HASASHE KO BURI

PAGE 2️⃣3️⃣⏩2️⃣4

by @prettys01

*ABUJA*

Cike da nishaɗi suka koma gida, har ga Allah yana ji a ransa saura kaɗan ya mallake mata huɗu, so yake ya cika sunna, abin jin daɗi, biyu an bashi dama kuma yana ji da yardan Allah komai zai ta fi yadda yake so. Part ɗin Hajja suka shiga, aikam nan sun ka ga, Aunty Aisha, gaisheta suka yi ta amsa cike da walwala, da yake ta shirya za ta wuce, aikuwa Ukasha ya sanya Driver ya kaita har gida, kuma ya ba ta maƙudan kuɗaɗe, godiya ta yi mai sosai, sannan ya dawo ciki, take Rahma da wata yarinya suka fito, kallo ɗaya Ukasha ya musu ya ɗauke kansa dan shi bai son kallan mace, yanzu ne dai da aure ya saka sa gaba.

“Yaya Umar sannu da dawo wa, Laaa Uncle Ukasha ana ganinka da ma?.” Rahma ta faɗa suna zama a gefe, da ta so Ukasha fiye da tunani, har an fara maganar aurensu, sai aka fasa da ta ji burin sa, tabbas a lokacin akwai mata uku da suke ƙasa amma ta zame kanta daga nan zance ya ruguje, cikin ikon Allah ta haɗu Abubakar wanda ya fi Ukasha komai sai dai ba lalle ya fi Ukashan kuɗi ba dan shi ma mugun mai kuɗi ne.

“Ina nan, ya Kano ɗin da Abubakar?." Ukasha ya faɗa sai ta ce.

“Alhamdulillah." Dun ƙafar ƙawarta ta ta ka, take ta buɗe baki ta ce.

“Ina wunin ku?.” suka amsa atare.

“Uncle Ukasha dama na yi ma wannan ƙawar tawa magana ne akan ka, to ta yadda ta amince, dama Yaya Umar ya ce na ta ya shi bincike, kuma an dace dan Kanuri ce." Ta faɗa da ɗan ɗar-ɗar. Ukasha kallon Umar ya yi dan ƙarin bayi, sai yaga Umar ya basar. Ƙwafa ya yi ya kalla yarinyar da ƙyau, bai ta ɓa ganinta ba sai yau, ba laifi ba mummunan ba ce, kuma dai-dai take, akwai dai dogon hanci sosai, ba ta haske sosai amma ta ƙara da bleaching.

“Ta faɗa miki komai akai na?." Ya faɗa yana karantar natsuwarta.

“Eh, kuma na amince, dan Burinka mai ƙyau ne.”

“Ma sha Allah, kai gaskiya na yi murna." Umar ya faɗa sai Ukasha ya ce.

“A ina kike da zama?, Ban ta ɓa ganin ki ba?."

“A barno iyayena suke amma ni a nan na girma wajen yayan bababmu, karatu ne ya haɗa ni da Rahma, kuma ina yawan zuwa gidan nan amma ɓantaɓa ganin ka ba.” ta faɗa harda wani ranƙwaɗa murya.

“Eh ban wani zama, ban numberki zan nema magabatanki dan jin ta bakinsu." Take suka yi exchanging number.

“Ya sunan Hajiyar?.” Ukasha ya faɗa sai ta ɗan yi murmushi sannan ta ce.

“Zuby, wato zubaida.” sai ya yi saving da haka sannan ya bar ɗakin. Yana fita Umar ya ce.

“Ke da muka yi magana a sirri, ai da sai ki min magana, yanzu ji yadda kika ɓa ta komai."

“Uhmmm ai shike nan, ƙawata zo mu shiga ciki.”

“Yamma na yi yaushe za ki wuce?.” ya kuma tamabaya ganin ko shiryawa ba ta yi ba.

“Sai gobe zan wuce, Baba nake jira.” ta faɗa tana shigewa ɗakin tare da kulle ƙofar.

“Ƙawata ya kika ganshi?.”

“Gaskiya Guy ɗin ya yi, ƙawata ina godiya.”

“Kinfi ƙarfi haka a wajena, yanzu dai da biyu na zo Abuja, dole muje wajen Mai sittin goma kafin na wuce."

“Gaskiya kam, nima ko kwalli ya ban dan na janyo hankalinsa."

“Sosai ma kuwa, ai wani bura-uban sai bayan auren, duk ki yi waje da sauran ki mallesa kaman yadda na mallake Abubakar, kinsa tin daga wancan lokaci har yau bai sake waiwayen familynsa ba, kuma suna can cikin wahala.” tafawa suka yi, dan tin da Zuby ta shigo hirar da suke yi kenan akan Ukasha, balle yanzu da Zuby ta gansa sai ta yi ya yi mata 100%.....

