PAGE3️⃣9️⃣⏩4️⃣0
by @prettys01
_Bayan wata biyu, abubuwa sun faru da dama wasu na daɗi wasu marasa daɗi, bari mu garzaya kowane bangare dan ji me ya faru a cikin wata biyu._
*UKASHA*
Wani aiki ne babba ya taso mai, dole ta sa yabar ƙasa, dan haka aka sa bikinsa saura wata biyu ta kuma kowane bangare suna ta shirye-shirye gadan-gadan, duk da yace shi ba ya buƙatar komai daga mace sai mace kawai yake so a kai cikin gidansa a yanzu haka ya washegari ne ɗaurin auren Ukasha, dan haka gaba ɗaya ba shi da wani natsuwa, duk da komai kuɗi kwai yake turawa, ba ƙarya ya saki kuɗaɗe domin kowace sai da aka mata akwati guda sha biyu, kuma ya yi ma kowace kaya irin na al'adar su, ya yi ƙoƙari fiye da misali, dan ko ina sai maganar wannan auren ake yi. Sannan duk ya samu fahimta mai kyau ga dukka matan, kuma yana fatan babu mai bashi matsala a ciki, sai dai tun kafin auren, Fillo ta gama mamaye mai zuciya, abun har mamaki yake yi sai dai ba'a mamaki da ikon Allah, sannan baisan dalili ba yana son ganin Ashake, ita kuma masifarta da rashin hakurinta na burge sa, yana son zuwa wajenta hira dan kuwa yana sha sosai, sau ran biyun kuwa suna girmamasa sosai kuma yana jin daɗin haka.
*SAMARI* Su Shamo kuwa sun gama shirye-shiryen tafiya US domin kuwa sun kammala jarrabawan su, basu ji sakamako ba, sun c daya fito sai a tura musu. Yau ne tafiyar kuma sun gama shiri tsaf, washegari ne tafiya US, hankalin su a ƙwance dan sun gaba biyan kuɗin komai, ba karamin kuɗi suka kashe ba amma da yake a yanzu kuɗi ba komai bane a wajen su, suna wasa da kuɗi, dan dai can ɗin aikin za'a fi samu da ba in da za su, so domin ƴan matan su sun tsaya musu especially ma I.B dan a yanzu ba ƙaramin kuɗi yake da shi ba, sai dai duk ya sun siya filayen kuma ta hannun Alhaji, sannan ya a dana takaddun sosai.
Shamo da Abdul sai da suka san yadda suka yi aka ɗaura musu aure da ƴan matan su kafin su tafi, da cewa aiki yakan kama ƙasa sai a turo su kawai, Muheey ce da kyar mahaifinta ya yarda da hakan dan shi bai kamata mace ta yi aure kuma ta ci gaba da zama a gidansa amma ba yadda ya iya, dan Muheey ta nace, dan a tinanita kar ya je can, ina ya ga fararen fata ya ce ya fasa da ita. Bayan hargitsin aka ko ɗaya musu aure, ita dai Ma'esh ba'a samu matsala ba ta bangarenta domin kuwa yana magana aka ɗaura auren da cewa bayan wata biyu za ta bi shi ita ma, karya ba'a yi taro sosai ba amma fa an kashe kuɗi. I.B ma yaso haka amma shi babu dama sai dai shi daya dawo ko ta tsiya sai sun aure juna.
*Mymoon*
Tun bayan kammala jarrabawarta Dad ya hanata fita ko'ina, sannan ya mata tambayar akan ina take kai kuɗaɗe dan wasan kuɗin na ta ya yi mugun yawa, haka motocin ta guda biyu duk babu yanzu, da ya tambaye ta sai ta ce.
“Ai tana da hankali, tasan me take yi da shi, ita ba yarinyar ba ce." Dad ya gaji, shi yasa ya kulle gaba ɗaya account ɗin ta, sai dai ba tasan Dad ya gane I.B ke hure mata kunne ba, kawai ya share zancen ne, abin da yafi damun shi bai wuce number Taj da baya shiga kullum.
Zauna yake a kan kujera idonsa na kan tv amma sam baya gane me ake yi a cikin tv domin gabaɗaya kwana biyu ne yana cikin damuwa, saboda sauyawan Mymoon, bayan kuɗaɗe da take wasa da su yanzu haka kamfaninsa guda ɗaya ya ruguje duk saboda hannun jari ya karye a ciki kuma ita ke rike da wannan kamfanin, a yanzu abin ya ishesa ne shiyasa ya zuba mata ido tare da ɗaukan tsattsauran mataki akan ta. wayarsa ya ƙara ɗauka sanana ya kuma kiran numbar nan sai dai kamar kodayaushe in ya kira ba ta shiga, sai dai mai yana kira na biyu wayar ta fara ringing, da sauri ya gyara zaman sa yana mai fatan Taj ya ɗauki wannan, kiran sai dai katse har sau uku, sai ya ajiye wayan yana mai tunanin gobe dole ya tafi dubai domin dubo shin lafiya yake, shurin ya yi yawa, baya kwana biyu ba tare daya kira su ba, amma tun sati biyu baya bai kira shi ba, take wayarsa ta hau ringing da sauri ya ɗauka ganin number Taj ne, picking ya yi yana kai kunnensa take wani dakakkiyar muryar mai cike da amu ta doki kunnensa, gaishesa ya fara yi cikin ladabi, sa'annan ya amsa yana mai ce wa.
