Musabbabi Book 1

Page 6

by @yargidanimam

rayuwa mara dadin ji ko gani, shin meye dadin wannan rayuwar? A hankali Musaddik ya cire cokali a cikin abincin, fuskarsa gaba daya duk ta canza ya shiga cikin damuwa, ya ce a sanyaye, "Inna babu wani dadi ga rayuwar da na ke ciki, hakia inda ina da ikon canja hanyar da na biyo, da na yi gaggawa na canja, domin ko kadan ban jin dadin rayuwar. Amma na rasa dalilin da ya sa na kasa yaki da zuciyata na daina, duk da ina kyamar abinda na Ke aikatawa ni ma,”

Inna Halima ta jinjina kai fuska cike da tausayinsa tace "Ka yi yaki da zuciyarka ne, ka dage ka kori shaidan, domin hakika shine yake yi maka huduba, ka tuna irin gata da arziki da ka taso a ciki Musaddik kayi tunanin irin girma da kamalarka da dubban jama' a suke gani a da, sannan ka tuna irin ilimi da hangen nesa da ka ke da shi wanda a yanzu duk sun tattara sun gudu, a sanadiyyar tsarin rayuwarka da ka canja, ka duba ka ga yadda ka maida kanka, hakika lamarinka na damun mu, yana kuma daure mana kai kwarai da gaske Afrah da ke tsaye gaba daya sai ta juyo ta dora ma Musaddik idanunta wadanda suka cika da hawaye, zahiri tana daya daga cikin wadanda lamarin yayanta Musaddik ke damu, ta kan shiga