PAGE3️⃣7️⃣⏩3️⃣8
by @prettys01
_ABUJA_
“Tinda ki ka ji na amince da auren nan to kawai ki yadda, kinsan waye Ukashe kuwa? ki dai bari ayi auren nan a nan ne za mu fara target din mu, yanzu baki ga yanda nake mulkin babanki ko akwai wani matsala a cikin gidan nan babu, dan haka ki mai da hankali, mahaifinki shi yace ya miki a mijin aure Ukasha, ki amince domin kuwa in Ukashe ba ƙaramin mutumin ba ne, mai mugun kuɗi ne kuma haka nake fatan ki aure mai kuɗi, to gashi Allah ya kashe ya bamu, yanda nake Hasashe ma duk yafi samarin ki kuɗi, don haka ni nan mahaifiyar ki na amince da auren nan ki, bayan aure zamu mallaka gidan da shi kansa, sannan ki dinga juya sa da sauran matayen gidan, ke za ki zamo sarauniya idan ma ba kya son su sai muyi waje da su ki mallake sa ki mallaki gidansa.” murmushi budawar yarinyar dake zaune ta yi tana karka ƙafarta.
“Wo ke Mamanaaaaa, gaskiya ina son ki Allah ya bar min ke, gaskiya ne naga Guy ɗin ya haɗu ba laifi amma Mama, ina da kishi fa gaskiya ina da kishi bazan iya sharing mijina da mata har uku ba, Mama kuma ƙabilu daban-daban."
“Hmmm ki bi komai a hankali, ina ji dai ko da wani yare aka zo, bahaushiya ita ce gaba dan haka Maryam ki natsu ki jini da ƙyau, kina ji na?.”
*Eh ina jin ki Mamana."
“In bakya son kishiyoyin duk zanyi waje da su idan kina so kuma su zama miki ƴan aiki duk sai su zama miki, ba ki da case yarta.” tashi ta yi da sauri tana runguma mahaifiyar ta cike da jin daɗi da annashuwa, da sauri kuma ta nufa ɗakin ta na mai tafiya ta na haɗawa da rawa da ɗan ihu.
Ba laifi Maryam budurwa ce wacce ba za ta wuce shekara ashirin da biyu ba, tana da duhu fata amma kyakkyawa ce ga jiki dan ba za'a ce mata siriya ba ko kaɗan, ita ce tilo a wajen mahaifiyarta, sannan ga samu tarairaya sosai domin komai kuwa ita kaɗai Allah ya ba ta. Maryam ta taso ne cikin gata da jin daɗi, haka mahaifiyar ke fatan ta huta a gidan mijinta, dan ita ta shigo gidan mijinta ne yana da mata biyu, amma sai da ta kora kowacce ta mulki gidan ta mulka mijin in zan faɗa kalma ɗaya bai isa ya sauya mata shi.
Fatan ta ɗaya shine Maryam ta aura mai shaken ƙudi yanda zasu juya shi yadda take so sai gashi Allah ya basu, Mahaifin Maryam shi ya bashi ita kyautar domin a ƙarƙashin sa yake aiki a kamfaninsa ta yi farin ciki da jin haka sosai kuma tana fatan ayi bikin lafiya daga nan za su fara ba za mulki a cikin gidan Ukasha, za ta sanya Maryam ta mallake gidan gaba daya sai abin da Maryam tace shi za'a cikin gidan, za ta nunawa kowace yariya cewa bahaushiya ba sa'ar su ba ce ba kuma sa'ar kishin su ba ce haka. sai ta saki wani murmushi na mugunta tana mai cewa.
“Mu je zuwa, Ƴa ga sai kin zama sarauniya a gidan mijinki da yardar ubangiji, kuma babu mai juya min ke.”..........
*KANO* Haidar da Ameeratulkhair su wani kulle sosai, dan a cikin kwana 7 da suka yi saoyayya mai zafi tashiga tsakaninsu wadda dukansu sun makance a soyayyar, abu na Allah har suka cikin kwana bakwai babu wanda iya ganin ko da farcin Ameeratulkhair ne, dan akwai da taka tsan-tsan sosai.