“Taj ina ka shiga ne, me ya samu number ka baya aiki, ai da zuwa gobe nan zan shigo dubai ɗin, shirun ya yi yawa meke faruwa ne." Ya kai maganar cikin ɗan damuwa, sai wannan murya ya yi murmushi wanda yake jiyo sautin ta ta cikin wayar sa'annan yace.
“Haba Dad ina cikin koshin lafiya, abubuwa ne suka min yawa sosai, so nake ma in kiraka in ce maka gobe zan dawo Nigeria."" Baisan lokacin da murmushi ya kwace masa ba, sai ya ce.
"Kamar kasan neman ka, nake yi ruwa a jallo, goben dai zaka dawo."
” Eh insha Allah Dad, zuwa goben nan za ka ganni na dawo, fatan duk kuna lafiya lafiya?."
“Alhamdulillah, sai dai akwai yar matsala amma sai in ka iso ɗin.”
“Toh shike nan Dad, ina godiya Allah ya saka da alkhairi.”
“Ameen yarona.”
“A huta lafiya." daga haka ya kashe kira yana mai jin wani nishaɗi da jin daɗin gobe Taj zai shigo, ji yake kamar ya zubar ruwa a ƙasa ya sha dan murna.
Fitowar ta kenan daga kitchen, ta ji wannan hirar Dad yake yi, take ta kuma haɗe fuskan, dan dama ba ta cikin walwala kwana biyun nan, tsaki ta ja tana mai ayyana cewa.
"Ya zo din wallahi wallahi bazan aure Taj ba, gaskiyar I.B gashi ina gani wani zai aureni saboda kuɗi.
“Toh Alhaji mu dai zamu tafi.” Faɗin Abdul yana saba jakkan.
“Shike nan Allah ya tsare hanyar da ku isa ku tabbatar kun samu kun kira ni domin V.I.P ne ba za'a haɗa ku da sauran mutanen da kuka gani ba." Alhaji ya faɗa yana ƙara gyara babban rigarsa.
“Allah ya tsare min ku, fatan sa'a." Faɗin Abbas jiki a mace, wannan shine karo na farko da zasu yi tafiya ba dukkansu ba, daga haka Shamo da Abdul da kuma I.B suka shiga wannan babbar motar dake ɗauke da samarin maza kusan guda goma a ciki, Abbas in da yake ya ɗaga musu hannu jikin sa babu laka domin bai son suyi tafiyan nan ji yake kaman ya bisu amma ina yanzu haka ya kammala shiri ne na tafi aybuja, sai da motar nan tashi ta bar wajen sa'annan ya kaɗa kansa tare da jakan bayan sa, tasha zai nufa daga can zai nufa Abuja, Alhaji na kallon Abbas ya wuce sai ya girgiza kai tare da faɗin.
“Allah sarki Abbas, baka da rabon wahala, Allah ya soka, Allah kuma ya ce ce ka, kai mai sa'a ne kuwa, abokanka kuwa ka musu kallo na karshe kenan, dan har abada abadan ba za ka kuma ƙara ganin su ba.” Ya faɗa hakan yana mai murmushi, sai ya ciro wayarsa yana mai kai kunne.
“Hello, motan ta tashi sun tawo, to shike nan ina godiya, a miƙa min godiya wajen *Giji Zulƙu* ina matukar godiya kafin zuwa dare na zo, kuma ina farin cikin da Mamba a cikin ƙungiyar halaka.” daga haka ya kashe wayan yana fada yana wai wani murmushi, ya tabbatar ba mutane kusa da shi shiyasa ya saki jiki yake magana a haka, shiga mota ya yi yana mai barin wajen cike da annashuwa.
