudan kuɗaɗe, sai dai ba su san shi kuɗin Alhaji ba ya gaban sa ne.
“Barkan ki da gida, ina wunin ku.” ya gaishesa cikin jimla, sai dai me babu wacce ta amsa sai ma bi shi da suke yi da wani irin kallo, shikam a banza dan kuwa ko a jikinsa, part ɗin Ummi ya wuce direct.
“Kinga wannan tsinannan yaron kullum ƙara ci gaba yake, hmm na tsanesa wallahi.” wacce ta ke farko ce ta faɗa haka.
“Maman Sumayya kenan, ai ni dan kin ƙi yadda ne, gobe muje wajen sabon malamin nan Mai sittin goma, a kashe mana shi daga doran duniya.”
“Ba haka za mu yi ba, kinga dai yanzu mun fara ciresa a zuciyar yaran mu, kuma a hankali gidan nan zai gagaresa zama, sai dai mun kasa ciresa a cikin zuciyoyi iyayensa, kullum mukaje sa'a ce 'hakan ba zai yuhuba saboda akwai wai abu da yake gani a tare da yaron, kuma ya kasa gane menene shi, yanzu kashe Haidar ba shine mafita ba, kashe Abban Haidar shine mafita, lokacin mallakan komai ya yi Maman Safna.”
“Hana ne, kuma insha Allah da munje wajen Mai sittin goma, komai zai yi dai-dai, ance aikinsa kaman yankan wuƙa ne.”
“Kinga abu na farko, a cire mai wannan zarran in munce abu to shine dole, so muke ya dawo mana biyayya kaman uwarshi." sai suka yi shewa suna tafa hannu, gaba ɗaya su babu mai imani a cikinsu, ƙawaye tin daga makaranta, kuma basu da buri sai auren miji ɗaya mai tarin dukiya, shine wata rana suka yi arba da Mahaifin Haidar, wanda suke cema Abu Haidar. aikam daga wannan lokacin, Boka ya musu aiki, Maman Sumayya ita ya fara aure, sai Maman safna, wanda tsiransu kaɗan ne dan wata biyu ne tsakanin bikin, tin shigowarsu wannan daular suke wadaƙa da kwasan kuɗi suke tarawa, babu wacce ta shige musu gaba sai Ummin Haidar, sunyi sunyi a haukatar da ita amma hakan ya ƙi cimmawa saboda kullum cikin azkar take yi, gashi Abban Haidar yana mata wani mugun so, domin kuwa auren haɗi ne tsakanin su jinin su ɗaya. Haidar shi kaɗai ta haifa, suma yaransu ɗai ɗaya ne. Sun manyanta babu aure dan sun kai 28yrs dukka kafin suka yi aure, haka kuma daga shikan su sun haifa yara mata, daga nan kuma shuru har yanzu, yaran shekarun su 20 amma ita Safna ba ta gama haɗa wa. Suma sun taso sak halin iyayensu na maitar kuɗi, da rashin ganin Uwar gidan Abban Haidar da ƙima, yanzu haka yaran sun fara jami'a dake cikin gari, kuma suna more wa da kuɗin ubansu.
“Assalamu alaikum.” ya shiga ɗakin Ummin, sai dai babu komai a wannan parlourn sai ƙaran tv, tashar Africa tv, ɗaga kitchen ta fito, dan ita ya kanyi wiya ka ganta a babban parlour. Babbar macece mai cike da haiba da kalama, matar akwai ta da cika ido sosai, hannunta yana ɗauke ne da break, murmushi ta saki tana kallon tilon yaron na ta.
“Wassalamu Alaikum, My son ka dawo.”
“Eh Ummi, ya gida?.” ta zauna tana faɗin.
“Alhamdullah.”
“Ba dai yanzu za ki ci abincin rana ba?.” ya faɗa dan yasan halin Ummi ba ta son cin abinci gashi tana da ulcer. Ganin ta yi wani murmushin yasa ya ce.
“Haba dan Allah, Ummi me yasa, na faɗa miki banso, sau nawa ina kawo masu aiki, sai dai su dena zuwa, ni ko aikin da kike yi banso, kuma Abbana ya umarci da a dinga kawo miki abinci har nan.”
“Kai ma kasan wannan zance ne kawai, iyayenka ne za su min girki.....?.” sai ya katseta.
“A'a mai girki Zarha mana.”
