PAGE 3️⃣5️⃣⏩3️⃣6
by @prettys01
_KANO_
A kwance ta riske Abubakar a kan carpect, sai ta fita masu shara ta kira, wasu matasa, Usman mai shara, Nuhu mai cefane da Adam mai girki. Su suka kama shi suka mai da shi kan kadon.
“Adam me aka girka ne?.” Adam da ba zai wuce sa'arta ba ya ce.
“Madam, Doya da ƙwai.”
“Okh, Nuhu zan tura ma kuɗi kaje kasuwa dan yin siyayya, daya dawo Adam ka min dambu.”
“To Madam.” suka amsa tare sannan suka yi waje. Sai ta koma ɗakin, ruwa ta samu ta yayyafa mai amma bai farka ba, sai dai barci mai nauyi ya ɗauke sa.
“Ka yi wani tunanin da ya motsa aljanun da Mai sittin goma ya aiko kenan, dole haka ya same ka, na ce ka dena ta kura wa kanka da sanin kai waye amma ka ƙi ji, shike nan.” daga haka ta nufi part ɗin ta..........
_Washegari_
A ranar suka fara aiki, kuma cikin ikon Allah a waje ɗaya sun samu abubuwa masu yawa. Komai Ameeratulkhair ta gani sai ta rubuta, shi kuma Haidar ya ɗauka, haka dai suka wuni, shi har mamaki yake dan da handglobe take rubutu, a ransa ya ce 'Ameeratulkhairi, ko hannu ba a so mu gani kenan hmmmmm.'
A wani wajen suka kuma kafa tantina, sai dai Ameeratulkhair ta fara gajiya da kayan jikin ta domin kuwa, hijab ne four yeard, sannan ta sanya atamfa doguwar riga a ciki, gaba ɗaya iska ba ya ratsa da kuma niƙaf ɗin ɗaurin cikin hijabi ta yi, ga safa hannu da ƙafa. Shuru ta yi tana mai kallon yadda kowa ke raha daga gefe can, wayarta ta ɗauka sannan ta tura ma Haidar saƙo, dan a iya wunin yau sun wani shaƙu sosai.
“I need your help." Shi ya gani ta tura mai, sai ya miƙe ya isa wajenta.
“Khair, meke faruwa ne?.” sai ta yi mai alamana da ya zauna, zama ya yi, sai ta kuma mai typing.
“Sai zuwa gobe ne zamu isa masauƙin koh?.”
“Eh.” ta kallesa.
“Gaskiya ba zan iya tsallake yau banyi wanka ba.” sai ya yi murmushi.
“Dole sai dai gobe, Ni kaina haƙuri na yi, dan na iya wanka kaman ƙwaɗo.” ta tura mai Emoji na dariya, sai kuma na damuwa.
“Menene, Gimbiya ta.”
“Mamamki nake yi, kai baka sanni ba, ba kasan ya nake ba amma wai kana sona.”
“Zuciyata ta gani kuma ta yaba ne.”
“Zaka iya min alfarma ɗaya dan Allah.” sai ya ɗaga mata kai yana kallonta, so yake ko ƙwayan idanunta ya gani, amma babu dama. Jin saƙo ya shigo ya kalla wayan.
“Minti 30 nake so na yi a cikin nan, dan Allah kar wani ya zo, ina son na sauya tufafi kuma na ɗan sha iska."
“Yadda kika ce, zan miki gadi, a huta lafiya.” ya faɗa yana barinta a wajen. Zip ta zuge na Tintin ɗin sannan ta buɗe na sama yadda iska zai dinga shiga. Hijab ta fara cirewa sannan niƙafa da safa hannu. Lumshe idanunta ta yi tana ɗan kwanciya akan ƙaramin tabarma mai kama da katifa. Fuskar fayau take, haka kuma gashin idanunta sun kwanta sosai baƙaƙe dogaye, yadda kasan dai wata balarabiya, akwai ƙyau fiye da misali, sai ma da ta miƙe, hmmmm mace iya mace mai cikar halitta, akwai jiki dai-dai, sannan Allah ya ba ta dukiyar Fulani masu cika da ɗaukan idanu, doguwar rigar ta cire sannan ta sanya wasu riga da wando marasa nauyi, haka ma hijab ɗin ta sanya mai saukin nauyi, sai ta zauna, ta jima a haka kafin ta kuma rufe fuskarta ta sanya safar ƙafa da hannu, fitowa ta yi ta nufesu dan yanzu tana jin iska sosai.
