Page 3️⃣3️⃣⏩3️⃣4
by @prettys01
*KANO*
Kamar kullum wayarta ce ƙiran techno ce a hannunta tana junjuyawa, da sauri ta kuma juya miyar dake kan gas, wayar ta kalla tana faɗin.
“Ko sai yaushe zan cire rai da kiran wannan mutumin oho, na ma kai na alƙawarin in dai ya kirani, to na mallaka mai zuciyata na har abada.” kallon wacce ta shigo Kitchen ta yi.
“Zahra, ba ki ga min miyan ba?.”
“Aunty Safna yanzu zan gama." Daga haka Safna ta yi waje, a zuciya ta ja tsaki, dan tana zamanta wai Safna ba za ta ci abin da aka dafa fa sai taliya da miya shine yake yi. Tana gamawa ta kai mata kan dining sannan ta nufa wani ɗan ɗaki dake gefen kitchen, a nan take kwana. Shiga ta yi tana mai hayewa kan babban katifar ɗakin dan sabuwa ce fil. Tabbas ta gaji da rayuwar wannan gidan amma in ba ta yi ba ya za ta yi, dole ce ga kawo ta aikatau wannan gidan mai hargitsi, tasan komai da ake yi a cikin gidan har da abubuwan da matan gidan ke ƙullawa akan Ummin Haidar, ko da tana aikine sai wani sanadi ya kaita in da za ta ji sirrinsu..
A parlour kuwa, Safna ke cin abincin tana latsa waya da hannu ɗaya, sai Sumayya dake kallo a I.G (Instagram).
“Kalla Abbas, ji karatun da yake yi, lokacin da suka kammala ND1.” Safna ta kalla ba ƙyarya magana Abbas yake a video kaman wani bature, sannan Abbas yana da kyau da cikan haiba. A kan stage yake yana koro zance.
“Gaskiya Guy ɗin ya haɗu, amma ina rabaki da su Mom.”
“Karki damu, banda case da su." Ci gaba da cin taliyar ta yi hankali kwance. A fusge Sumayya da Safna suna ya yi, duba da hasken fatansu, mai haske ne ba can ba, sannan kusan tsayinsu tsaya, a na dai ganinsu anga jini ɗaya.
“Yanzu sai mu jira dawowan shi, musan yadda za mu yi ya ci abinci da wannan garin." sai ta mai da garin ciki jakka.
“Maman Safna yau Abban Haidar na wajenki, zuwa anjima sai ki goga a in da Mai sittin goma ya ce.” ta amsa ɗan ƙwalba mai ɗauke da ruwa kalan blue. Ya ce ta shafa a wiyarta, ƙasanta, da ƙasan brest ɗinta. Tina wa ta yi da abin da ya ce.
“Dole Ummin Haidar ta fuskanci tsana daga wajen Abban Haidar in dai ku biyu kuka yi aiki da su, sannan shi Haidar ɗin da ya ci abinci sau uku da garin nan shike nan, za ku juyasa yadda ya muku, sannan ku yi wasa da dukiyar Alhaji.” ajiyan zuciya ta sauke....
*ABUJA*
_Ukasha_ Ya rasa ina zai sanya kansa dan farin ciki, Ashake yoruba familynta sun amince, haka na Fillo Fulani ance a tsaida lokaci, sannan jiya yaje Borno nan ma alhamdulillah ya samu tarba mai ƙyau, dan nan ma ance a tsaida bikinsu da na Zuby Kunuri, ji yake kaman ya sha ruwa a ƙasa, yanzu haka kuma an bashi wata Maryam Bahaushiya, bai ganta ha amma shi kam ya amince, tinda wani amintaccen sa ne a wajen aiki ya bashi ita. Anan ba maganar ɓa ta lokacin dan an bashi, farin ciki kawai yake yi, take kuma ya yi ma Umar ƙyautan sabon gida, Umar godiya ya yi ba tare da ya yi zumuɗi ba.
“Umaruna menene?.” Ukasha ya faɗa tana kashe system ɗin sa.
“Aboki, da matsala, gaskiya banjin daɗin yadda kake neman aure haka, ba soyayya ba shaƙuwa, sannan kai aure kawai ba zaɓin Allah, sam banjin kana Allah ya ba ka ta gari.” sai ya dafa Umar.
“Wallahi duk sallar dare, sai na roƙa mace ta gari, mai ibada da sanin ya kamata. Shi yasa na ce inason mai addini, domin kuwa kishinsu ba zai huce yadda addini ya tsara ba.”
“Haka ne, Allah ya kaimu wannan lokacin?.”
“Ameen, hmmm akwai abu fa, ban wayarka.” ba musu ya ba Ukasha, contact ya shiga, sai ya karanto number ya na faɗin.
“Shine ko?.” Kai Umar ya ɗaga mai, sai yaga Ukasha na murmushi.
