RAUNIN DA BA A GANI

Chapter 15

by @meefatinkwriters99

RAUNIN DA BA A GANI 

Meefat ink ✍️ writers 

Shigowa tayi da gudu tana cewa “ammie albishirinki” ammie tayi murmushi karfin hali tace “goro auta irin wannan gudu haka bana hanakiba” cikin zumudi tace“addace tasiyamin abaya a shop dinta” “habadai, dagaske"sai tadago takalli ruhy daketa murmushi tatsaya abakin kofa “ya kika tsaya kuma” karasowa tayi tareda gaisheda ammie “au namanta ammie ina wuni” cewar huda “lafiya kalau ruhaina, ke huda kinmanta da gaisuwarma sai murna ai” “tazo tacikakida surutu, tashi muje auta nayimiki wanka muzu muci abinci dannasan ammie ma bataciba jiranmu take” cewar ruhy, kamata tayi suka wuce dakinta tahadamata ruwan wanka sai taje tadauki kayan huda adakinta sannan tazo tayimata wankan, bayan tagama tashiryata cikin kananan kaya short da vest pink colour, sai itama ta watsa ruwa agaggauce tasaka three quarter da top milk colour takamo hannun huda suka fito. Kitchen tawuce auta kuma wajen ammie zubumusu abinci tayi tafito tana cewa “auta jekidauko ruwan wanke hannu” bayan takawo sai tace “adda muci a dining mana” dakuwa ruhyn tayi mata tace “baza aci acandinba zauna” bayan sungama ci sai huda takawashe komai takai kitchen, suka tattara wajen yayinda ammie ke kallonsu cikida sha'awa da godewa Allah da yabata yarinyar kirki kamar ruhy, ruhy ce takase mata tunani yayinda take cewa “ammiena kinsan me, wlhy yau su fina sukazo suka karbi kayan ankon dana fadamiki” “eh natuna"cewar ammie “toh shinefa suka kalli posts din abayanda nayi suka ce sunaso dukkansu suka dauka, akalla kowacce tadauki biyu” “masha Allah, Allah ya kawu kasowa mai albarka, saura nima nazo nabiya na autana” “haba ammie kibarshi kawai” “ke ba'a yiwa kasuwa haka” “to aima narigada na mayar da kudin, yanzu dai kimin alfarma anjima kar inyi girki mufita dinner kawai ammie” girgiza kai ammie tayi almun a'a “dan Allah fa ammie” tafada tana marairaice fuska auta dake gefema tace “dan Allah ammiena kiyarda muje pleeeeeeeeeease” “toh shikenan naji amma ruhaina ba'awa kudin kasuwanci haka” “to ammiena danmesa manake neman kudin badan in farantamiki keda autaba, idan bazanyi hakanba to me amfanin kudin, danku nakewa sabida banida kowa saiku”. Kwanciya tayi a cinyar ammie tana bata labarin school dakuma taronda za'ayi “harfa wai fina tace wai mutafi office na head of student musamesa dan yamana hanyarda za'abamu award nace mata a'a” “ruhaina” ammie takira sunanta cikin kaushin muryar “nayi farinciki dakike bin tarbiyyar dana doraki kai kuma ko gobene wata qawa ko malamin dakanshi yace kije kisameshi a office karki kuskura kije” amsawa tayida toh ammie “Allah yayi muku albarka yakareku aduk inda kuke” “ameen ammie” “bazan hanaki kawanceba amma kisan wadanda zakiyi hulda dasu, safina tanada hankali amma wadannan kawayenta dagani suna da rawankai” “wlhy ammie ko a school ma bana yawudasu samhace kawai bestie na sai fina” “hakan yanada kyau"hira suka cigabada yi har la'asar tagabato sai kowa yashiga dakin sa danyin sallah. Ruhy tana raka'anta nakarshe samha tashigo dakinda sallama, ta samu waje tazauna tare suka shafa addu'ar. Sai ruhy tace.