MATAR GIDA PAGE 27
MATAR GIDA 027
SHUUKRAN/022
P27
Ɗalha tare da sauran abokansa suna tsaye jikin mota wasu daga cikin su na zaune cikin mota duk suka bi ƙungiyar matan gida da ido har suka ɓacewa ganinsu,Ɗalha ya kalle Muhsin da ya yi mutuwar tsaye ya ce ''Allah yasa ba abinda nake tunani bane'' Muhsin ya sauki ajiyar zuciya ya mayar da dubansa ga Ɗalha ya ce ''kwantar da hankalin ka ƙila sun zo ma mahaifiyarta ne ko wani ba lallai dan Unaisa suka zo ba'' Ɗalha ya sauke ajiyar zuciya tare da faɗin ''Allah yasa'' a can cikin gida kuwa bayan shigar Hajiya Bilƙisu da tawagarta Aisha ta shimfiɗa masu tafurma cikin wani ɗaki da ba'a cika amfani da shi ba amma an gyara ɗakin tsaf saboda baƙi masu zuwa biki,Aisha ta kawo masu abincin biki wanda farar shinkafa ce da miya babu laifi ya ji nama daidai gwargwaɗo sai dai babu salak ruwan piya wata leda guda ta kawo masu haɗe da kunu da zobo da aka ɗura a gora,fita daga ɗakin Aisha ta yi kafin daga bisani ta dawo hannuta riƙe da katan ɗin pop cola guda ɗaya,fuska babu yabo babu fallasa Hajiya Bilkisu tare da muƙarrabanta suka yiwa Aisha godiya daga haka Aisha ta nufi hanyar fita daga ɗakin daidai lokacin Hajiya Ɓilkisu ta ce ''dan Allah in amarya na kusa a kira mana ita mu gaisa bana tunanin ta san mun zo'' cike da tsantsan mamaki Aisha ta ce ''to za'a mata magana'' ta faɗa tare da faɗaɗa murmushi da bai kai ciki ba,da wani irin sauri Aisha ta shigo ɗakin da Unaisa ke ciki ta tarar Unaisa zaune tare da Anty Lantana tana mata nasiha da kuma jan kunne kan zamantakewar aure, waje Aisha ta samu ta zauna ta kafe Unaisa da ido da aka rufewa fuska da koriyar mayafi kalar folawar da aka yiwa leshin jikinta ado,bayan Anty Lantana ta gama wa Unaisa nasiha ne ta mayar da dubanta ga Aisha ta ce ''in ce kowa ya mata nasiha"? Aisha ta ce ''eh'' Anty Lantana ta ce ''to sai ki fito da ita in kin gama ya kamata a kama hanya da wuri kar a yi tafiyar dare'' Aisha ta ce ''to Anty zamu fito yanzu'' bayan fitar Anty lantana ɗakin ne Aisha ta mayar da dubanta ga Unaisa fuska babu alamar wasa ta ce ''buɗe fuskarki ina son magana da ke'' babu musu Unaisa ta buɗe fuskarta ta sauke ido kan Aisha ganin babu alamar wasa fuskar Aisha yasa Unaisa shiga nitsuwarta Aisha ta fara magana inda ta ce ''kin yi baƙi suna can ɗaki'' Aisha ta yi shiru har sannan idonta kan Unaisa.
Unaisa da bata yi tunanin su Hajiya Bilƙisu za su zo bikinta ba saboda ɗaya daga cikin ƴan kungiyar ta haihu a garin Bauchi jiya aka yi suna wannan dalilin yasa Unaisa bata tanadar masu komai ba,a tunaninta suna can Bauchi,babu wani abu na musamman da ta ajiye da niyyar su,hakan yasa ta yi mamaki sosai da abinda Aisha ta faɗa harda bata san su Hajiya Bilƙisu bane,saboda babu wanda ta gayyata bayansu su koma basa gari,kallon Aisha ta yi kamar yadda itama take kallonta ta ce ''yayah ɓaki kuma daga ina?" Aisha ta ce ''ke zan tambaya'' shiru Aisha ta yi na wasu ƴan sakanni kafin ta ce ''mai ya haɗaki da Hajiya Bilƙisu shugabar ƙungiyar Matan gida a ina ki ka santa?"kirjin Unaisa ya yi wani irin bugu lokaci guda ta fita hayyacinta wani irin abu ne haka za su zo basu faɗa mata ba,da ta san da zuwarsu baza ma ta sauki su a gidan mahaifinta ba saidai ta sama wasu wani wajen na daban shikenan za su raina ta harda duk sun san iyayenta ba wasu