MATAR GIDA

MATAR GIDA PAGE 28

by @maimunabala209

MATAR GIDA 028




SHUUKRAN/022




P28



Cike da tsantsan mamaki Ɗalha ya ce ''me ki ka saba da shi?" cikin nuna halin ko in kula Unaisa ta ce ''bakin mana bafa wani damuwa bane'' ta yi magana tare da tashi daga kwanciyar ɗa take,saif ta nufa ta buɗe kofar saif ɗin suturarta ne ciki da duka basu wuce kala biyar ba,sauran kayan suna cikin akwatin lefenta, wata sitin atamfa ta dauko riga da zani da ɗankwalinsa zanin atamfar Unaisa ta dauka ta daura a ƙirji kafin ta cire doguwar rigar bacci da Ɗalha ya dauko mata daga akwati cikin dare,nan kasar ɗakin ta jefar da dogowar rigar baccin,Ɗalha na nan tsaye yana binta da kallon mamaki ganin ta nufi hanyar fita daga ɗakin ne yasa ya yi mata magana ya ce ''ina kuma za ki je haka?" daidai sanda ta zo kusa da shi ta buɗe baki ta yi hamma wani mugun wari da ya daki na ɗazu ne ya buge hancin Ɗalha,ji ya yi bazai iya jurewa ba, ba tare da ɓata lokaci ba ya yi saurin barin wajen yana toshe hanci zuwa wannan lokaci ran Ɗalha ya fara ɓaci hakan ya sa ya haɗa girar sama da ƙasa ya ce ''lafiyar ki kuwa?'' Unaisa dake tsaye bakin kofa ta ce ''ƙalau nake'' fuskar Ɗalha babu alamar wasa ya kalle Unaisa ya ce ''wuce ki je ki wanke baki'' ya faɗa yana nuna mata kofar bathroom , cike da mamaki Unaisa ta yi magana inda ta ce ''ban gane na je na wanke baki ba, na faɗa maka sai jibi zan wanke baki,na ga dai bakina ne ba naka ba dan Allah Mallam kar ka takura min,baza fa ka canza min tsarin rayuwa ba,wannan shine tsarina wanka ba kullum nake ba sai bayan kwanaki  biyu zuwa uku nake, brush kuma sai bayan 12 days,yauwa kar a wani dame ni ina dalili daga zuwa gidan ka zaka fara kafa min dokoki'' tana gama faɗin haka ta yi wucewar ta parlour inda ta zauna nan ƙasan parlour ta buɗe food wormer taga ƙosai a ciki,ɗaya wormer ta buɗe ta ga doya soyayya da ƙwai,sai kunun tsamiya cikin flask,ɗaya daga cikin kufuna da aka sa a basket ta dauko ta zuba kunun a ciki,nan cikin parlour ta yi zamanta ta cika cikinta,mamaki ya kusa kashe Ɗalha bai taɓa sanin Unaisa ƙazama bace sai yau, iya zaman sa da Amirah bai taɓa jin wani abu mai kama da wari daga jikinta ba,murya can ƙasa ya ce ''me na aikata ne me na yi wa kaina? ya aka yi ban gano hakan ba tun kafin aurena da ita?" gaba ɗaya ya rikici Unaisa ta gama cika sa da mamaki babu shiri ya fita daga ɗakin ganin Unaisa ya yi zaune ƙasan parlour ta baje da daurin kirji tana cin doya hankalinta kwance,kallo ɗaya ya yi mata ya dauke kai,ƙasa zaman gidan ya yi gaɓa ɗaya 













Abinda Ɗalha ya fi tsana a rayuwarsa shine ƙazanta,duk sanda ya je zance wajen Unaisa ganinta yake tsaf tsaf da ita ta yi baza kamshi wani lokaci har magana yake mata kan ta rage turaren da take sa yana yawa,yanzu ya fahimta dalilin da yasa tana fesa turare over,wanka kawai ya yi ya shirya kansa cikin wata farar shadda da aka yiwa ɗinki jamfa,Unaisa na nan zaune cikin parlour Ɗalha ya wuce zai fita, ganin fita zai yi ya sa Unaisa yin magana da sauri miƙe tsaye tana gyara daurin zani ta ce ''fita za ka yi?" Ɗalha ya yi shiru bai tanka ta ba Unaisa ta daura da ''gaskiya ya kamata ka ci abinci kafin ka fita'' ta yi magana tana zuwa inda yake da wani irin  sauri Ɗalha ya dakatar da ita da hannunsa ya ce ''dan girman Allah kar ki ƙaraso'' cikin sauri Ɗalha ya fita daga ɓangaren bai tsaya ko ina ba sai bangaren Ammi ya tarar da Dady zaune cikin parlour tare da Husnah suna hira,gaishi Dady Ɗalha ya yi kafin ya gaida Ammi,Ammi ta amsa gaisuwar ba tare da ta kalle fuskarsa ba amma cikin zuciyarta farin ciki ne fal,a tunaninta ɗanta ya samu nitsuwa harda dai ta san Amirah na kokari,sannan hakan ba yana nufin ta daina son Amirah bane,Ɗalha ya dauki a ƙalla mintina arba'in zaune cikin parlour tare da Ammi da Dady can dai ya yi masu sallama, bayan fitarsa gidan wani abokinsa da ke nan Kano ya nufa me suna Al ameen 













