Musabbabi Book 1

Page 3

by @yargidanimam

takama Mama Hauwa birki akan irin mugun rikon da take ma Afrah Hakanne ma ya sa, kusan rabin rayuwar Afrah take yi a gidan Inna Halima, domin duka ranar juma'a. Can take tafiya, sai ranar lahadi take dawowa gida, wannan dalilin ya sa Mama Hauwa da Inna Halima ba sa shiri ko kadan. Makarantar Islamiyyar da Afrah take yi, anan kuma take koyar da kananan yara, saboda hazakarta. Ya Sayyadinsu Habib ya maida ita Malama, a ajin haddar Kur' ani ta kananan yara, tana daukarsu gun koyon Kur ani da Tauhid. Malam Habib shine mutum na farko da Afrah ta fara tsayawa da shi a matsayin masoyi, ta kuma amshi tayin soyayyarsa, domin yarda da ta yi da irin son da yake mata na tsakani da Allah da kuma hanyar Ubangiji da yake doreta akai. Hakan ya sa take da tabbacin cewa daga gare shi za ta sami kyakkyawar rayuwa, ko ba kudì da jin dadi, to idan har akwai Allah a cikin rayuwarsu, to ya ishesu daga dukkan komai, don haka ta tsayar da zuciyarta gun mutum daya, wato Ya Sayyadinta Habibu.