PAGE2️⃣7️⃣⏩2️⃣8
by @prettys01
*KADUNA*
_Abbas_
Abbas da ogansu suka nufi Kano dan kai wata mota, tin asuba suka fita saboda mai motar na jira, dan Alhajin ya shigo Kaduna ne motar ta samu matsala, sun isa da wuri dan kuwa motar lafiyayya ce sosai. Da isarsu gidan Alhajin, aka umarci su jira yana zuwa, a dai-dai lokacin Haidar ya fito daga part ɗin sa cikin shigar manyan kaya ya yi ƙyau sosai, sannan ya ɗauko trolley wanda ya zuba abubuwan da zai buƙata. Har ƙasa suka gaishe da Haidar sai ya yi murmushi yana dafa su da faɗin.
“Injin miya (Haka yake kiran Ogan Abbas) ban so, ko Abbana bason wannan gaisauwar yake ba, ya Kaduna?”
“Alhamdullilah.”
“Sir good Morning." Abbas ya faɗa sai Haidar ya miƙa mai hannu suka gaisa.
“Morning, kai ma Injin miya ne koh?.” sai ya yi murmushi ya ce.
“Eh muna ta ɓa wa.”
“Allah ya ƙara jagora, bara na shiga zan fito da Abbana ɗin.” daga haka ya yi ciki, su kuma suka bishi da idanu.
“Kasan waye me wannan gidan?.” Ogan Abbas ya faɗa.
“A'a Oga.”
“Kasan H - Halal Nigeria Motors?.”
“Oga waye bai san wannan Company ba, ai yawancin daga can ake kawo mana kayan aiki.”
“Haka ne, to wanda muka zo wajensa shine mai wajen, wannan kuma da ya wuce shine babban ɗan sa, kuma ma'anar H- Haidar Halal Motors.” zaro idanunwa ya yi, yana ƙare ma gidan kallo, tabbas tin shogowanshi ya san mai gidan nan ya tara sosai, dan motocin dake gidan baya iya ƙirgawa.
“Ashe yau zanga wannan Attajirin."
“Aikuwa, shi yasa na tawo da kai, na aminta da kai sosai, kuma na yadda da kai, shi Alhajin yana neman na turo mai yaron aiki na guda 1 tak, amma bansan dalili ba, sai dai kai na za ɓa, duk da ba komai ka iya ba, amma hazaƙanka ya na min sosai.”
“Ogaaaaa na gode.” Abbas ya faɗa yana rungume Ogan sa.
“Kai sake ni, ka bari ya fito dai, tare zamu koma sai bayan wata biyu zaka dawo domin zuwa lokacin ka kammala karatun ka.”
“Haka ne, dan yanzu shirye-shiryen exam muke yi." Tare suka fito suna tafiya a tare cike da nishaɗi, yadda kasan wasu abokai, haka suka jero har wajensu.
“Ina kwana Alhaji.” suka haɗa baki wajen gaisasa, da murmushi ya amsa.
“Har kun kawo kenan, da yake wani zan ba mota kuma yau yake so, shi yasa na ta doku."
“Allah sarki, yanzu dai mota ta gyaru sosai.”
“Yauwa haka ake so, ina ɗayan maganar na mu?.”
“Alhaji gashi nan, sunnan sa Abbas."
“Haidar ga wanda na maka.” Haidar ya saki murmushi yana kallon Abbas sai ya ce.
“Masha Allah kaman kasan ina so na ƙara maka magana.”
“Ya yi maka?.”
“Eh, Abba tunda Injin miya ne ya kawosa na amince, amma sai nan da wata uku zuwa lokacin mun kammala wannan aikin har result ya fito, amma kafin nan ya fara zuwa dan sanin komai kafin na zo."
“Alhaji dama shima yana so ya kammala karatunsa gashi shirin exam suke yi ma.”
“Ma sha Allah, ai hakan ya yi, da ka kammala kawai ya zo nan.” godiya suka mai sosai.
“Abbana sai na dawo.” Haidar ya faɗa yana raba hannuwansu.
“Da kun isa ka tabbatar ka kira ni.”
“Insha Allah, Abokina zo muyi wata magana mana.” daga haka ya ja hannun Abbas, tare suka jera har gaban wata arniyar mota wanda ya shiga cikin ya ajiye abubuwan hannunsa sannan ya ce.
