Musabbabi Book 1

Page 4

by @yargidanimam

"Inna abinci na ke so,yunwa nake ji” ya fada da wata irin budaddiyar murya Inna Halima ta yi ajiyar zuciya, sannan ta kalli Afrah ta ce "'Afrah aje tsintsiyar nan, ki zubo ma yayanki abinci.”

A hankali ta yi kasa da tsintsiyar, sannan a sanyaye ta wuce kicin. Inna Halima ta maida kallonta ga Musaddik, wanda yake tsaye ya nannade kafafun wando tace "Zo ka zauna" Ta nuna masa tabarmar da ke shimfide, ya wuce da takalmi da komai ya zauna akan tabarmar, ba ta damu ba, domin ba yau ya saba yin hakan ba, ta ja kujerar da ta tashi akai, ta koma ta zauna tana kallonsa. Tana saka abubuwa da dama a ranta. •Har zuwa lokacin da Afrah ta dawo dauke da faranti cike da shinkafa da miya da ta dafa,a hankali ta aje a gabansa, sannan ta juya ta wuce Zuciyarta cike da tsananin tausayin Musaddik da halin da yake ciki. Musaddik yace "Inna na kan so na zo cin abinci gidanki duk ranar sati, saboda na san Afrah tana gidan nan, ina jindadin abincinta, komai rashin gyaransa” Maganar Musaddik ta katse mata tunani da take yi ta juyo da idonta tana kallon sa, a yayin da Inna Halima ta jinjina kai tace