Page10
Inna Halima ta numfasa gami da gyara zamanta ta ce "Ni Yaya akwai hanyar da na ke ganin wata Kila zai iya zama sanadiyar shiryuwarsa". Mallam Mahmud yana kallonta yace “Wace hanya ce wannan?” Ta dan muskuta tana kallonsa sosai sannan tace “Aure, yi ma Musaddik aure ina ganin zai iya zama wata hanya ta samun nutsuwarsa, domin duk rashin jin namiji , idan ya yi aure ko yaya ne akan samu sauki, ko bai daina abinda yake yi duka ba, zai rage". Mallam Mahmud ya ce. "Haka me, aure hanya ce ta samun natsuwa, zai kuma iya canja wa rayuwarsa tsari, amma ba anan gizo ke sakar ba, wacece za ta aure shi, kada ki manta a dalilin halinsa ya rabu da matarsa, sannan tun daga lokacin babu wata da ta karav sauraronsa, saboda ba shi da natsuwa, to yanzu ina zai samo mata shi da ko lokacin kansa baida shi balle lokacin wata, wace ce za ta yarda da shi har ta aure shi a haka?" Inna Halima Ta ce. "Tabbas! Abinda kamar wuya, samun me auransa, domin kowace mace burinta ta sami kintsattsen namiji. Domin ta samu kwanciyar hankali a gidan auranta, don haka yaya ya zamar mana dole mu yi sadaukarwa saboda zumunci.?” Malam Mahmud ya dubeta cikin rashin fahimta Yace “Sadaukarwa? ban fahimce ki ba”Inna Halima ta ce "Ina nufin dole a cikin 'ya' yan mu mu sadaukar da daya ga Musaddik ya aura, mu yi aikin zumunci”, Ta gyara zamanta fuskarta ta canja alamun damuwa ta ce.