Musabbabi Book 1

Page 5

by @yargidanimam

"Ba kai kadai ke jin dadin girkin Afrah ba, kowa yana yabawa, tun daga kan yara har zuwa maigidan kansa.” Ya yi dan murmushi, a yayin .da yake cin abincin, ya dan waiwayi inda Afrah take wacce Ke cigaba da karasa shara ya ce, "Haka ne Inna, shi ya sa ni ma na kan kwaso yunwata zuwa gidanki. Don na san idan na ce kwadayin girkinta zai dinga kai ni gidansu kullum, za mu sami matsala da Mama Hauwa, don na san farantina ba zai dinga cika ba kamar yadda yake cika a gidanki." Gaba daya suka yi murmushi, a yayin da ya maida hankali kan cin abincinsa. Inna Halima kuma tana zube masa da ido, tana matukar tausayin Musaddik da kuma rayuwarsa wacce bata taba tsammanin zai koma haka ba. Duk tsananin Kamun kansa ilimi da cikar kamalarsa. Amma rana tsaka rayuwarsa ta koma haka. a lokacin da ya kamata ace rayuwarsa ta inganta, babu wanda zai ga Musaddik ya yarda ya kuma amince Musaddik din da ne, lamarin yana da matukar daure kai. Inna Halima ta yi kasa da murya à hankali, ta fara yi masa magana "Musaddik, anya ka na ganin wannan rayuwar da ka dora ma kanka za ta kai ka ga hanya madaidaiciya, wannan wace irin rayuwa ce? Da mutuncinka da darajarka, rana tsaka duk ka kore wannan, ka koma ka na Kaskantarciyar

Ku dakace ni

YAR GIDAN IMAM

bazan yarda da rashin yin comments ba don wallahi ina iya barin yin posting din idan bakwa comments. MUSABBABI

NA

HAJ HABIBA ABUBAKAR IMAM

***