“Haidar share kawai, tin da Allah ya ban lafiya bar ni, da masu aikin sun zo sai su kuresu kuma ni banshiga harkan su, ina raunin zuciya sosai abu kaɗan ke tsayamin a zuciya, haka su Sumayya ɗazu suka shigo nan karka yadda suka zage ni, ban faɗa ma ɗan ka rama min sai dai komai Lokacine.” ta faɗa tana kai bread ba kun ta, murmushi ya yi, inda ya gode Allah Ummi ba ta fita wancan parlour, kuma suma an musu iyaka da na ta parlour, sai da ya danna zuciyarsa sosai sannan ya kalla Ummi wacce kwata-kwata ba sa kama.
“Gobe wannan tafiyar.” addu'a ta mai sosai dan ta san da maganar, daga haka ya bar part ɗin, a lokacin su Maman Safna ba sa nan, part ɗin sa ne a farko dan haka can ya nufa tare da yin tunanuka barkatai........
*(Hmmmm har yanzu wasa muke yi, domin kuwa wannan littafin mai dogon zango ne, na kusa koma wa kiran sunaye dan Kano da Abuja da Kaduna ya kusa zama labari ɗaya.)
_Abubakar_
Bayan ya koma gida suka ƙara waya da Darling akan sai gobe za ta dawo, bai mu sa ba, ya kashe wayan, abincin da mai girki ya girka shi ya ci, yana ci yana ƙwaɗayin ranar da zai ga matarsa ta girka mai abinci sannan ta ba shi a baki, sam ita Darling ba ta san wani tarairaya ba sai tsabar tuhuma, yana so ya ƙara aure amma yana tsoron ya faɗa ma ta dan ba za ta yadda ba. Wayarsa ya ciro tare da shiga wannan wajen, so yake ya ɗan yi karatun *littafin sirrin Ameeratulkhair*. Bai tsaya ɓa ta lokaci ba ya shiga na gaba *MATSALA TA* .
“Toh fa, Allah ya sa yana da daɗi." Ya faɗa yana shiga.
( Yauwa bara na dasa, kafin na rubuta komai bara na ɗan rubuta labarina kaɗan, Ni ce dai da nake rubutu wato Ameeratulkhair, shekaruna 20, hmmmm matsala ɗaya tak, sume Family na, da fari sun rabani da uban na, sannan sun raba ni da iya magana, sai dai ni da Allah na dogora, ina rayuwa ne bisa yadda ya tsaɓarmin, tin Ina ƙarama na zama mai fuska biyu, domin kuwa babu wanda yasanni, ban bayya fuskata domin cikin tsoron ƴan uwan nake, gani nake kaman da sun ganni za su sanya a kashe ni, neman rai na suke kaman yaƙi, sune kawai matsala amma su jira ina nan bayya a lokacin da *BURINA* yan cika, lokacin na zama tauraruwa, zan bayya ga duniya hmmmm ina tsimayen wannan lokacin, banda mugun nufi akan su amma wallahi wallahi ban yafe ba, da sun barni da muryata amma ina me naaaa naaaaa naaaa). Ƙarshen kenan sai Emoji na kuka, tabbas yasan a lokcin kuka ta yi ita ma, shi kansa ya ji wani iri haka sai ya ce.
“Yanzu tana magana shine wasu suka mai da ta haka!?, Innalillah wa'inna ilaiyi raji'un', duniya ina za ki kaimu, yau kam sai na gama karanta dukkan wannan bara na kammala cin abinci." Ya faɗa yana ci gaba da cin abinci duk da sam girkin ba ya mai daɗi.........✍️ END.
> Tab 😳😳😳😳 ku kuma kun ƙulle kenan team ɗin Mai sittin goma, hmmm Allah ya shirya mu. Toh fa kunfara jin ɓangaren *Haidar* shima dai ba sauƙin. Hajiya Ameeratulkhair 👂 yau fa Abubakar ya ce sai ya kai ƙarshen littafin sirrinki 🤣🤣. I'm sorry gaskiya ƴan uwanki sun cuceki, sun rabaki da Magana da Mahaifin ki 😭😭. Mu dai je zuwa Guys .........HASASHE KO BURI✍️ PRETTYN JAJIRTATTU ce ✍️.
🔥 *Let’s goooo!* 🔥 Hit that LIKE 👍 if you're truly *ready for the ride*! Because *HASASHE KO BURI* isn’t just a story — *it’s an experience.* 💭✨📚
✍️ _By PRETTYN JAJIRTATTU_ 💕
💔 *_HASASHE KO BURI_* 💔
> 📖 A powerful story filled with dreams, struggles, and destiny!