Musabbabi Book 1

Page 9

by @yargidanimam

Tace “Yaya ba wani abu bane dama magana ce na ke son mu yi akan Musaddik". Mallam Mahmud ya jinjina kai ya ce "Ya kara dakko wata maganar ne?” Ta girgiza kai Ta ce "*A'a, babu abinda ya yi, kawai dai wani tunani na yi akan halin da yake ciki, wanda yaya ka fi kowa sanin duk duniyar nan. Mu ke nan mu uku iyayen mu suka haifa, daga kai sai marigayiya Harirah mahaifiyar musaddik sai kuma ni, yadda ba za mu so mu ga 'ya ' yan da muka haifa cikin wata fitina ba. Haka shi ma. Musaddik ba shi da kowa duk duniyar nan sai mu, kuma mu kadai ne ba za mu juri ganinsa cikin wani hali ba, don ina da tabbacin da mahaifiyar sa ce take a matsayinmu. Ita ma sai inda karfinta ya kare akan 'ya yan mu, shi kadai ta haifa a duniya kuma shine sanyin idaniyarta, don haka duk yadda za mu yi, ya zama dole a kanmu mu yi kokarin daidaita rayuwarsa. Malam Mahmud ya numfasa, damuwarsa ta Kara fitowa fili. Ya ce "Halima kin fi kowa sanin duk duniya ba ni da wata damuwa da ta wuce -damuwar Musaddik.ina cikin tsananin tashin hankali akan rayuwar da yake yi, ina kuma takaicin yadda na kasa taimakonsa akan ya natsu, babu kuma abinda ba zan yi masa ba,matukar zai shiryu domin ba ni da wani burin da ya wuce haka, duk addu’ata akan musaddik take karewa Halima”.

Ku dakace ni

YAR GIDAN IMAM

Bazan yarda da rashin comments ba don wallahi zan iya daina posting din idan bakwa yin comments. MUSABBABI

Na

HAJ HABIBA ABUBAKAR IMAM

***