HASASHE KO BURI

PAGE 3️⃣1️⃣⏩3️⃣2

by @prettys01

*KADUNA*

Su biyar ne a zaune a cikin ɗakinsu, Alhajin dake sanye da babban riga ya kuma yin murmushi sannan ya ce.

“Zuwa jibi zasu wuce, na so ace da ku a ciki, amma ku kammala karatun sai ku bisu, kar ku yi wasa da aikin nan domin sai an biya makuɗan kuɗi ake samu, amma saboda ina son taiamaka ku ne, farashin kaɗan na nema, gashi ana samu fiye da tina.” ya kai maganar yana ɗaukar pure water sannan ya kai bakinsa.

“Alhaji, insha Allah da mun gama zamu yi maka magana, gaskiya muna godiya.” faɗin Shamo sai I.B shima ya ce.

“Haka ne Alhaji, muma muna buƙatar wannan aiki.” sai ya duba wayansa alert ne da 800k ya shigo daga Mymoon.

“Zan biya mana kuɗin jirgin in lokaci ya yi." I.B ya kuma faɗa sai Alhajin ya ce.

“Shike nan.....”

“Gaskiya ni na fasa, saboda na samu wani aikin hannu kuma ya min sosai, dan kuwa nan da two month zan koma aikin a Abuja ƙarƙashin Company H - Halal Nigeria Motors.” Da mamaki suke kalla Abbas, sai ya ɗaga musu kai alaman tabbatarwa.

“Mene? Wai ba za ka U.S ba? Akan me Abbas?."

“Kawai dai Abdul.” yana faɗin haka ya yi waje.

“Aiki ne ai ba dole ba ne, akwai masu so zan musu magana, ku dai shirya.” daga haka Alhajin ya yi waje. Shuru ya ratsa ɗakin.

“Meyasa Abbas yake son tarwatsa mune?." Sai ga Abbas ya shigo.

“Abbas ya wuce su ɗauke ka a mai wanke mota, ni dai gaskiya ban yadda ba da kai zamu.” sai Abbas ya yi murmushi sannan ya dafa kafaɗar Shamo ya ce.

“Karka damu mutumina, muna tare har abada, kawai zan ci gaba da aikin hannuna kawai.” haka suka jima suna bashi baki amma ina ya kafe sosai. Daga haka suka bar maganar.

Haka dai rayuwa ta ɗan fara gangarawa suna shirin exam, Mymoon na ta narka ma I.B kuɗi masu yawa har sun siya filaye huɗu duk da sunansa sannan a cikin ɓakin ta zuba kuɗaɗen kaman yaƙi.

“Mymoon, ina kike kai kuɗi ne, kashe kuɗin ya yi waya." Dad ya faɗa yana kallon Mymoon da ta haɗe rai.

“Dad, bansan ya kake so na yi ba, shike nan na dena ta ɓa komai a ciki shike nan.”

“Ni bance, domin kuwa duk dukiyata na kune ke da Taj......” sai ta miƙe.

“Dad wani Taj ɗin?, Ta ya kuɗin ka ya zama na sa, ohhhh na gane.” daga haka ta bar Dining ɗin, girgiza kai ya yi yana kallon Mom da ke cin arish ya ce.

“Yarinyar nan duk ta sauya, bansan me ya shiga kanta ba sam, kallona take tana mai faɗa min magana.”

“To Ni Dad me zance, ba ka son Ina mata faɗa, ga kuma lokacin yin faɗan ya yi amma ba ka saba ma ta ba." Sai suka yi shuru.

“Hmmm duk me ke kanta zan sauke ma shi, Taj zan kira ya shigo ƙasar nan domin aurensu, in na mata auren sai na ga ƙaryan tsiya.” murmushi Mom ta yi tana faɗin.

“Ban shiga tsakanin ku, zan iya jin kunya nan gaba.” sai shima ya yi murmushi.

*** Dariya ta yi sosai dan jin abin da Abdul ya ce.

“Kai Honey, yanzu dai mubar wannan zancen, nawa ne kuɗin da kake buƙata.”

“Uhmmm 500k ne haka.”

“Shike nan karka damu, zuwa gobe za ka ji saƙon.” sai ta miƙe daga kan gadonta tana kuma cewa.

“Zan yi ma Uncle magana, yanzu dai da mun kammala exam sai tafiya.” hira suka sha sosai sannan ta kashe wayan.

