Musabbabi Book 1

Page 7

by @yargidanimam

dimbin damuwa da tunani idan ta tuna halin da yake ciki, Sannan ta kan rasa inda zata sa kanta, idan ta kasa gane dalilin canjawar Musaddik, mutumin da ya taso da nagarta, kamala, natsuwa, ilimi da matukar hangen nesa, tana daya daga cikin wadanda rayuwar Musaddik ke matukar burgewa. Yana matukar ba ta sha'awa, rayuwarsa da yadda yake tafiyar da lamuransa, abin a tsaya a kalla ne a kuma yi koyi da su.amma meya kawo wannan canjin?. "Inna kada ku gaji, ku yi ta tayani da addu'a don Allah". Furucinsa ya Kara dasa tausayinsa a zuciyar Afrah. Inna Halima ta ce "Addu'a muna nan muna yi Musaddik. Allah ya shiryeka, ya dawo da kai hanya madaidaiciya, ba za mu gaji da yi maka addu'a ba." Ya gyada kai ya ce "Na gode Inna, bari na tafi” inna Halima tace "Ka karasa cin abincin mana” Ya girgiza kai lokaci daya yana mikewa. "Na koshi Inna, na gode.” Ya juya ya dubi Afrah Yace "Na gode da girki,." Yana gama fadin haka, ya juya da sauri ya fice. Inna Halima ta numfasa cike da damuwa tace "Allah ka yi mana maganin abinda ya fi karfinmu." Afrah ta amsa da "Amin."Sannan ta juya ta ci-gaba da aikinta,amma zuciyarta na cike da tunanin Musaddik da tausayinsa, domin ta san hakika yana bukatar taimakon addau'a, ta kuma kara shan alwashin