Yana nan zaune cikin parlour yana jiran Al ameen ne tunanin Amirah ya faɗo masa hakan yasa ya ciro wayarsa daga aljihu ya kira layin Amirah,Amirah dake zaune cikin parlour tare da yaranta suna kallon carton gaba ɗaya daren jiya Amirah ta nime barci a idonta ta rasa,a jiyan ta kira Ammi da safe dan su gaisa kamar yadda ta saba duk bayan kwana huɗu nan ne Ammi ke sanar da ita a jiyan ƴan rakiyar Amarya sun koma Kaduna ita a tunaninta sati zasu yi,kusan kullum sai Ɗalha ya kirata ya ji ya suke ita da yara amma bai taɓa kawo mata zancen amarya ba hakan yasa bata san komai dangane da amaryar ba,tun bayan gama waya da Ammi taji gaba ɗaya hankalinta ya ƙasa kwanciya haka ta uni ranar gaba ɗaya zuciyarta babu daɗi dare kuma bacci ya kaura a idonta tun karfe uku ta fara ayyukan gidan hakan yasa kafin sha ɗaya na safe ta gama komai ta haɗa kan yaran ta zaunar da su parlour ta kunna masu tv tana zaune tare da yara wayarta ta fara ƙara alamar shigar kira daukar wayar ta yi taga Ɗalha ne ke kira gyara zama ta yi kafin ta amsa kiran




















 Cike da nitsuwa ta gaishi Ɗalha shima kuma ya amsa mata cikin taushin murya,tambayarta  lafiyar yara ya yi ta ce masa duk suna lafiya daga haka ya daura da ''anjima za ki yi wata baƙuwa daga nan Kano'' kirjin Amirah saida ya buga lokaci guda,cikin zuciyarta ta ce Allah ya sa ba Amaryasa zai turo min ba,jin ta yi shiru bata ce komai ba yasa Ɗalha faɗin ''kina ji na?" Amirah ta ce ''ina ji'' Ɗalha ya daura da ''wacce zata riƙa taya ki ayyukan gida ne,na ga ya dace a samo wacce zata riƙa taimaka maki'' tsabar mamaki Amirah ƙasa magana ta yi sama da shekaru hudu tana rokon Ɗalha ya sama mata ƴar aiki amma ya ƙi sai gashi yau ya sama mata bayan ta cire rai,cikin rawar murya Amirah ta ce ''ƴar aiki?" Ɗalha ya yi murmushi me sauti da Amirah ta ji sautin murmushin kafin ya ce ''eh ƴar aiki mamaki ki ke?" Amirah ta yi shiru kamar tana gabansa ta wani noƙi murya ta ce ''umm'' Ɗalha ya ce ''bai kamata ki yi mamaki ba pupsik you deserved more dear'' yau dai Amirah ta gama cika da mamaki ganin yadda Ɗalha ke mata magana rabon da ya yi mata magana haka har ta manta kawai ta baye masaita ce ''thanks love Allah ya saka da alkairi ya ƙara buɗe'' fuskar Ɗalha dauke da murmushi ya ce ''ameen'' shiru ne ya biyo baya na wasu ƴan sakanni can Ɗalha ya ce ''ranar monday lesson teacher zai fara zuwa,zai rinƙa taimakawa yaran da homework ɗinsu zai kuma riƙa masu karatun alku'ani'' tsabar murna Amirah bata san sanda ta ce ''Allahu akbar Allah na gode maka,Abban Sudais Allah ya sa ka fi haka'' murmushi kawai Ɗalha ya yi ya kashi wayarsa












 Amirah ta mayar da dubanta ga yaran ta ce ''Abbanku ya sama maku lesson teacher'' duk suka zuba mata ido su dai basu ga wani abun farin ciki ba a ganinsu takura ce kawai kenan baza su riƙa wasa a gida ba kullum cikin karatu duk yaran idonsu a kan tv Suhail ya mayar da dubansa ga Amirah ya ce ''Mumy kanmu bazai fashe ba saboda karatu?" Amirah ta yi murmushi kafin ta ce ''a'a dan albarka sai dai tarin ilimi da fasaha'' daga haka ta tashi zuwa ɗaki bayan shigarta ɗaki layin Rumaisa ta kira bugu ɗaya Rumaisa ta amsa kiran nan Amirah ta sanar da Rumaisa Ɗalha ya sama mata ƴar aiki ya kuma samawa yara malami da zai riƙa yi masu karatu a gida ya kuma taimaka masu da homework,sosai Rumaisa ta nuna farin cikinta Amirah na shirin kashi waya Rumaisa ta jefo mata tambaya inda ta ce ''anya kuwa ango ya sami amarya yadda ya kamata ya sameta kuwa?daga tara da Amarya sai kyautatawa uwargida abinda aka yi ta roƙonka ka yi ka ƙi, dare ɗaya ka tashi ka ce ka aminci lallai wallahi da sake'' ita dai Amirah bata kawo komai cikin zuciyarta ba kawai ta sallame Rumaisa ta kashe wayarta daga haka ta koma parlour cikin yara tana nan zaune wani bacci mai nauyi ya dauke ta 














