Musabbabi Book 1

Page 3

by @yargidanimam

Yau asabar ne Afrah tana gidan Inna Halima, yau gyara take mata na gidan gaba daya. Inna Halima tana gefe a zaune, duk inda Afrah ta yi, tana bin ta da kallo, tana matukar sha'awar yarinyar da halayenta, domin duk inda ake neman yarinya me hankali wacce ta rike maraicinta, aka sami Afrah, to an wuce wajen. Tana matukar jindadin kasancewa da Afrah, a duk sanda ta zo gidanta, ta daina aikin komai, duk abinda za ta yi Afrah, ta kan dauke mata, hatta girki ba ta yi, ta kan dauke mata komai. Inna Halima. na tsaka da yin wannan tunani aka bugo kofa da Karfi. Musaddik ya fado cikin gidan, tamkar wanda aka jefo ba tare da sallama ba, Inna Halima ta mike tana kallonsa

'Musaddik". Ta Ambaci sunansa da karfi, a yayin da Afrah ta yi saurin ja da baya, domin kar ya bugeta.

Musaddik nagartacce,kuma kyakkyawan matashi. wanda ya hada komai da za ka iya kiransa da jarumin matashi, sai dai kallo daya za ka yi masa. Ka san ya rasa wani ginshiki na rayuwarsa, wanda ya hana shi damar da za'a kira shi da mutumin kirki, ba shi da natsuwa, da ganinsa ka ga wanda ya yi nisa a shaye-shaye, ko a yanzu ba'a cikin hayyacinsa ya ke ba.