*KANO*

_Haidar_ Yana isa haraban gidan tv na GOODNESS TV, ya riske mutane duk sun shirya, har Bus ɗin ɗaukarsu ta iso. Hatta Ameeratulkhair an ba ta I.d card, daga in da yake ya ke karantar natsuwarta, a takure take sosai dan ta kasa sakin jiki, kamar dai kullum irin wannan shigar ta yi. Sun jima sai Haidar ya kira Sir Abubakar, jin abin da ya ce aikam ya ce.

“Duk mu tafi, C.E.O ba zai shigo da wuri ba.” da mamakin take kallon mutanen dake shiga dan a ƙalla sun kai kusan 15 haka. Sai ta saki ranta dan ta za ci ita da Haidar kawai za su.

A layin na uku ta zauna sannan mota ta hau titi, take Haidar ya dawo kusa da ita yana faɗin.

“Fatan ban takura ki ba?.” sai ta ɗaya mai kai, zaman sa ya gyara sannan ya ciro wayansa yana ɗan latsawa, sun ɗan jima a haka kafin ya ce.

“Ameeratulkhair, gaskiya kina burge ni sosai, jiya na soma ganinki amma kin shiga raina, ban ta ɓa soyaya kuma bansan yadda ake yi ba amma akan ki na ji wani abu na daban haka." Ya kai maganar cikin sanyin murya, ita kuwa murmushi kawai take saki, a karo na farko wani yace yana son ta ba tare da yasan wacece ba.

“Naso ace a yanzu muna magana da ke sai sai babu dama, sanya min numberki sai mu yi chat, Please." Ba musu ta sanya mai number sannan suka hau online suka fara chat.

“Na miki?.” sai ta tura mai Emoji na thinking, can sai ta rubuta 'No' shuru ya yi sannna ya yi typing.

“Why?.”

“Ka fiye surutu.”

“Na dena.” sai ta yi murmushi sannan ta ce.

“Zan yi tinani to.” kaman sun san juna haka dinga shan hira sosai, dujuka huɗu za su wanda duk an tsara tafiyan na su.

“Na ji daɗi na ga muna da yawa, mu 15." Sai ya mata reply.

“Eh, kinsan aikin babbane shi yasa, kuma kowa da aikinsa, kinsan dai naki.”

“Ɗaukan rahoto, rubuce-rubuce."

“Eh ni kuma photo.” ba ta san lokacin da ta sake da shi ba, sai faman hira suke yi sosai, sai wajen yamma suka isa wani daji, gaba da baya bishiyoyi ne sosai, haka kuma wajen akwai ƙyau sosai. Kafa runfuna suka yi, dan harda masu gadi suka zo, su uku ne masu aiki, Haidar mai ɗukan hoto, Ameeratulkhair mai rubuce-rubuce sai wani mai jawabi, sauran daga masu girki sai masu gadi.

Huta suka kunna a tsakiya , anan duk suka yi alwala sannan suka yi salla cikin jam'i, gaba ɗaya a hau hira cikin nishaɗi, ko wa zafi yake ji amma banda Ameeratulkhair dan ko niyyar cire nikaf ba ta da shi sam. Duk sun ci abinci amma banda ita ta dai ajiye agefenta, kuma tana da ga nesa da su.

“Barka." Haidar ya faɗa yana zama tare da kai goran faro bakinsa.

“Ba ƙyajin yunwa ne?.” sai ta girgiza.

“To ki ci mana.” ta kuma kaɗa kai kaman ƙaɗangare.

”Tashi na rakaki cikin can sai ki ci.” ba musu ta bi bayansa har zuwa ɗaya daga cikin rumfan nasu, zama ta yi a ciki shi kuma ya zauna a waje, ya fahimci ba ta so a ga fuskarta ne.

“Aganinka ya za ta kasance? Ƙyaƙƙyawa ko mummunan? Fara ko baƙa?." Zuciyarsa ta tambayesa. Sai ya yi saurin faɗin.

“Koma ya take Ni kam zuciyata ta ya ba gaskiya.......” END. > Hmmmm masu tafiya U.S Allah ya sa aikin yadda kuke tsammani ne. Amma I.B kana bura uba, sai kace tsafi kabi sai jidan kuɗin Mymoon kake🙄🙄🙄.

> Finally dai Dad ya ce Taj zai dawo..... Ko Mymoon za ta iya rabuwa da I.B oho, kuma ga dukkan alamu ba ta don Taj.....

> Hmmm Soyayya ruwan zuma, Haidar ka rufta amma ka ji daɗi dan ta na biye maka, karfa amanta da Abubakar tab......😳🥱🥱🥱

💔 *_HASASHE KO BURI_* 💔

> 📖 A powerful story filled with dreams, struggles, and destiny!