*ABUJA*
Gabaɗaya Sumayya ba ta cikin nutsuwar ta, tana cikin wani hali, ta ji haushi abin da ya faru, a ce kamar ita mai aji ƴar kwalisa, cikakkiyar mace budurwa mai ji da dukiya tana neman wani amma yake wulakanta, da ba ya ɗaukar number ta, sai dai ta yi mai saƙo ta whatsApp, sai dai ya yi ta gani amma baya reply, daga ƙarshe blocking ɗin ta yi a shekaran juya, tin daga haka take cikin wani yanayi dan ta rasa makama, ba ta san me za ta yi ba, ji take kamar ta je har kaduna ta samu Abbas ta ci mai mutunci ta ji dalilin da yasa yake wulakanta ba kamar ita mai aji tana kula shi dan talaka amma baya ga ta gabansa, ta fara bin abin a hankali amma ta ga abun ƙi yiwuwa, yanzu gashi an ɗauka kusan wata biyu da fara kulawa da ta yi, ba ta manta kalma na karshe da ya ta ɓa shiga tsakanin su ba, ce mata ya yi.
“Sumayya ina da wacce nake so kuma na mata alkawarin zan aure ta, dan haka dan Allah ki fita daga sabgata, in tasan da wannan maganar za ta yi fushi dani sosai, kuma fushinta tamkar ana zuba min garwashin wuta ne a jikina, dan Allah ki rabu da ni." abin da ya faɗa mata kenan ta kasa mai reply domin voice ya mata take kuma ya yi blocking ɗin ta, ta yi kiran duniyar nan bai ɗauka, saboda shi ka canza lambobi da dama amma duka a banza, sai dai me ta kai karshe so take ta faɗa wa mahaifiyar ta, koda kuwa ba za ta so ta ji tana son ɗan talaka amma ta taimaka ta yi mata hanya, rayuwarta na gaba da rugujewa in dai ba ta auri Abbas ba, ji take tamkar ta samu attack na zuciya.
Da sauri Safna ta faɗo ɗakin tana cewa.
“Sumayya! Sumayya!! Sumayya!!!, albishirinki.” gaba ɗaya zazzabi ya rufe ta, dan ko tana ji a yau ɗin nan dole sai ta je asibiti an duba lafiyar ta, a hankali ta budye bakinta ta ce.
“Ke da Allah banda lafiya, ki ƙyaleni ke Please.”
“Na kawo miki maganin zazzaɓin.” idanu ta buɗe a hankali, tana kallon Safna dake tsaye akanta.
“Ina wannan tsinanen yaron da kika haukace ma wa, yanzu na gan shi a cikin haraban gidan nan, yana tsaye da jakan bayinsa ya zo yana neman Abban Haidar.......” ai ba ta ƙarasa maganar ba ta zabura da sauri tana cewa.
“Ab......Ab....Abbas wai.”
“Eh Abbas, yana cikin gidan nan a yanzu haka.” ba ta damu da shigar dake jikinta ba, ta yi waje saboda girgiza kai tana cewa.
“Wai Sumayya ta haukace da yawa.” sa'annan ta ɗauki mata hijab ta bi bayanta.
Tana tafiya tana haɗawa sauri har da haɗawa da gudu-gudu ta fita haraban gidan, tsaye ta hangi Abbas yana mai latsa wayarsa gefen gate, shi ga nufa da sauri-sauri har ta isa gaban sa, ta isa tana haki, kallonsu take yi tana mai yi mai kallon tuhuma, shi kuwa sai a lokacin ya ju ya kalleta, kallo ɗaya ya yi mata sannan ya ɗauke kansa, domin kuwa rigar bacci ne a jikinta mai ragaraga wanda aka ganin kalan kayan da ke cikin jikin ta, tsaki ya ja a cikin zuciyarsa, yana faɗin.
“Wannan yarinyar sam ba fa da hankali, jibi yadda ta fito daga cikin gidan nan.” kafin ya yi wani maganar har Safna ta karasu sannan ta miƙa mata hijabi, ta amsa tana mai sanyawa sai a lokacin ta lura da kayan da ke hukunta, a hankali ta buɗe bakinta ta fara cewa.
“Ab......Ab..........Abbas." take ta yanke jiki a wajen, da sauri Safna ta yi kanta ta na mai cewa.
“Sumayya! Sumayya!! sumayya!!!.” amma ina ta yi nisan kiwo domin kuwa suma ta yi take.
*ABUJA*
Babban Masallacin jumma'a ne wanda ya cika sosai, a yanzu a ka gama ɗaura auren Ukasha da ƴam mata huɗu, abin da ya ma wa mutane da yawa mamaki kenan. Tsaye yake cikin babban riga sai faman murmushi yake yi, ba ƙyarya ya yi ƙyau fiye da misali, farin shadda ce ƙal a jikinsa an mai aiki da golding colour. Gefansa kuwa Umar ne shima ya sha wani shadda, matsawa ya yi kusa da shi ya ce.
“Ango, Ango Allah ya yi dai.” hannusa ya riƙe yana faɗin.
“Wallahi wani farin ciki nake yi sosai, alhamdulillah buri na ya cika.....”
“Saura Hasashen burin....” sai ya kuma sakin wani murmushi. END.