Karfe biyu na rana daidai ƴar aiki Ammi ce tsaye kofar bangaren Unaisa tana ta bugun kofa haɗe da sallama,ta dauki a ƙalla mintina bakwai tsaye wajen tana sallama haɗe da bugun kofa amma ba'a buɗe mata ba hakan yasa ta yi tunanin ƙila bacci Unaisa take,buɗe kofar ta yi haɗe da sallama,shiru parlourn ya yi baka jin motsin komai sai ƙarar AC dake aiki idonta ne ya sauka kan basket ɗin safe da ta shigo masu da shi ta ga plate da kofi da aka sha kuna nan wajen har ya fara bushe da fari ta yi tunanin kwashe kwanuka amma wata zuciyar ya ce ta barsu kawai hakan yasa ta ajiye basket ɗin abincin rana,tuwon shinkafa ce miyar taushe daga haka ta fita daga ɓangaren,karfe uku da rabi na rana Unaisa ta farka daga nannauyar bacci da ya dauketa tun misalin sha biyu,a hankali ta tashi zaune har yanzu jikinta ciwo yake musamman ƙasan ta,haka dai ta daure ta tashi ta wuce bathroom tana gyara daurin kirji bayan shigarta bathroom zama ta yi kan siter bayan ta gama abinda zata yi ne ta cika buta da ruwan ɗumi dan yin tsarki amma tsoro ya hanata yin tsarki yadda ya kamata har sannan wajen bai daina mata zafi ba,ta dauki a ƙalla mintina biyu zaune kan siter kafin daga bisani ta watsa wa wajen ruwa kawai ba tare da kai hannuta wajen ba,babban buta ce lamba shida haka Unaisa ta yi ta watsa ruwan butun ba tare da ta sa hannu ba har ruwan ya ƙare,daga haka ta dauro alwala ta gabatar da sallar azahar bayan ta idar da sallah ne ta fita parlour da niyyar ƙarasa sauran kunun safe saboda yunwar da take ji,ganin wani basket banda na safe yasa Unaisa ƙaraso cikin parlourn da sauri nan ta samu waje ta zauna ta dauki ƙullen tuwo ɗaya ta buɗe daga leda ta sa a plate sai faman turure tuwon ke yi ta buɗe wormer miya ta ɗiba miya ta zuba kan tuwon bata tsaya ɓata lokaci ba ta shiga cin tuwon hankalinta kwance,bayan ta gama ci ne ta tashi ta bar komai yadda yake food wormer's da plate ɗinda ta yi amfani da su duk ta barsu a wajen kitchen ta shiga ta dauki gorar ruwa ta buɗe ta kafa gorar a baki ba ta cire gorar ba saida ta sha ruwan sama da rabi kafin ta cire gorar,bayan shigarta ɗaki ne ta ji ana kiran sallar la'asar hakan yasa ta wuce bathroom ta dauro alwala ta gabatar da sallah bayan fitarta daga bathroom ta zura dogon hijab kan daurin kirji ta tayar da sallah, bayan ta idar da sallah ne ta cire hijb ɗin jikinta ta ajiye shi kan darduma daga haka ta yi kwanciyar ta kan gado  wayarta ta dauko daga jaka ta kunna data rabonta da wayar tun jiya da rana,bayan ta kunna data ne ta shiga group ɗinsu na matan gida ta shiga charting tana nan kwance bata san sanda bacci ya dauke ta ba,karfe biyar daidai Ɗalha ya shigo bangaren Unaisa bakin sa dauke da sallama ya shigo amma ga mamakinsa ya fara cin karo da kwanuka cikin parlour lokaci guda ran Ɗalha ya ɓaci hakan ya sa bai tsaya ɓata lokaci ba ya wuce ɗakin Unaisa nan ya ganta kwance rashe rashe kan gado daurin kirginta ya kwance yadda nononta ɗaya na waje ɗaya na rufe da zani kanta babu ko ɗankwali ta sake baki miyu na tsiyaya, dafe kai Ɗalha ya yi murya can ƙasa ya ce ''na shiga uku what is the meaning of this ya rabbi help me'' idonsa ne ya sauka ƙasan ɗakin yadda yaga gaba ɗaya ɗakin a hargiste ga pant da bara ɗinta nan watse a ƙasa tun daren jiya da watso su ƙasa hakan nan ta barsu rigar bacci a can suturar da ta sa daren jiyan kafin ya canza mata zuwa rigar bacci suma suna can watse ƙasan ɗaki











SHUUKRAN