“Sir Haidar, wannan matar aure ce ko?.” wani ya faɗa yana kallon Ameeratulkhair take nufi su.
“A'a amma soon zan yi wuff da ita.”
“Gaskiya ka yi sa'a akwia kamun kai.”
“Haka ne, iya su sun wadata zuciyata akan ta.” ya faɗa yana kallon taba zama kusa da masu yin girki, hannu kawai ta ɗan ɗaga musu.........
_Abubkar_
Cikin dare ya farka da sunan Allah, kallon kansa yake da mugun tsoro dan yadda jikinsa ya jiƙe da zufa, da ƙyar ya watsa ruwa sannan ya fito sallolin dare da ya manta rabon da ya yi shi ya raye daren dashi, daga nan ya dasa karatun Alqur'ani har asuba ta yi, wani iska ne ya ji na daban na shiga jikinsa.
Misalin 7:30am na safe ya bar gidan lokacin ko Daling ba ta farka ba, abubuwa da ya ne ke masa mugun yawo a cikin kansa. Haka dai ya kusan wuni babu abin da ya iya yi a gidan Tvn. Files ne ya shiga dubawa bayan ya ga wanda yake so ya duba sannan ya yi waje tare da nufin wani address da ya bincika, ya sha wuya sosai kafin ya gane gidan domin bai taɓa zuwa unguwar ba, ya ɗan ƙarasa yana kwankwaso kofar gidan, anjima sosai kafin aka buɗe gani namiji tsaye yasa ta tsaya tana kallonsa da mamaki, sai ya gaisheta yana cewa.
“Na zo gurin mahaifiyar Ameeratulkhair ne, dan Allah tana nan.” sai ta ƙara jigun take ta ɗan saki fuska sanan ta mai iso bayan ta sanarwa mahaifiyar Ameeratulkhair ɗin.
A falo ya zauna, ƙanwar Adda ta ɗibo mishi ruwa, bai sha ba sai ya kuma ƙara gaishe da su cikin girmamawa, suka amsa sai Adda ta ce.
“Th bawan Allah daga ina? Me yasa kake nemana ta fatan dai lafiya.” sai ya fadyada murmushin sa yana faɗin.
“Sunana Abubakar ni ne mai gidan tv godness tv inda ƴar ki ta fara aiki jiya........” da sauyi ƙanwar Adda mau suna Aunty Saratu ta ce.
”Innaliillahi me ya sami Amiran? fatan tana lafiya?.” ta faɗa da sauri sai ya ce.
“Alhamdulillah, ni bama wannan ne ya kawo ni ba don tuntuni suka tafi, kuma munyi waya ma, kusan sun yi rabin tafiyar.” Sai Adda ta ce.
“Hmmm to me ya faru?.’
“Gaskiya Mama ba zan ɓoye miki ba, wallahi wallahi Ameeratulkhair tashiga raina, ban iya ɓoye-ɓoye ba shi yasa na zo nan direct domin in faɗa miki ke da kika haife ta, ban santa ba ban taba ganinta ba sai a dan kwanakin nan amma ta shiga raina fiye da yadda kuke tsammani, jiya na kasa barci saboda tunanin ta sa yau na ce zanyi shawarar in zo wajenki, abu na gaba na karanta littafin sirrinta wanda anan na fahimci wasu abubuwa dangane da rayuwarta, ina babu damuwa ina so in zama wannan bangon da take so ta dinga jingina da ita da mahaifiyarta, dan Allah ki faɗa.” ya kai nan yana mai jiran ya ji abin da mahaifiyarta za ta ce. Ta shiga ransa fiye da tsammani me zai ji ya dawo ba ya tina wannan, abinda ke gaba kawai yake tinkara, shuru ɗakin ya ɗauka na lokaci mai tsawo, ta jima Adda na ƙare mai kallonsa sa'annan ta ce.