bane amma ace kungiya su zo bikinta amma babu kaji babu lafiyayyan abinci,gashi har an fara tambayar ta ina ta sansu,a gaskiya basu kyauta mata ba,cikin rawar murya Unaisa ta ce ''mutumci muke da ita'' Aisha ta ce ''tambayar ki na yi inda ki ka santa,wani irin mutumci ku ke?" har sannan Unaisa bata cikin nitsuwarta cike da kiɗima ta buɗe baki ta ce '' a islamiyyarmu'' Aisha ta ce ''karatu take a ismaiyyar taku?" lokaci guda Unaisa ta ji ranta ya ɓaci hakan yasa ta haɗa gira ta ce ''yayah bafa wani abu bane kawai dai mutumci muke dan Allah ki bar magana nan haka kin ga dai gidan a cike yake da ƴan biki'' Aisha ta ce ''au rashin kunya za ki min'' rai ɓace Unaisa ta ce ''ba rashin kunya zan maki ba,tambayar ce ta fara isa ta kin tambaye ni na baki amsa amma sai faman tambaya ta ki ke,yayah ni fa ba yarinya ba ce shekaruna ashirin da biyu ina da dama da kuma yancin tafiyar da rayuwata yadda nake so'' Unaisa ta kare magana fuska babu walwala Aisha ta ce ''yanci? kina nufin hulɗa da mutanen da basu dace da rayuwarki ba shi ne ƴanci? kin kuwa san abinda ki ke?" Aisha ta kare magana cike da mamaki haɗe da ɓacin rai Unaisa na shirin magana ne Anty Lantana ta shigo ɗakin tare da faɗin ''wai me ku ke a ciki ne har yanzu ku fito mana'' ta kare magana tana rufawa Unaisa fuska da gyale,Anty Lantana na riƙe da hannu Unaisa suka fita daga ɗakin
dakin Mama Anty Lantana ta wuce da Unaisa Mama ta yiwa Unaisa nasiha kan ta yi hakuri da duk abinda zata gani gidan mijinta sannan ta riƙe kishiyarta da ƴaƴan kishiyarta amana,duk rashin kunya da tsiwar Unaisa a wannan lokacin ta ji gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi nan take ta shiga wani irin yanayi na kewar mahaifiyarta da ƴan uwanta,lokaci guda hawaye ya shiga zuba daga idanunta ji ta yi kamar ta fasa auren kamar ta yi zamanta kawai da Mama wani irin runguma ta yi wa Mama babu shiri Mama ta sake murmushi ta ce ''hakuri za ki yi Unaisa Allah ya yi maki albarka ya baku zaman lafiya'' ta faɗa tare da yiwa Aisha alama ta kama Unaisa su tafi,da kyar aka ɓanɓare Unaisa daga jikin Mama kuka take babu ji babu gani,Unaisa na cikin wannan yanayi Hajiya Bilƙisu da tawagarta suka fita daga ɗakin da aka sauke su,babu abinda suka taɓa cikin abubuwan da aka basu suka bi ƴan kai Amarya, mutum uku aka cire daga dangin mahaifin Unaisa sai yayunta mata uku daga gefen uba,haka daga gefen Mama mutum uku aka cire Anty Lantana da ƙanninta biyu sai Aisha da jikar Anty Lantana, motoci uku aka kwashi su tare da Amarya sai motocin Hajiya Bilƙisu da tawagarta guda biyu,tafiyar awanni uku ne zuwa huɗu daga Kaduna zuwa Kano karfe ɗaya na rana daidai da suka tashi,karfe huɗu da mintina arba'in suka isa Kano gidan Ammi,tarɓar arziki Ammi ta yi masu nan parlournta ta sauke su,inda aka cika su da abubuwan motsa baki iri daban daban Ita kuwa Unaisa ɗakin Ammi aka wuce da ita bisa Umurnin Ammi Amma ta sa an kai mata abinci ita da jama'rta tawagar Hajiya Bilƙisu dake Ammi bata san su ba a tunaninta duk dangi ne,sallah suka fara yi bayan sun idar da sallah ne sun dan taɓa abubuwa da aka kawo masu Anty Lantana ta sa aka fitar da Unaisa nan suka ƙara gaisawa da Ammi da ƴan uwan Ammi,daga haka aka fara gudanar da abubuwan da suka dace irin ta al'ada Husnah ƙanwar Ɗalha aka bawa uwar ɗakin Unaisa.
