Chapter 16:RDBG
RAUNIN DA BA A GANI
Meefat ink ✍️ writers
“Kawar arziki ya kike yagida” “lafiya kalau fa” samha ta amsa “kin haduda ammie” “toh kekina tunanin zanshigo gidannan har na shigo dakinki batareda nanemi ammie mun gaisaba, kodai kina tunanin ammie takice kekadai” dariya ruhy tayi tace “daga tambaya, to maida wukar ” “ai gwaradai tafito miki da wukar, dukdama naga yartawa bata shigomin ba yau saida taga kinzo kafin tashigo"ammiece kemaganar lokacinda tashigo da turaren wuta dan ta ajiye adakin ruhyn, “aa wlhy ammie abokan baba ne sukazo masa dubiya shiyasa ban shigoba” “ayya kice yau kinsha aiki ya jikin baban” “eh wlhy ammie dasauki sosai ma” “ai da kinkirani natayaki” cewar ruhy sai ammie tafita yabasu waje “ai nasan bakyanan shiyasa ma bankirakiba” “ke yaufa zamu fita chilling ina gayamiki”cewar ruhy “dan Allah” “wallahi ammie ta amince dama banida niyyan yin girki yau dinnan”.
SAMHA
Samha kawar ruhyce tun suna yara hakama gidajensu nakallon juna, maman samha da mahaifinta sun rabu tun tana karama kuma bata sake waiwayarsuba ammiece ke kula daita wasu lokutan dan tana matukar tausayin yarinyar tun lokacinda mahaifin ruhy ke raye yabada daman ammie tana kula da yarinyar kasancewar mahaifin samhan matafiyine kuma suba yan garinbane balle taje gun yan uwa, haka rayuwarta yake yau ta kwana gidan ammie gobe kuma baba, shakuwace mai karfi tashiga tsakaninsu har ya kaiga komai in baban ruhy zaiyiwa ruhyn to tare yake musu hakama ammie tadora bayan rasuwarsa, baidade ba baba yayi hatsarin mota sai ta maida kwananta gida dan kulada mahaifinta wani sain ruhy kan tayata dan ita samha hatsarin baba yadan dakatarda ita zuwa school sai yanzu da jikin yayi sauki tacigaba.
“ammie kinga duk mungama shiryawa amma ruhy har yanzu bata gamaba” cewar samha dake gyarawa huda mayafinta “ai nauyin jikinta sai ita” cewar ammie “toh gani na fito muje” sai samha tace “ai dole kice muje bayan kinbata mana lokaci” dariya sukayi sai auta tace “ammie me zamu kawomiki for dinner” “a'a kunsan ban fiye son cin abincin restaurant ba kubari kawai” samha tace “a'a ammie dan Allah kifadi komene mukawomiki koda tuwo ne"tafada tana kunshe dariya, huda tayi caraf tace “eh ammie especially pounded yam dinsu akwai dadi” “toh sarkin ci angaisheki, wayace tuwo zamu kawowa ammie order mai kyau zamu yimata” cewar samha “shikenan kukawomin pounded yam din da egusi dukda banida tabbacin zaiyi dadi” “inshaa Allah zakiji dadinsa ammie har sai kince ke kullum ordern su zakici” cewar ruhy duka sukayi dariya ammie tayimusu addu'a da gargadin kadasu dade “nifada zakubi shawaratama kuyi order kawai basai kunfitaba” nan da nan suka marairaice kamar zasuyi kuka suka dinga ba ammie hakuri dan tsaf zata iya sauya ra'ayi, sai tace suje amma banda shashanci kuma kar suwuce 8pm dan alokacinma 7 takusa sukace toh sannan suka tafi.
Eatry mai kyau nan kusa sukaje anan suka zauna aka kawu musu menu, ruhy tayi ordering catfish, pepper soup da smoothie samha kuma pepper chicken fried rice da drink planet auta Irish, balango da chips, suka fara ci cikin nutsuwa da farinciki suna yin hira jefi jefi gameda award day dinsu dan samha tana karanta radiography under MBBS, suna maganan an tsayar da rana on Saturday za'ayi, bayan sun gama suka yiwa ammie da baba order sai suka wuce sukayi kananan siyayyansu sai suka wuce gida Allah yasa tara batayiba kuma sunsamu napep na unguwa har kofar gida yakawosu, samha batashigaba gidansu ruhybatayi musu sallama tashiga nasu gidan.