“Ban ta ɓa karanta littafin na, hmmmm amma ina da yaƙinin ta rubuta wasu abubuwa ne dangane da rayuwar mu dai, rayuwar mu na baya sai dai na ce maka, kayi haƙuri, baka san wacece ba, kada ka shiga inda ba za ka iya fita ba, Ameeratulkhair ba yariya ba ce da kasafai mutum zai gani yace yana santa, tana da tarin matsaloli a rayuwarta, mun dawo nan ne domin tsiratar da rayuwarta da kuma ranar da za ta bayyana ga duniya, sai dai me ina tabbatar maka a ranar sai an rabani da ganinta na har abada, mutane uku suna neman ta ruwa a jallo tun ba yanzu ba, tin daga shekara biyar baya muke rayuwa kaman wasu dabbibi, daga nan sai nan, cikin jin daɗi da wahala. dan Allah kar ka kawo wani zance aure a ciki domin kuwa akwai matsala.” sai ta yi shuru, take ya ce.
“Ni kawai ina so na zamo bango a rayuwarta ne, ban damu da ko suwa ke neman ta ba, ni dai ki bani wannan damar.” sai ta kuma yin murmushi.
“Kasan wacece Ameertulkhair?.” sai ya girgiza kai.
“Ban sa ni ba amma wallahi ko ya take ni dai ina son ta.”
“Hmmm zan baka labarita idan na gama sai ka tantance shin za ka iya zama da ita ko a'a, domin rayuwarta ba irin rayuwar kowace ƴa mace bace tun daga haihuwa ta fara samun kalubale na rayuwa har izuwa yanzu da kake gani, tana da juriya ba ta bayyana komai hakan yasa ina farin ciki da hakan, a yanzu zan faɗa maka wacece *AMEERATULKHAIRI* da cikakken tarihin rayuwarta, ita kanta wacece, zan faɗa maka amma kafin in ce komai na gode sosai bakasan ƴa ta ba, kake sonta baka ta ɓa ganinta ba amma ta shiga ranka, baka ta ɓa jin sautin muryar ta ba amma ka ce kana sonta.
“Daga zuciya na ke jin ta, ban samu da sanin ko wacece ba." sai Adda ta kalla Sararu murmushi ta sakar mata sannan ta ce.
“Idan har za ka ji za ka iya auren ta to ni nan a matsayina na mahaifiyar ta na baka ita halak malak indai za ka iya rayuwa da ita, sai sai nasan hakan ba zai yiwu ba ko kadan.” A hankali ya furzar da iskan bakin sa yana mai ritsa idanuwansa domin a wunin yau kaɗai ya fahimci akwai abubuwa da dama na rayuwar sa da ya yi missing, daga nan in ya tashi babu in da zai nufa sai wani gidan da yake tsammanin ganin ƴan uwansa a ciki, ya manta su amma a yau ya tina da su, a karo na farko da yaji Darling ba ta gabansa, ta mai kira har sa huɗu sai dai ya dinga yankewa abin da bai taɓa yi ba kenan, jiya ke a yanzu ya dawo mutum cikakke ba da ba da yake rabi mutum, muryan Adda ce ta dawo da shi duniyar nan.
“Ka shirya jin cikekken labarin AMEERATULKHAIR?." Sai ya ɗaya mata kai. Take hawaye ya fara gangaro daga idanun sai kuma kuka mai sauti ya ƙwace mata, sam labarin Ameera babu daɗi, sam ba ta son tunawa da komai, amma a yau za ta tina, za ta ba da labari, za ta tuna wasu mugayen mutane dake addabar rayuwar Ameera........... END.
> Toh fa wai jama'a wacece AMEERATULKHAIR ne, sannan ko dai asirin Darling ya karye ne....... PRETTYN JAJIRTATTU ce ✍️
🔥 *Let’s goooo!* 🔥 Hit that LIKE 👍 if you're truly *ready for the ride*! Because *HASASHE KO BURI* isn’t just a story — *it’s an experience.* 💭✨📚
✍️ _By PRETTYN JAJIRTATTU_ 💕📖
[9/14, 08:00] PRETTY SK NOVERLIST: ***
❤️ _I love you deeply, Habibah. Always and forever._
Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥 *Keep shining, JAW family!* *** 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_
🌟🔥 *HASASHE KO BURI* 🔥🌟
*📖 A powerful story filled with dreams, struggles, and destiny!*
💡 *Ka shirya?* Wannan ba labari bane na wasa — *it’s a journey into the heart of dreams and reality!* 😍