*KADUNA*

_Muheey_

Yau a gidan su ta wuni, ta sha faɗa sosai wajen mahaifiyarta akan rashin leƙosu da ba ta yi, dan rabon da su haɗu da Mahaifinsu ta manta.

“An ce ana ganin kina fita a motar Hajiya (Mariya), haka ne?." Mama ta faɗa tana kafe Muhibbat da idanu, haɗe fuska ta yi tana faɗin.

“Mama ashe har gulmata ake kawo miki, to dan ta a ramin menene a ciki, har mijin na ta ya sani ai."

“Hmmm ina raba ki dai, bansan wannan halin wallahi, ka tsaya in da Allah ya ajeka ya fi, amma ke tin kina ƙara akwai son rayuwar ƙarya, gidan nan dai babu abin da muka rasa amma ke sam mafiyinsa kike so."

“Mama dan Allah ya ba ka bashi kenan ba ka nema ƙari da mafiyinsa." Ta faɗa tana miƙa wa, ɗakinsu ta koma, a lokacin duk ƙanenta na Islamiyya, dama ita ta yi sauka, to ci gaban ne ya gagara.

*Merry*

Kamar yadda ta yi tsammani sai da Abbas ya dawo mata da wannan kuɗin, murmushi ta yi dan ganin alert ɗin sannan ta yi accepting kiran da yake mata.

“Babyna me yasa in na maka alheri kake dawomin da shi?.” ta faɗa tana zama kan fridge dan shigarta kitchen kenan.

“Malamata kenan, ni ya dace na miki ba ke ba, yanzu dai ba wannan ba, kinci abinci kuwa?."

“Gani a Kitchen dai, zan haɗa custard ne."

“To shike nan, haɗa zan ta ya ki sha.” murmushi ta yi sannan ta sauka, kashe wayan ta yi sai bayan da ta gama haɗawa sannan ta koma room ɗin ta, video call ta kirasa, duk da ɗakin nasu da haske amma ya yi dishi-shishi dan haka ya koma waje dan ya fi haske, hira suka sha sosai. Ita dai tana zaune ne kan babban gadonta, ɗakin komai pink colour ne dan shine favourite ɗin ta.

“Ustaz ɗina, yanzu da mun kammala karatu sai ka bar ƙasar nan! Gaskiya banso.” sai ya yi murmushi.

“Aikin ba tabbas domin wani Alhaji ne ya yi mana alƙawari, balle ni a gaskiya na fasa zuwa, insha Allah zuwa lokacin aikin hannuna ya yi ƙwari kuma ina samu, zai fimin da barin county.”

“Haka ne, domin a can ɗin bakusan wani aiki za ku yi ba."

“Aikin company ne."

“Okh, ni da kana son aikin soja dana neman maka."

“Soja a'a, nafison aikin hannu, amma Malamata in shi ɗin nasamu zanyi.."

“Zan ma hanya."

“Na gode, ki barshi kawa.”

“Baka so na ko kaɗan, komai na ce kai bai maka ba, shike nan sai da safe." Kafin ya ce komai ta kashe kiran, take yi offline, kiran wayan ya yi _witch up_ sai ya yi murmushi sannna ya koma cikin ɗakin na su.

“Ɗan soyaya an gama ƙonewar kenan?.” Shamo ya faɗa da sigar tsokana.

“Na lura kaf cikin mu babu wanda ya kai Abbas iya soyayya, mu na mu duk wasan yara ne."

“In na fika (I.B) iya soyayya ai sai an bugani a jarida, ni Bara na matso mu yi sirri, dan kuwa ina so ka ƙara koyamin kalamai sosai, na lura Ma'esh sai da haka." Abdul ya kai maganar yana dariya, sai a lokacin Abbas ya ɗan dafa kafaɗar Abdul yana faɗin.

“Hmmm Allah ya shirye ku, yauwa shamo ya maganar mu ne?." Sai Shamo ya ce.

“Don't worry mutumina, zamu ja maka attendance."

“Gobe hala akwai aiki sosai ne a gareji?.”

“Eh Abdul, akwai motar da za mu kai Kano, da asuba zan fita." Hira suka sha kamar kullum, wani suyi dariya wani kuwa su yi hayani akai, haka har suka yi barci.......✍️ END.

> Hmmmmm na yi shuru kawai.

🔥 *Let’s goooo!* 🔥 Hit that LIKE 👍 if you're truly *ready for the ride*! Because *HASASHE KO BURI* isn’t just a story — *it’s an experience.* 💭✨📚

✍️ _By PRETTYN JAJIRTATTU_ 💕

💔 *_HASASHE KO BURI_* 💔

> 📖 A powerful story filled with dreams, struggles, and destiny!