Page 1
Fateema Mahmud wacce aka fi sani da Afrah, a sakamakon sunan kakarta ta wajen uba da ta ci, nagartacciyar yarinya ce, kyakyawa haifaffiyar garin Minna. Mai cikar kamala, hakuri, juriya, sune manyan halayenta na-gari abin koyi, sai kuma tsantsar ilimin Islama da Allah ya wadata ta da shi, domin tun tasowarta take kokarin koyon addininta, har zuwa yanzu da ta mallaki hankalin kanta. Ta zama cikakkiyar mace, domin tuni ta kammala karatunta na sakandire, tana zaman jiran sakamako ne a yanzu. Idan akwai abinda ya ragi Afrah a rayuwarta. To ba zai wuce maraicin rashin uwa ba, domin ta dandani dacin maraici tun tana 'yar shekara biyu, kuma ita ce kadai 'yar da mahaifiyarta ta haifa tare da mahaifinta Malam Mahmud. Bayan rasuwar mahaifiyarta ne, rikonta ya koma hannun matar Babanta. Mama Hauwa, wacce a matsayinta na uwargidan Malam Mahmud, tana da yayyi guda biyar biyu maza, Mansur wanda shi