“Da ace washegarin ranar ka faɗa min, to da yanzu kun haifa min yaro, amma ka wani ɓoye min, toh wannna number ne abu mai sauƙi ne dab ba sai na yi amfani da system ba, yarinyar akwai basira tasan cewa number ta da cire za ka iya samu domin Code ta cire, kuma na Mtn ne, dan haka number biyu zan baka ka kira a ciki dole a samu ɗaya, bayan 070, sanan 3 ko 6.” ba musu Umar ya fara sanya 6, sai dai number ba ta aiki, sai ya sanya 3 amma ya kira har sau huɗu ba'a ɗauka ba.
“Karka damu, a ciki tabbas akwai, ni yanzu so na ke na leƙa Zuby dan mu gaisa.”
“Okh, hope ka kammala fitar da taswiran asibitin."
“Eh, yanzu zan turo maka ta Email, ka ƙarasa komai sai ka kira mutumin.” daga haka Ukasha ya ɗauki car key yana barin office ɗin. Company biyu garesa ɗaya _ARCHITECT / CIVIL ENGINEERING SERVICES._ Sai kuma _REAL ESTATE DEVOLOPER. Yana Gina gidaje, offices, estate da haya da siyarwa, yana samun kuɗi ba ƙarya.....
Gaisawa suka yi cikin sakin fuskarka, ita dai Zuby akwai ta da fara'a sosai.
“Ba ki ji sosai?.”
“Eh bawani can ba amma na iya.”
“To yi mana inji.” sai ta ɗan jingina da motarsa tana ce wa.
“Sunana Zuby, Ni Kanuri ce, kuma ina alfahari da yaren na, akwai mu da tsafta, ga ƙamshi, uhmmm kuma muna da tsafta sosai. (Inji Zuby, In Kanuri mana, kuma inji togo na, wa so gaji, wa lahi, uhmmm wa so tsatfa sosai.) Sai ya yi dariya.
“Eh kaɗan-kaɗan dai haka, (E, kaɗan kaɗan, dewa wo.).”
“Yaren akwai daɗi, bara na gudu sai zuwa wani lokacin.” Daga haka suka yi sallama yana barin wajen, murmushi ta saki dan sun haɗe idanu kuma ta sanya wannan kwallin.
*KADUNA* Yau ma wani filin suka ƙara siya, ko bayan da suka koma ciki school, suka riski har an gama lecture, dan haka suka zauna suna hira.
_Shamo da Muheey_
“Yanzu ni da so samu ne, a ɗaura mana aure, da munje in aikin ya kama ƙasa sai ku biyo mu.” ya faɗa da sigan jan hankali, sai ta yi wani murmushin.
“Why not! Ai hakan ya yi sosai.” ta faɗa tana imagine ganinta a jirgi.
_Maryam_
Ita kaɗai ce zaune akan a sit ɗin ta, yau ma Abbas yana je gareji, murmushi ne yalwaccen akan fuskarta, dan baya gajiya da mata ƙyauta ko ya ye, kuma hakan na faranta mata rai sosai, yanzu haka kati ya sama mata na 1k, shine ta ke jin daɗi. Lumshe idanunta ta yi dan jiya ta ji daɗin labarin da ya zo mata na aiki a Abuja, ita ya fiye mata barin ƙasa sau dubu....
_Abbas_
Kamar kullum sanye yake da kayan aikin sa, hannusa duk ya ɓa ci da ɓaƙin mai, dan yanzu ya fito daga ƙasan wata mota, sai ya shiga dan kwada aikin ya yi. Aikam motar ta tashi, sai da zagaye garejin sannan ya dawo.
“Oga komai normal.” sai Ogan ya jinjina kai dan akwai wani spaner da ya riƙe da baki dan shima ƙarƙashin wani motan zai shiga. Sauke ajiyan zuciya ya yi dan wannan motar ta hawalar da shi sosai, amma gashi ta tashi. Bayan Ogan ya gaji ya fito dan motar ta ƙi yin yadda yake so, Abbas ne ya shiga take motar ta tashi, aikam Ogan ya dinga sa mai albarka, yanzu kusan Abbas an yayesa dan abu ɗaya daya gani shike nan, sai ma in ya yi yafi na wanda ya koya mai. Bayan sun yi sallar Azahar suka zauna cin abinci, bread da Pepsi mai sanyi suka siya, suna ci suna korawa, sannan ana hira........... END.
> Kuna tinanin me nake tinani kuwa..... Anya ba Zahra mai girkin gidan su Haidar ita ce wacce Umar ke na ma ba, mu je zuwa.....
> Ukasha an kusa dai, Ni ma dai bara na kuma faɗin maganar Umar, Allah ya kai mu dai...ameen.
🔥 *Let’s goooo!* 🔥 Hit that LIKE 👍 if you're truly *ready for the ride*! Because *HASASHE KO BURI* isn’t just a story — *it’s an experience.* 💭✨📚
✍️ _By PRETTYN JAJIRTATTU_ 💕📖
[9/14, 08:00] PRETTY SK NOVERLIST: ***
❤️ _I love you deeply, Habibah. Always and forever._
Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥 *Keep shining, JAW family!* *** 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_
🌟🔥 *HASASHE KO BURI* 🔥🌟
*📖 A powerful story filled with dreams, struggles, and destiny!*
💡 *Ka shirya?* Wannan ba labari bane na wasa — *it’s a journey into the heart of dreams and reality!* 😍