Daga haka aka buɗe masu bangaren Unaisa, sosai bangaren ya yi kyau farin fenti aka yiwa bangaren nata an zuba mata furniture milk colour da labulaye kalar ƙasa ga manya manyan frime sosai bangaren ya yi kyau,babu wasu tarin kaya ko ado mai yawa komai ya yi looking so mature and luxury,kowa faɗi yake masha Allah gida ya yi kyau sosai, Hajiya Bilƙisu da tawagarta ma sun yaba gidan harda ba wani girma ne da gidan ba ɗaki biyu ne da parlour sai kitchen amma tsarin ginin da kuma luxury furniture da Ɗalha ya zuba mata ya sa gidan yin wani musulmin kyau,furniture irin ɗaya ya zuba mata Kano da Kaduna,bayan sallar magrib Hajiya Ɓilkisu da mutane ta suka kama hanyar Kaduna bayan sun bawa Unaisa gudummawar naira dubu ɗari uku da kungiya ta haɗa mata sosai Unaisa ta ji daɗin ƙudin da suka bata,washe gari Husnah ta haɗa bikin buɗan kai yadda ta kira masu decoration suka yi mata decoration mai kyau,an gudanar da bikin buɗan kai cikin tsari kowa ka gani cike yake farin ciki da anisuwa,Amarya Unaisa ta sami kyaututtuka daga dangin miji sosai,har mamaki ƴanuwan Unaisa suke saboda sun sami labarin dangin Ɗalha na son Amirah sosai musamman Ammi amma sai suka ga itama Unaisa sun tarɓeta hannu bibbiyu,washegari iyaye da ƴanuwan Unaisa suka yiwa Unaisa da Ammi sallama,sosai Unaisa ta sha kuka har ta gode Allah
Ranar da ƴan rakiyar Amarya suka koma daren ranar ango Ɗalha ya shiga ɗakin Amaryarsa Unaisa,wannan dare ya kasance daren tarihi wajen Ɗalha jin kansa ya yi a wata duniya ta daban tun da Ammi ta haifisa bai taɓa shiga yanayin da ya shiga a wannan daren ba har ji yake kamar yau ya yi aure kamar bai taɓa sanin mace ba sai yau,ji ya yi tun da can maneji yake,ya ilahi,gaba ɗaren Ɗalha ya ƙasa rintsawa kawai ya kafe fuskar Unaisa da ido kamar yau ya fara ganinta,ba ƙaramin wahala Unaisa ta sha ba cikin wannan daren ta yi magiya ta yi kuka,cizo yaƙushi amma duk a banza sau biyu ta suma cikin wannan daren,da kyar ta samu Ɗalha ya sarara mata shima saida ta rinƙa kiran sunan Ammi kafin Ɗalha ya ƙyaleta,kamar yadda Ɗalha bai yi bacci ba haka ma Ammi duk ihun kiran sunanta da Unaisa ke yi tana ji amma babu abinda zata iya mata a wannan lokacin da ya wuce addu'a,haka Ammi ta kwana zaune tana sallah da azkar,can ƙasar zuciyarta kuwa tausayin Amirah ne fal,Ɗalha da kansa ya yiwa Unaisa wanka cikin daren ya gasa mata jiki Unaisa ta yi ta gaya masa ɓaƙaƙen maganganu amma ko a jikinsa,bayan dawowarsa daga sallar asuba ya tada Unaisa ta yi sallah amma sai cewa ta yi ƙabarinsu ba ɗaya bane saboda haka ya ƙyaleta ta yi bacci babu yadda Ɗalha bai yi ba Unaisa ta ƙi tashi ta yi sallah,ya gaji da tashinta ya hakura ya kwanta bai dau lokaci ba bacci mai nauyi ya dauki shi,can cikin bacci ya ji ana buga masu kofa da ƙyar ya samu ya tashi ya je ya buɗe kofar ƴar aikin Ammi ce riƙe da basket ta kawo masu abin kare karɓa basket ɗin Ɗalha ya yi, nan cikin parlour ya ajiye basket ɗin kafin ya wuce ɗaki bayan, shigarsa yaga Unaisa bata kan gado yana shirin barin ɗakin ne ta fito daga bathroom da alama alwala ta yi tana tafiya tana buɗa kafa kamar ƴar shayi,Ɗalha ya kalle agogon dake daure kan bed site drower yaga karfe takwas da rabi na safe,bai ce komai ba yana nan zaune Unaisa ta tada sallah,bayan ta idar da sallah ta tashi bata tsaya addu'a ko azkar ba ta nufi gado zata kwanta,da mamaki Ɗalha ya bita da ido kamar ba zai ce komai ba sai kuma ya ce ''ba ki yi addu'a ba za ki kwanta?" ba tare da ta kalle inda yake zaune ba ta ce ''in kai ke karɓa sallah kar ka ƙarɓa'' tana gama faɗin haka ta yi kwanciyar ta kan gado a hankali Ɗalha ya tashi daga inda yake zaune ya koma kusa da Unaisa ya kai fuskarsa daidai tata yana ƙarewa fuskarta kallo murya can ƙasa ya ce ''tashi mu je ki yi r breakfast Ammi ta aiko mana da breakfast in mun gama sai ki cigaba da baccin ki'' banza Unaisa ta yi masa ta cigaba da baccinta Ɗalha ya sauki ajiyar zuciya ya ce ''come on babe tashi muji'' buɗe idanunta ta yi kafin ta fara magana, wani irin wari ne ya daki hancin Ɗalha wari mai ɗaga hankali kamar warin mushin ɓera haka Ɗalha ya ji warin da fari bai san daga inda warin yake ba sai daga baya ya fahimci daga bakin Unaisa ne hakan yasa ya yi sauri tashi kusa da ita,Unaisa da ta fahimci hakan sai cewa ta yi ''aiy hakuri za ka yi saboda ba kullum nake wanke baki ba rabona da wanke baki yau kwana tara,sai jibi in Allah ya kaimu zan wanke'' shiru ta yi tana ƙarewa Ɗalha kallo da shima ita yake kallo kaman tv ta ce ''da na ci abinci warin zai tafi sai kuma gobe ko can dare,saboda haka ba wani abu bane na saba da kayana''
SHUUKRAN