“Za mu yi magana, dan Allah ka riƙe amana, domin kuwa ni ba wani zama zan dinga yi ba, ina yin wasu ayyukan, amma karka damu zan ki raka, number ya yi?.” ya miƙa mai wayansa yana faɗin.
“Eh Sir, sai na jika, Na gode sosai.” murmushi Haidar ya yi yana faɗin.
“Injin miya zai baka saƙo." Daga haka ya tada motar yana fita.
Murmushi ne kwance a kan fuskarsa ya iso wajensu Alhaji.
“To muje."
“Injin miya ai ƙwayi breakfast, mu shiga ciki." Hmmmm ai ba'a magana kawai, Ogan Abbas da Abbas sai bin ko ina suke yi da kallo, dan gidan ba magana, a parlour suka zauna.
“Maman Safna, a haɗa musu breakfast, wai har kin shirya ne?.” Maman Safna da take sanye da hijab har ƙasa ta faɗaɗa murmushi tana faɗin.
“Eh Abban Haidar, muna so mu dawo da wuri ne."
“Okay, karku daɗe, kuma kuja ma Driver ku ja mai kunne ya bi da ku a hankali.”
“To Abban Haidar."
“Ku bi Flight kawai, zan miki transfer.”
“To muna godiya, daga haka ya yi part ɗin Ummin Haidar, wani harara ta dalla mai, dan kuwa duk buru-uba yau sai sun shiga tsakanin su.
Abinci masu rai da lafiya Zahra mai girki ta haɗa musu, aikam suka ja daɗi, bayan sun gama Alhaji ya basu dubu hamsin ladan aiki, sannan ya biya su kuɗin aiki. Aikam sun mai godiya sosai.
“Abbas sai mun ganka."
“Insha Allah.” a dai-dai lokacin ƴam mata biyu suka fito suna ta ranƙwaɗa, gaishe da Abban Haidar suka yi, sannan har sun ɗaga ƙafa sai Abban Haidar ya ce.
“Ni kaɗai kuka gani?.” da sauri suka gaida sauran, sai dai me da sauri Sumayya ta kuma kallon Abbas tana faɗin.
“A....A...Ab...Abbas.” ba shi kaɗai ba dukkansu suka kalleta, dan yadda ta kira sunan nasa.
“Abbas ni ce fa Sumayya Abu Haidar." (haka sunan su yake har a school, komai Abu Haidar ko Abban Haidar, shi yasa suka tsanar Haidar sosai).
“Bangane ki ba.” Abbas ya faɗa yana mamakin a in da ta sanshi.
“Yanzu school za ni, ban numberka za mu yi magana." Ganin kamar ba ta san Abban Haidar na wajen ba, yasa ya koma ciki, sam bai son ɗaga musu murya dan kanshi yana sarawa in ya yi hakan. Yana wucewa Ogan Abbas shi ya ba ta number sanann suka wuce.
“Ai da ba ka ba ta ba, sam ba ta da ɗa'a."
“A'a fa, kasan ko hakan wani alkairi ne." Suka ci gaba da hira har suka fita a babban haraban gidan.
Tana shiga mota ta rungume Safna tana faɗin. “Finally na samu number Abbas."
“A Ina kika san shi?."
“Hmmmm a facebook, guy ɗin ya min, ke in kika bibiye page na shi ko, za ki kwasa ilimi, ɗan boko ne sosai, ina yawan ganin videos na shi yawanci friends dinsa ke daura, ke kinji speech, hmmm su 4 ne gaba ɗaya Poly na Kaduna ke ji da su.”
“Okay amma dai ba sonsa kike ba?.”
“Kina wasa ne, ai ni na haukace a soyayyar Abbas."
“Kina ruwa kinsan dai Mom ba za ta yadda ba." Ta figa motar tana wani sakin murmushi.
“Ni dai na gani kuma ya min.” girgiza kai kawai Safna ta yi dan tasan hauka kawai Sumayya ke yi............✍️
> Hmmmmm 🤐 yanzu wasan zai fara kun faji wata sabuwa Sumayya ƙanwar Haidar da son Abbas, gefe guda ga Merry ♥️, hmmm haɗin biza kenan....✍️
FREE PAGE'S ya kusa ƙare wa, ai munyi da waya, akwai point ɗin da nake so ku kai ne..... PRETTYN JAJIRTATTU ce ✍️.
💔 *_HASASHE KO BURI_* 💔
> 📖 A powerful story filled with dreams, struggles, and destiny!