Musabbabi Book 1

Page 8

by @yargidanimam

za ta ninka akan addu'ar da take yi masa Haka ta kasance cikin tunaninsa da tausayinsa a wannan ranar kamar yadda ta saba a duk lokacin da suka hadu da juna. Washegarin lahadi. Inna Halima sai dare, sannan ta sa Afrah a gaba zuwa gida, domin tana son ganin Dan’uwanta Malam Mahmud, hira suke yi a hanya har suka isa gida. Dawowar Mallam Mahmud kenan daga masallaci sallar Issha"i, fuskarsa ta fadada da fara' a yana kallon "Yar-uwarsa, ya ce. "'Halima, ai na dauka "yar ta ki sai gobe za ta dawo, da na ga dare ya rufa? “ Ta yi murmushi, tace “a’a yaya. Na ce ta jirani ne mu taho tare, saboda ina son ganinka, na san kuma iyanzu ne zan sameka a gida a tsanake” Ta karasa maganar tana zama a kan tabarmar da yake zaune akai. A yayin da Afrah ta durkusa ta gaishe shi, Cike da so da Kauna ya amsa mata, sannan ta wuce dakin Mama Hauwa, domin ta gaida ta, amma haka nan ta amsa ba yabo ba fallasa fuska a hade, Na'ima ko tana kwance akan gado ko kallonta ba ta yi ba harta fice ta shige dakinta.

Mallam Muhmud ya dawo da kallonsa ga Inna Halima bayan sun gama gaisawa, sannan ya ce “Halima ina fatan dai lafiya ki ke son ganina, da daddaren nan?"' Inna Halima ta gyara zamanta