Yau ce ranar ƙarshe sun shirya tsab dan dawowa, su gama haɗa komai da hujjojin suna mai farin ciki dan kuwa abin da suka zo nema sun samu ninkinsa, dajuka huɗun nan da suka zaɓa kuma Alhamdulillah basu samu matsala a dukka, kuma duk suna cikin koshin lafiya.
Farin ciki ne kwance akan fuskar Haidar dan kuwa a yanzu Amira jinta yake a jikin jikinsa. Kuma ina suna tare sai ya ji tamkar ya shiga wani sabon duniya ne, ya ara wayanta ya kai sau ba adadi domin ko zai ga hoton ta amma sai dai babu komai a ciki sai hotunan aiki da wasu abubuwa amma babu hoton ta a ciki, yayi-yayi ya ga fuskar ta amma taki sam, ina kuma ya matsa sai tayi fushi tare da rubuta mai kawai su haƙura da soyayya amma da ta faɗa haka sai ya ruɗe sannan ya ba ta haƙuri.
A kwana bakwai nan yanda kasan sun tafi yawon shakatawa ne dan kuwa kullum suna tare, suna yin chat, da yake sun ta fi da power bank kusan guda huɗu manya-manya wadanda har ila yau basu kare ba.
Ta cikin niƙaf ta sakar mai wani murmushi, tana jin san Haidar a cikin zuciyar. Ta tina chart ɗinsu na ƙarshe.
“Wace irin mace kake so?.”
“Sak ke." Murmushi ta yi sannan ta ce.
“Eh, amma a ra'ayinka ya kake son mace.” a lokacin ya jima kafin ya ce.
“Ina son mace mai juriya, mau baki dan ta dinga ƙwatar kanta a wajen kishiyoyin ta.”
“Wai kana da aure ne." Sai kawai ya fizge wayanta dan yana kusa da ita sannan ya ce.
“A'a ba mata na bane, matan Abba na ne, ba su da sauƙi, mace dai-dai su suke buƙata." Ta so ta ce wani abu amma sai ta fasa.
Numfashi ta ja, tabbas ta yi kuskuren faɗa wa soyayya da wanda ba ta sani ba, hakan ba shine illa ba, shin wanda suke nemanta ba za su bar Haidar da rai kuwa muddin suka sani, ta yi kuskure sosai da ta faɗa wa tarkon Haidar na soyayya. dogon ajiyan numfashi ta kuma sake wa sa'annan ta rinsa idanun da nake cikin nikaf ta buɗe su, sun ja sosai. Mamakin yadda ta sake da shi take, dole ta nisanci kalmar soyayya domin duk wanda ya yi gangancin kusantar rayuwarta, to kuwa ya na kira ma kansa matsala ne, domin ɗayan-biyu ne ko mutum ya rasa ransa ko mutum ya zaucewa.
Ba ƙaramin abu bane a wajen su hake mutum, sai dai ta dogara da Allah kuma shi ne majibancin al'amura, shi zai mata tsari ga ku duk masu ganin bayanta, mutum uku sun hata natsuwa, sun jakula mata lissafi.............. END.
> Cab Maryam Bahaushiya 🙄🙄🙄🙄🙄. Hmmm akwai abu fa. Ku kuma masoya sannunku *Haidar da Ameeratulkhair* ka ga Abubakar a gefe, sannan har yanzu ba musan wacce ita ba.......muje zuwa dai✍️
🔥 *Let’s goooo!* 🔥 Hit that LIKE 👍 if you're truly *ready for the ride*! Because *HASASHE KO BURI* isn’t just a story — *it’s an experience.* 💭✨📚
✍️ _By PRETTYN JAJIRTATTU_ 💕📖
[9/14, 08:00] PRETTY SK NOVERLIST: ***
❤️ _I love you deeply, Habibah. Always and forever._
Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥 *Keep shining, JAW family!* *** 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_
🌟🔥 *HASASHE KO BURI* 🔥🌟
*📖 A powerful story filled with dreams, struggles, and destiny!*
💡 *Ka shirya?* Wannan ba labari bane na wasa — *it’s a journey into the heart of dreams and reality!* 😍
_Reposting_
~LAST PAGE OF BOOK ONE~