Musabbabi Book 1

Page 2

by @yargidanimam

ne na farko, a yanzu ma'aikaci ne a hukumar wutar lantarki, wato (NEPA). Yana rife da babban mukami, ya yi aure har da 'Yarsa daya, sai Kabir, shi kuma ma'aikacin banki ne, shi bai wuce watanni uku da aure ba, sai Naja"atu da Sakina, su ma duk sun yi aure. Na'ima ce ta rage, wacce take tsarar Afrah, duk tare suka kammala makaranta. Sai dai abu daya da Afrah ta rasa a gidan mahaifinta, shine kulawa da kowace "Ya take samu na uwa, domin irin rikon da Mama Hauwa ke mata, ba irin riko bane na amana. Wanda maraya ya kamata ya samu ba'a kowane mataki. Mama Hauwa na nuna bambanci kiri-Kiri tsakanin Afrah da 'ya' yan ta, Ko kadan ba ta kyautata mata, rayuwa take a gidan tamkar ba "yar gidan ba, duk da Malam Mahmud yana iya kokarin sa domin ganin marainiyar 'Yarsa ta samu riko me kyau daga Mama Hauwa. Amma hakan ya kasa tabbata, domin Mama Hauwa ta zama tamkar tauraruwa me wutsiya, domin shi kansa Malam Mahmud din ta fi karfinsa, ta kan yi duk abinda ta ga dama ko a gaban idonsa ko a bayan idonsa. Inna Halima wacce ita kadai ce kanwar Malam Mahmud. kuma ita kadai ce take iya